Ruhanai

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Mallam Amadu mai ruhani,

    Mallam Amadu mai ruhani,

    Kun ji gamon ALA mai waƙa da,

    Mallam Amadu mai ruhani.

     

    Zan nemi tsari gun Sarki Allah da akai na shaiÉ—anu zan hani,

    Tsare ni tsarewa ya Allahu raba ni da ruÉ—in ‘yan zamani,

    Ka ba ni wadatar zuci Allah ka sa na fi ƙarfin duk sheɗani,

    Ya Allahu ya Ƙayyun na yi tawassili da Ƙur’ani.

     

    Ka ƙara daɗin tsira ya Allah ga Ahmadu Mamudu bawan Allah,

    Manzon baiwa É—an Abdallah Muhammadu mai kwana yin sallah,

    Tsira da aminci ya Allahu da alaye nasa bayin Allah,

    HaÉ—a Asahabi ya Allah abin koyin bayinka Allah.

     

    Ran Juma’a bayan almuru na hikima ni É—aya al’umma,

    Sai ga mota ta alfarma tai fakin da direba mai kima,

    Ya zo shi sayen kaset a hikima ya ce wai ina Alan al’umma?

    Na ce masa ni ne Alan waƙa yai mamaki ƙirar hamma.

     

    Ya ce mini ALA ka burge ni da ka yi waƙar Sarki mai girma,

    Sarki Ado ÆŠan Bayero mai temako gurin al’umma,

    Ya É—auko alkhairi ya ba ni ya ce ci tukuici dan alfarma,

    Albarkacin Ado Bayero da kai wasa shi cikin al’umma.

     

    Mu kai ekscenjin lambar waya mukai ban kwana da mai ruhanai,

    Ga shi gari da sanyin safe za shi Abuja mai ruhanai,

    Ya zo muka tattauna ni da shi na ce masa nemi anan ruhanai,

    Ya ce mini aiki ne ya saka ake mani inkiya da ruhani.

     

    Ni na ga abin ai ban mamaki da Mallam Amadu mai ruhani,

    Na ga abin zamÉ“am al’ajab da Mallam Amadu mai ruhani,

    Kuma na ga karamar wannan ƙarni ga Mallam Amadu mai ruhani,

    Toh ya ƙasaita ya gawurta ya tumbatsa mai ruhani.

     

    Ya ba ni du’a’i in lazimta ya ce da fa an mai rauhani,

    Ya ce mani sharrin É—an Adam da aljan ka kere a zamani,

    Ya ce mani kar kai hasssada ga kowa ko ƙyashi a zamani,

    Ashe Mallam babban gwarzo ne a fannin karatun Ƙur’ani.

     

    Ya ba ni du’a’i in lazimta ya ce da fa an mai rauhani,

    Ya ce mani sharrin É—an Adam da aljan ka kere a zamani,

    Ya ce mani kar kai hasssada ga kowa ko kyashi a zamani,

    Ashe Mallam babban gwarzo ne a fannin karatun Ƙur’ani.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.