Aminar Mama

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

Amshi

Rabbu kai ni gidansu Amina in sha ruwa Aminar mama.

Taƙwara a zumunci namu da ni da ke ba zan manta ba.

Rabbu kai ni gidansu Amina in sha ruwa ɗan randa.

 

Sabo da zumunci sai da gamon jini,

Baba ba ni in baka sai da farin jini

Shimfidar fuska sai dai da farin jini,

Shi adashin kyauta sai da farin jini,

Amina ta mama.

 

Duniya mai yayi daina guna-guni,

Yau da mu taka juyi gobe gidan wani,

Goɗiya mukke Allah da farin jini,

Ba mu yin katsalandan kan sha'anin wani Amina ta mama.

 

Taƙwara na taso don na rabe aya,

Taƙwara mu rabe tsakuwa da tsakin aya,

Ga ɗiyan Hausawa sun gaza taciya,

Sun gaza da rabe tsakuwa da tsakin aya,

Su mai jar koma.

 

Alfijir mai kau da duhu na shigar dare,

Da ruwa da wuta ba sa zamani tare,

Yau ga labarina na ruwan dare

Kafin a fahimta ai tsayuwar dare.

 

 

Kan batu na zumunci an yi karan tsaye,

A bayanin ƙauna an yi fashin tsaye,

Ƙauna da zumunci an masu gautaye,

An haɗa su da soyayya a karan tsaye,

Duk an daddama.

 

Lamarin soyayya kwai rabuwa ciki,

Lamarin ƙauna ko ba rabuwa ciki,

Ƙauna da zumunci sa ni da ni ciki,

Lamarin rabuwa ku cire ni na bar ciki,

Ku min alfarma.

 

Ɗan uwa na hakika nakke a gunku ni,

Ɗan uwa na shaƙiƙi nakke a gunku ni,

Sahibin da alaƙa baki rabo da ni,

Ni da ku fa alaƙa ba ta da ƙa'ida,

Amina da mama.

 

Rabbu kai ni gidan su Amina in kwana can,

Rabbu kai ni gidansu Amina in saura can,

A gidansu Farida Amina in ƙoshi can,

Mui raha da zumunta mui yo dariya da yayan mama.

Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Post a Comment

0 Comments