Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Bi isimu Rabbul bariya
Bi hubbi nabiyil auwabi
Nana Faɗima alawiyya,
Nana Faɗima mardhiyya,
Nana Faɗimattu adiyya,
Ya haura'ul insiyya.
Nai nufin yabo ga abar yabo Nana Faɗima da karimci,
Mai haƙƙuri mai kyauta yi tsatson girma da mutumci,
Nana Faɗima abin da kuka yi shi ne muke ta kwatanci.
Muke ta kwatanci,
Tsatson girma da mutunci,
Silar haske da karamci,
Tushen girma da kawaici,
Turgadar adalci mafificiyar a so da karimci,
Nana Faɗima kin ciri tutar so a biyayya kin cancanci,
A ciraci takarda ai maki baiti cikin cari da kwatanci.
Nana Faɗima Fauziyya,
Nana Faɗima alawiyya,
Nana Faɗima mardiyya,
Nana abidattu zakiyya,
Ya na'ima bittu adiyya,
Nana sajida shamsiyya,
Ya haura'ul insiyya,
Nana taufatul ahwaziyya,
Zahara zakira zakiyya,
Saliha sadika aliyya.
Nana Faɗima bintu nabiyu zaujatu aliyu abal turaba,
Yau Aminu Alan waƙa mai haiba hubba,
Nai tawassali da biya ta dafa da nake ga ahlil hubba,
Rabbana ka ɗau raina da tsantsar son Fati Fauziyya,
An tambayi sayyiduna Ali ya zamanku da bintu adiyya,
Ya ce zamanmu da ummu abiha ba cuta ba ƙarya,
Irin zaman 'yan aljanna muke da Faɗimattu adiyya,
Nana haƙƙuri da biyayya,
Nana tausayi khairiyya,
Nana ba ta yi jayayya,
Nana Faɗima mai kunya mai kyan gani ga mai dubayya,
Kamarta kamar an tsaga kara ga Annabi khairul bariya,
Abida sajida ummul Hasan Usaini adiyya,
Ummul hasanul salihina,
Wa Usainil masanuna,
Da Ali zainul abidina,
Da bakirul hadimina,
Da Ja'afarussadiƙina,
Musa kazim a yabona,
Da ridha Ali akilina
Da Ali alhadi na zana,
Da Muhammadu jauwadina,
Da Alhasan askarina,
Mahdi mai zamanina,
Ina sonku dare da rana,
Dare da rana,
Dare da rana.
Nana Faɗimattu tsokace ta cikin jikin nabina,
Hiya madhgatun minni fad ce ta khairul alamina,
Man azaha fa kad azani in ji masoyina,
Man aza ni fakad azallahu faɗa ta manzona,
Wal iyazu billahi.
Wal iyazu billahi.
Na tuno da Nana A’ishatu ‘yar Abubakar Saddiku,
In ta kalli Nana Faɗimatu sai ta yi kuka bil hakku,
Ta ce Nana in tana tafiya da dariyarta a hakku,
Har da murmushinta in baku,
Komanta babu firaku da ubangidan sadfiku,
Shi ne Muhammadurrasulillahi assadikul masduku,
Mai gaskiya abin gaskatawa bil taslimil hakku.
Ya shahida ya makiya,
Ya mauluda ya madaniya,
Ya wasila imamiyya,
Ya sa'ada ya sharifiya,
Ɗayyiba sayyida makiya
Sa'ida ta'iba zuhriyya,
Nuratu ainul nuriyya,
Ya babal khairi adiyya,
Jannatul arifina zakiyya,
Ummul shurafa'u aliyya,
Ummul shurafa'u adiyya.
Nana hujjatullahi alannasi abar yabon tsinkaya,
Bintu Muhammadur rasulallahi batula margatun nabiyya,
Nai tawassali a gurin Allah da baitin da nai wa adiyya,
Ya zamo silar saduwa da Annabi a duniya da kiyama,
Ba don dabi'ata ba,
Ba don dabi'ata ba.
Na tuno da taron Kuraishawa sarakuna ma'azurta,
Mata na tamayyurin tafiyar isa cikin ƙasaita,
Fatima bintu nabiyullahi ta yi shiru cikin keɓanta,
Wasu na gori a gareta,
Babu suttura a gareta,
Ba mulki na sarauta.
Wasu zafafan hawaye sunka ƙwaranyo a fuskar Binta,
Faɗimma tai dawayya gurin Rasulu babban gata,
Tana isa taj ji albishir saƙo na mai halitta,
Rigar girma alfarma,
Zinare ne aka tsarma,
Lu'ulu'u har ma kumama,
Yaƙutu jikinta da dama,
Zubardaji an tsattsarma,
Ta yi shiga shigar alfarm,
Da ma kun san ba dama,
Fagen kyan zubin alfarma,
Nan fa sai Faɗima ta koma,
Kallo ya koma sama.
Sai ta zamto kama da wata a cikin taurari kuma,
Sai fa tambaya suna shafarta suna a ina kika sama,
Faɗima a nan tab ba da dama kowa imani ya cira ma,
Karima azeema,
Karima azeema.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.