Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.
Amshi
‘Yan mazan fama gidan soja ginshiƙin yaƙi mazaje,
Nassara na rundunar soja don tsare haƙƙin mutane.
Shimfiɗa
Yan mazan fama mazan tafiya gaba dai gaba dai mazaje,
Kui rawar daji mazan soja ga amana ba garaje.
Kun ga harsasai da ke aske ‘yan ta'adda ‘yan garaje,
Guguwa kin bar kiyasai,
Kar su koma manna gidaje.
Na ga kwarkwasa da tsatso suna ta hargowa ga mage.
Babu ban baya gidan soja ko da sanda ko da lauje,
Koriyar tutar ƙasar Naja,
Kore da fari a tsarme.
Dokuna ga tambarin mikiya bayani zan a tsame.
Ga alamar dokuna akkawal a tsari ko a camme.
Allami na baki yana nuna ga ƙasar noma a sheme,
Mikiyar na nuna Nijeriyar abar alfahhari ce
Ga alamar Y da ke nuna mahhaɗa ta koguna ce,
Cibiyar kogin riɓer Niger ga riɓer Benuwe a gicce,
Inda sunka haɗe a kogin gari garin Lokoja a sace.
Ita alamar dokuna akkawal alamar martaba ce,
Unity peace and progress kun ji motor na ƙasar ce,
Wai haɗin kai ci gaba da zama na luma babu ƙwace,
Tambari na ƙasar uwa da ubanmu ƙasar Nijeriya ce.
Rabbana masanin shirin sarrari da na ɓoye Alhalilu,
Kai ka ƙagi ƙasarmu Nijeriya ka yi ta ƙasar ƙabilu,
Kan nufe mu zaman ƙasa ɗaya al'uma ɗaya Zuljalalu,
Mai shirin raba kawunanmu ka bar shi a tutar gaffalallu.
Arziki na ƙasarmu ba zai bari a bar mu haka kawai ba,
Wassu na fitinar ƙabilanci ba abin alfahhari ba,
Wassu na fita ta addini ba da hujjar dogaro ba,
Wassu na fitina a kan dukiyar da ba ko hakinsu ce ba.
Tambarin nan peace ku samar da shi da yarda babu yarda,
Rayukan jama'a ku kare shi daga saran ‘yan ta'adda,
Don ƙasar ɗaya ce ku tilasta masu tawaye su yarda,
Nassara na gunku ko dai da lalama ko ko da jigida.
Kun ci ƙarfinsu a yau nassara tana kaki na soja,
Jamma'ar birni da ƙauye suna du'ai kanku soja,
Malaman birni da ƙauye suna du'a'i kanku soja,
Babu ja baya a tausa su dai mazan famanmu soja.
Gwamnati tai tanadin tsarraba fagen yaƙinku soja,
Tankunan yaƙi egwa har da ma jiragen yaƙi soja.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.