Astagfurullah

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin WaÆ™oÆ™in Aminu Ladan Abubakar (ALA)Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi

    Astagafirullah, Astagafirullah,

    Astagafirullah, Astagafirullah,

    Astagafirullah, Astagafirullah,

    Astagafirullah, Astagafirullah,

    Astagafirullah, Astagafirullah,

     

    Abin da nay yo bisa kure sarki Allah,

    Gare ka na miƙa wuyana ya Allah,

    Astagafirullah, Astagafirullah.

     

    Abin da kullum naka raya shi a rayina,

    Da abin da kullum naka ganinshi da idona,

    Abin da kullum naka jinsa a kunnena,

    Da abin da kullum naka faÉ—in sa a harshena,

    Da abin da kullum naka tuna a ƙwaƙwalena,

    Da abin da kullum naka taɓa shi da hannuna,

    Da wajen da kullum naka zuwan shi da ƙafafuna,

    Da abin da na yi da gangan bisa ra'ayina,

    Da abin da da na yi rashin sani yash sha kaina,

    Astagafirullah, Astagafirullah.

     

    Abin da na yi saƙarsa da fusahata,

    Da abin da na yi na isar da hikimata,

    Da abin da na yi da 'yan dabaru na fasalta,

    Da abin da na biye wa son zuciyata,

    Da abin da na yi ya wuce can na manta,

    Da abin da abin da na yi yanzu Alla gafarta,

    Da abin da zan yi gobe Allah gafarta,

    Sarkina kar Ka bar ni ni, ni da badarata,

    Jallallah ba tsumi garan da dabarata,

    Astagafirullah, Astagafirullah.

     

    Ya Allah Almudabbiru mai juyawa,

    Ya Allah Almusawwiru mai sauyawa,

    Sarki mai juya zamani mai shiryawa,

    Bawanka ya ga zamani mai rikitarwa,

    Na duƙa na kasa da kaina don hurwa,

    Yarje min na cika da ƙarshe kyawawa,

    Sarkina kar ka bar ni nayyo dambarwa,

    Gwadabena na riƙe abin kamawa,

    Nurullah Hashimi ɗa ga Ƙuraishawa,

    Astagafirullah, Astagafirullah.

     

    Ya Allah Arrahamanu Rahimu buwayi,

    Ya Allah Almuhaimun Ƙuddusu Buwayi,

    Ya Allah Assalamu munna Buwayi,

    Allah Almuhaiminu, Azizu Buwayi,

    Ya Allah Aljabbaru, Ƙaharu Buwayi,

    Ya Allah Alwahhabu Razaƙu Ƙaharu Buwayi,

    Ya Allah Alfatuhu Alimu Buwayi,

    Ya Allah Al’azizu Ganiyu Buwayi,

    Nai tsani Allah da kai ba wani shayi,

    Astagafirullah, Astagafirullah.

     

    Kai na riƙe garkuwa muhallin kwancina,

    Kai na riƙa mai tsaro muhallin tashina,

    Kai na riƙe taliƙin mulallin tafiyata,

    Kai na riƙa sanda fargaba ta shiga rayina,

    Kai na tuna tuntuɓe idan nai da ƙafata,

    Kai na riƙe in larura ta sha mini kaina,

    Kai na riƙe sanda maƙiya suka rufu kaina,

    Kai na riƙe sanda na rabauta da mai sona,

    Kai na riƙe lokacin da na rasa Abbana,

    Astagafirullah, Astagafirullah.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.