8.5 Kano Tumbin Giwa - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 397)

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Amshi:

    Kano garin saye da sayarwa jalla ta dabo babbar Hausa,

    Ko da me ka zo an fi ka Kano ta dabo tumbin giwa.

     

    Allah Ubangiji mai kowa Sarki tabara runbun baiwa,

    Sarkin da shi ya ƙagi birane yayo ta dabo tumbin giwa,

    Kano garin muzakkar birni birnin dake tsare mana kewa,

    Ko da mai ka zo an fi ka jalla ta dabo babbar giwa.

     

    Kano garin saye da sayarwa tun zamanin zuwan larabawa,

    Tun zamanin shehu maghili an san mu kan saye da sayarwa,

    Waɗanda sun ka kawo saƙon manzonmu adali ɗan baiwa,

    Jalla uwar jahohin Hausa mai tambari da tumbin giwa.

     

    Jahohi a nai musu take mu namu tambarin kasuwa,

    Kasuwa a kai maki dole ko an ƙi ko ana so baiwa,

    Mahadi ta al’ummomi kowanne ɗan jaha ya zowa,

    Uwa ma ba ɗiya mama ƙasurgumin gari san kowa.

     

    Komai ya zo Kano ya zamto bozo a nahiyar Hausawa,

    In ka ga mai zaman kashe wando sai dagalolo autan wawa,

    Ko da ƙasa ta gefen hanya ka kasa kana saidawa,

    Albarkatanmu babu iyaka sai dai na tsakuro ɗebowa.

     

    A ɓangaren sana’ar hannu mun markaɗe jahohin kowa,

    Na tuno ranar bajakoli ranar da na gano Turawa,

    Sun zo suna tayin ta’ajibi an kai su sun gano dukawa,

    Balle a kai su fannin ƙira ko nahiya ta majemawa.

     

    Malam ka duba harkar saƙa matanmu ma suna birgewa,

    Suna rabe zare da abawa har angalala ‘ya ‘yan baiwa,

    Sai ka ga masu sassaƙa turmi za kai jigum kana dambarwa,

    Noma ko ya zamo tushenmu da shi muke tufa da ciyarwa.

     

     

    Bajimin gari na Kanawa mai kasuwar da ta fi ta kowa,

    Muke da kasuwa ta Dawanau Kantin-kwari ku je Hausawa,

    Muke da kasuwar al’ada Kurmi fa kasuwar dukawa,

    Sabon Garin Kano ga Rimi bayan asibiti ta Kanawa.

     

    Muke da kasuwar Ƙofar Ruwa muke da kasuwar Nasarawa,

    Muke da kasuwar Singar nan ga abatuwa tumbin giwa,

    Muke da kasuwar Gama Otel sannan Tudun-wada san kowa,

    Muke da kasuwar Mariri ‘yan goro sai ku je sarowa.

     

    Muke da ‘Yan-kaba ‘yan gwari ga ‘yan lemo dake Na’ibawa,

    Muke da ‘Yan-awaki Kanawa ga kasuwar Daham nan baiwa,

    Ina da mai ado da tagulla sai kasuwa ta Kyau ta kanawa,

    Sarƙar gwalagwalai da azurfa har yaƙutu kana samowa.

     

    Mu tambarinmu tumbin giwa komai ka zo kana samowa,

    Mu ne matattarar al’ummai baƙon Kano yana walawa,

    Muke da masu sauƙar baƙi cuɗanyarmu tana birgewa,

    Kar ka taɓo fagen malumai mun sanƙe kudu da arewa.

     

    Sannan fagen siyasa dage mu munka zama doron kowa,  

    Muke da dandazo na mawaƙa in mun amo yana sadarwa,

    Komai kake so da ya karɓu kawo Kano ka zo ka kasawa,

    Albarkaci na manzon Allah sai ya keta ƙasashen kowa.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.