8.9 Zuciya - Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA) (Page: 406)

    Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0.

    Wa ya gagara koyo Allah,

    Matarbiyar mai koyo Allah,

    Makai kukan mai wayyo Allah,

    Majarrabin mai wayo Allah,

    Ka sa a min oyoyo Allah,

    Ranar da wasu ke wayyo Allah.

    Wa ya gagara koyo,

    Matarbiyar mai koyo,

    Makai kukan mai wayyo,

    Majarrabin mai wayo,

    Ka sa a min oyoyo Allah,

    Ranar da wasu ke wayyo Allah.

     

    Alo alo dangina.

     

    Mai abin yabo ke kushewa,

    Rawar gani ke takawa,

    Mai abin ka shi ke saida wa,

    Mai abin faɗake furtawa,

    Mai bikin zuwake cashewa,

    Mai abin gudu ke gocewa,

    Ga shirina dagar shayawa,

    Su matsoraci ke zullewa,

    Ga nina fito ba komawa,

    Ɗan halak fa ba ya fasawa,

    Ya madogara ta Jallallah,

    Nai roƙo da kai ba ƙosawa,

    Mai roƙo da kai bai taɓewa,

    Ya madogar bayi Allah,

    Mai tsare mutuncin Abdallah,

    Ɗaukakatana gun Jallallah,

    Yarda duk ya so yai ba hila,

    Haka za ta wanzu ibadullah.

     

     

    Ya madogar bayi Allah,

    Wanda duk ya dogara ba ƙila,

    Ya ɗafe wa turba ba illa,

    Babu mai gani baike walla,

    Koko mai ganin walle illa.

     

    Ya madogarata Jallallah,

    Nai roƙo da kai ba ƙosawa,

    Mai roƙo da kai bai taɓewa.

     

    Mai kaza a ƙugu bai jimirin asa asku duba dangina,

    Gana faɗa a cikin waƙar mai gidan gilashi baitina,

    Sara da sassaƙa ba ya kashe gamji duba kalmana,

    Gana faɗa a waƙar wanzami a baya a baitina,

    Kainuwa dashen sa Jallallah ba dashe na jinni da insana,

    Hakananna furta a lu’u-lu’u bakandamar waƙoƙina,

    Ga shi maƙiyana sun fara bayyana a fili dangina,

    Zamanin ga riga ta sawana saka idanuna kaina,

     

    Ya madogara ta Jallallah,

    Nai roƙo da kai ba ƙosawa,

    Mai roƙo da kai bai taɓewa,

    Mai amon a ji ke ƙwallawa,

    Mai abin ga ni ke hangowa,

    Mai kamar zuwa ke aikawa,

    Mai abin a karɓa ke baiwa,

    Rabbi kai kaɗai zan godewa.

     

    Godiya ga Allah Sarkina,

    rabuwar da nai da Abbana,

    Godiyar ga da in Allahna

    Da zamantakewar Momina,

    Ka sa mu ga kyan ƙarshen kwana,

    Za ni mu shuka irin ɓarna,

    Kanai mu shuka irin ɓarna,

    Ka sa mu ga kyan ƙarshen kwana.

    Daga Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.