Citation: Sani, A-U. (2021). Fasihahhiya: Gudummuwar Farfesa Ibrahim Ahmad Mukoshy a Fagen Kimiyyar Harshe. In Yakasai. S.A. et al (eds), A Great Scholar And Linguists: A Festchrift in Honour of Professor Ibrahim Ahmad Mukoshy, Pp, 537-543. Kaduna: Amal. ISBN 978-978-59094-3-2.
Fasihahhiya: Gudummuwar Farfesa Ibrahim Ahmad Mukoshy a Fagen Kimiyyar Harshe
Na
Abu-Ubaida Sani
Department of Educational Foundations
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Phone No: 08133529736
Email: abuubaidasani5@gmail.com
J - Jalla maƙagin kowa,
Allahu mai rayawa,
Gare ka nai roƙowa,
Na ilmi har ma baiwa,
Kullum ba ka gajiyawa.
I - Ilahu yau ma ga ni,
Sai dai a yau ta sauya zani,
Domin kusan karambani-
Na ne kawai ya saka ni,
Wannan aiki nai farawa.
N - Na soma aiki mai tsauri,
Batu a kan mashahuri,
Da ke buƙatar tsari,
Da zurfafawar nazari,
Ƙimarsa na ruɗarwa.
J - Jalla ba za ni iya ba,
Tab! Ba na ma fara ba,
Da son ka Sarki Rabba,
Zan yi shi ba tababa,
Abin yana rikitarwa.
I - Idan rana ta fitowa,
Tafi fa bai karewa,
Muruci in ya fitowa,
Ga dutsi yai shiryawa,
Ka fi su sai hangowa.
N - Na so a ce ku biyo ni,
Mu taka dukkan tsani,
Tare da ku kuma ga ni,
Domin ku fahimci bayani,
Kansa gwani ɗan baiwa.
A - A farko dai sunansa,
Ibrahim Ahmad sunansa,
Mukoshy inkiya nasa,
Maiwurno ne tushensa,
Sakkwato can gun baiwa.
G - Gimshi wajen ilimi ne,
Idan batun haifa ne,
Ɗai ga wata na ɗaya ne,
Na shekarar nayintin ne,
Sai foti wan ɗorawa.
A - Akwai ɗiya shida gunsa,
Jamilu babban ɗansa,
Ahmad Rufa’i ka bin sa,
Sai Faɗima ban Musa,
Mamman da Maimuna nawa.
F - Firɗi! Batun karatunsa,
Maiwurno yai farkonsa,
Da ke Sudan can nesa,
Nayintin foti sabin sa,
Sai fifti wan ƙarewa.
A - Al’mahad Al-ilmin nan,
Da ke a Omdurman ɗin nan,
Intermediate School ɗin nan,
Nayintin fifti tu ɗin nan,
Fifti sabin ya yi kammalawa.
R - Rankayawa yai sakandari,
A Khartoum can yai nazari,
Captic College wurin nazari,
Nayintin fifti ed fari,
A sisti ed yai ƙarewa.
F - Farko nayintin sisti tiri,
Ibadan ya fara yin digiri,
Yunibasiti nan yai nazari,
A sisti fo cikon ƙuduri,
Ashekar yai ƙarewa.
E - Elum boko bai masa ba,
Domin bai tsaya haka ba,
Sai da ya ƙara ciwo gaba,
Karatu tuni ya zam babba,
Tabbas ko ya yi ƙwarewa.
S - School of Oriental ya je,
London can ƙasar waje,
Jami’ar Wisconsin ya je,
Da ke a USA ta waje,
Duk ilm yai ƙarowa.
A - Akwai yunibasitin nan,
Sudan a Khartoum ɗin nan,
Tuni ya je har wannan,
Domin biɗar ilmin nan,
Babba abin gaisarwa.
I - Idan ko kwalifikeshin ne,
Tuli garai kowanne,
Abin a-zo-a-yaba ne,
Arabik wannan Ibadan ne,
Yunibasiti yai amsowa.
B - B.A. a harshe da al’ada,
Wisconsin can ya ida,
M.A. a Linguistics wanda-
Wisconsin shi ma ya ida,
Abin gwanin ban sha’awa.
R - Rawar ganin da ya taka,
Yunibasiti da ya sauƙa,
Can Khartoum ba shakka,
Hakan a Linguistics ya saka,
Ph. D. yai samowa.
A - In batun harshe kuwa,
Yana fahimtar da yawa,
Sa Larabci farawa,
Da Ingilishi daɗawa,
Fillanci ya yi ƙwarewa.
H - Har French yai ganewa,
Hausa ko sai ƙyalewa,
Domin ko ya yi ƙwarewa,
Ya yi fice da zarcewa,
Fitilarsa na haskawa.
I - Idan batun littafai ne,
Ya yi tuli kowanne,
Abin a-zo-a-gani ne,
Suna ilmantarwa ne,
‘Fulɓe’ kui dubawa.
M - Mutuncin Shehu ya duba,
Ya zayyano ba wai ba,
Siffofin Shehu je duba,
Transciency Nomadism duba,
Mobile Education Kammalawa.
A - A Fulfulde-English Dictionary,
Wannan an masa tsari,
Tindinore Demuwa ya yi ƙari,
Kaɗan ke nan cikin tari,
Yawansu ya fi ƙirgawa.
H - Haka yai littafai da yawa,
Sun fi gaban ƙirgawa,
Sannan editan masu yawa,
Gime Fulfulde farawa,
Sannan da wasu da yawa.
M - Matsayi ya fa rirriƙe,
Mai ji zai yo kasaƙe,
Nauyin kansa ya sauƙe,
Cikin adalci ya riƙe,
Kowa yana ta yabawa.
A - A ɓangaren koyarwa,
Ya je makaranti da yawa,
Kamar a Sokoto farawa,
Nizamiyya yai koyarwa,
Kowa yana ta yabawa.
D - Daɗi an ji a Ibadan,
Aikin da yai gadan-gadan,
Sun so riƙe shi har abadan,
A yunibasiti na Ibadan,
Kowa yana ta yabawa.
M - Mukoshy har a London ma,
Ya nuna ɗabi’un girma,
A jami’ar S.O. gama,
Ya yo aiki babu zama,
Sabo da zimmar koyarwa.
U - UDUS garai ai gida ne,
A ABU sananne ne,
BUK ma sananne ne,
Unimaid ba baya ba ne,
Har Khartoum ya yi koyarwa.
K - Kowa yana son barka,
Da fatar ƙara ɗaukaka,
Al’umma duk na son ka,
Saboda kyawun halinka,
Da ƙoƙarin ilmantarwa.
O - Organized mai recognition,
Ga Allah shi yai submission,
Gaskiya yai adhesion,
Outstanding in nation,
Farfesa ka sam dacewa.
S - Sannan yana da karamci,
Ga shi da kirki da mutunci,
Faɗin gaskiya duk ɗaci,
Amana ba ha’inci,
Rayuwar abin burgewa.
H - Har kullum kai dace,
Wannan gare ka du’a’i ce,
Aljanna ga kai ta kasance,
Makoma wurin hutawa.
Y - Yawan baitukan talatin ne,
Sai shida ‘yan ƙari ne,
Na ƙanƙanin ɗalibi ne,
Abu-Ubaida sunan ne,
Hamdan nai ƙarewa.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.