Gauta a Rana

    Wannan na ɗaya daga cikin jerin waƙoƙin Malam Khalid Imam da a kullum suke faɗakarwa da ilimantarwa da nishaɗantarwa. Yana taɓo fannoni daban-daban a cikin waƙoƙinsa, ciki har da abubuwan da suka shafi lamuran yau da kullum.

    Sun kasafta jihar ga kansu,

    Su da mataye da 'ya'ya.


    Wannan ya wafce Daba,

    Otal gun sauke baƙi.


    Wancan ya ba wa kansa,

    Daula Otel na birni.


    Wai da sunan masu jari,

    Sun sa jari su raya.


    Sun rabe wa kan su GP,

    Gidajen gwamnatinmu.


    Sun yi kab awut na fili,

    Duk sun saidawa kansu.


    A makarantun Jiharmu,

    Kasuwanni maƙabartu.


    Shaguna suka daddasa nan,

    Wasu can su masu wayo.


    Kura a wajen zalama,

    Take afkawa tarko.


    Masallaci na Idi,

    Balada sun cefanar ta.


    Abokai sun rarraba wa,

    Da kawalai su da dangi.


    Sun tsaya wawa da sata,

    Jihar Ikko ta yi nisa.


    Ariya boyis na titi, 

    Da ke Ikko babu su yau.


    Masu ƙwace waya da rana,

    Da fizge jaka a titi.


    Masu shan wiwi muraran,

    Suna cin kasuwarsu.


    Da yawa marasa sana'a,

    Samari na Kanonmu.


    Kwamnoni ko na Ikko,

    Sun share dukkaninsu.


    Gwamnoni su na Ikko,

    Suna kishin Jiharsu.


    Sun bai wa kasuwanci,

    Zuba jari lokacinsu.


    Da hankaka da shaho,

    Mu a nan ba sa ta tamu.


    Ta kan su suke a kullum,

    Su washe dukiyarmu.


    Sannan gaba da juna,

    Shi ne suka bai wa himma.


    Baƙin son kai na kura,

    Ke sa ta fashi da rana.


    Damisa kuwa dai zulama,

    Ke sa bishiya takan hau.


    Don kar kura da zaki,

    Su ɗanɗani nata kamun.


    Babban ligasin su shirwa,

    Da ungulu nai bayani.


    Namau Jimrau da Ƙosau,

    Shin wane ne waliyi?


    Magana Jari ku leƙa,

    Duk mai neman bayani.


    Ɓera burgu da dunka,

    Halinsu iri guda ne.


    Ko sun bamban a suna,

    Sata ita ce halinsu.


    Gafiya jaɓa muzuru,

    Ba a ba su riƙon amana.


    Sun maida Jiharmu baya,

    Sun tsaya sai sace-sace.


    Har jariran Jihohi,

    Yau ga da yawa gabanmu.


    Su dai a zatonsu mulki,

    Shi ne kwasar ganima.


    Yau ga shi a kan idonmu,

    Su ke tonawa kansu.


    Asiri sirrukan su,

    A faifai sun baje su.


    Kura in ta ci kura,

    Wataƙil jama'a su gane.


    Cewa gauta a rana,

    Za sui ja daina shakka.


    Ni takaici na guda ne,

    Ba sa kishin Jiharmu.


    Nutsuwa ke sa a gane,

    Bula ce ayyukansu.


    Duk mai shakka ya leƙa,

    Asibiti makarantu.


    Kwalbatoci sun yi shago,

    Ruwa na cin gidaje.


    Ba ruwa ko ɗan ɗigo ɗis,

    Na famfo yau a birni.


    Ba sa kishin su kwashe,

    Dalar bola a birni.


    Uwarsu suke wa fyaɗe,

    Da kan su ana ganinsu.


    In ka ce ya hakan nan,

    Don me za sui hakan nan.


    'Yan kore da masu fince,

    Su ma ca za su cinye.


    Allah yau ga uwarmu,

    Ɗauki kawo gare ta.


    Na sa aya a nan ni,

    Khalid Imam na Indo.


    Ango ne gun Hadiza,

    Baban Ahmad Jamilu.


    Haka ma Khalid Shuaibu,

    Duk 'ya'ya ne gare ni.


    Kuma su ma 'yan Kano,

    Suna kishin Jiharsu.


    Duk mai kishin Kanonmu,

    Zai tir da halin su shaho.


    Da hankaka da shirwa,

    Kaza ba ta ganinsu.


    Ta bar tsaki a hanya,

    Duka sharri ne cikinsu.

    Malam Khalid Imam
    08027796140
    khalidimam2002@gmail.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.