Ticker

    Loading......

Haddin Wanda Ya Auri Matar Babansa Ko 'Yarsa

Shari'ar musulunci ta halatta jini da dukiyar wanda ya auri matar babansa ko '‘yarsa, saboda ya halatta abinda ALLAH ya haramta.

 Daga Barra'u (R.A) Ya ce:

Na gamu da Ammina yana ɗauke da tuta tare dashi, sai nace ina ka nufa?

Sai ya ce:

 Manzon ALLAH {s.a.w} ne ya turani izuwa wani mutum daya auri matar mahaifinsa, kuma ya umarceni da na sare kansa na kuma kwaso dukiyarsa.

 Saboda haka halatta abinda ALLAH ya haramta kafirci ne, ridda ne, barin musulunci ne, duk wanda ya halatta abinda ALLAH ya haramta haƙiƙa ya yi ridda, ya zama kafiri.

 Don haka auren matar mahaifinka ko da bayan mutuwarsa ne, ko mutum ya auri '‘yarsa yana sane bawai a rashin sani ba, to wannan kafirci ne, hukuncin kisa yahau kansa.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments