Idan Mutum Ya Yi Umurah Zai Iya Yin Aikin Hajji Tumatu'i?

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum warahamatullah, malam dan Allah mutum ne ya yi umarah a watan shawwal to yanzu in mutum zai yi aikin Hajj Tumatu'i Sai ya sake wani umarah? Allah ya ba da ikon amsawa.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salamu Wa Rahmatullah, ‘yar uwa dama shi aikin Hajji na Tamattu'i malamai sun bayyana shi da cewa: Shi ne mutum ya yi aikin Umra a cikin watannin aikin Hajji, daga bisa kuma sai ya dawo ya yi aikin Hajji.

    Watan Shauwal yana daga cikin watannin aikin Hajji kamar yadda maz'habobi huɗu na Fiƙhu suka tabbar. Tun da haka ne to ashe ba sai kin sake yin wata umra ba, tun da dama Hajjin Tamattu'i shi ne maninyaci ya yi umra a watannin aikin Hajji, daga bisani kuma ya zo ya yi aikin Hajji.

    Watanin Aikin Hajji su ne Shauwal, da Zhulƙa'ada, da kuma Zhulhijja gaba ɗayansa a Maz'habar Malikiyya. Amma a maz'habar Hanafiyya, da Hanabila, watannin aikin Hajji su ne Shauwal, da Zhulƙa'ada da kuma kwanaki goma na farkon Zhulhijja.

    Allah S.W.T ne mafi sani.

    Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

     Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.