Kalmomin Fannu Na Wasannin Gargajiya (Keɓantattun Kalmomin Wasanni Da Ma'anoninsu) - Daga Littafin WASANNI A ƘASAR HAUSA (Page - xxviii)

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Kalmomin Fannu

A CikinWannan Rana: (A cikin wasar A CikinWannan Rana) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ake gudanarwa tsakanin rukunin masu wasa guda biyu. Na dandali ne, sannan yana tafiya da waƙa.

A Fiffigi Zogale: (A cikin wasar A Fiffigi Zogale): Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na gaɗa da ke ɗauke da waƙa mai nuna halayyar matan aure zuwa ga wasu mutane daga cikin danginsu da dangin mazajensu da kuma kishiya da danginta.

A Fim-Fim-Fim: (A cikin wasar A Fim-Fim-Fim) Ɗaya daga cikin nau’ukan wasannin mata na dandali da suke tafiya da waƙa da tafi.

A  Sha Ruwa: (A cikin wasar A Sha Ruwa) Wasan tashe ne na mata da ke ɗauke da waƙa.

A  Sha Ruwan Tsuntsaye: (A cikin wasar A Sha Ruwan Tsuntsaye) Wasa ne da yara biyu ke jeruwa sannan su mayar da hannuwansu baya tare da sarƙafa yatsun hannuwan nasu. Wani yaron kuma zai hau bisa hannuwan nasu da ƙafafunsa tare da dafa kafaɗunsu. Za su riƙa yawo suna waƙa yayin da yake ɗangalafe.

Afajana: (A cikin wasar Afajana) Wasan yara maza da suke aje riguna, sannan sarki da turke su tsaya daidai wurin da za a ɗauki rigunan. Sauran yara za su riƙa ƙoƙarin ɗaukar rigunan ba tare da sarki ya taɓa su ba. Duk wanda ya ɗauki rigarsa, zai riƙa dukan sarki da ita.

Afurka-Afurka: (A cikin wasar Afurka-Afurka) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke tafiya da waƙa.

Aika: (A cikin wasar Sabis) duba aike.

Aike: (A cikin wasar Sabis) yayin da ɗan wasa ya jambaɗi sabis da ƙarfi ƙwarai yadda har ta huce gabaɗaya abokan karawarsu, to ya aika abokan karawar.

Ajiye Sanda: (A cikin wasar sabis) 1: Yayin da wani ya shiga gidan abokan karawarsa da niyyar ya buga sabis, za su yi saurin furta wannan furuci kafin ya furta eskus, idan har sun riga shi, to abin da ya yi ya zama sata. Misali: Sun ambaci ~ saboda haka Musa ya yi sata. 2: Hukuncin da ake yi wa wanda ya yi sata. Zai ajiye sandansa a gidan abokan karawa sannan ya fita waje na tsawon wani lokacin da aka ƙayyade masa, kafin ya dawo ya ɗauki sandar domin ci gaba da wasa.

Alhaji: (A cikin wasar Sai Ka Yi Rawa A Nan) Sunan yaro ko yarinyar da ya/ta yi shigar dattijo yayin tashen.

Alhajin Ƙauye: (A cikin wasar Alhajin Ƙauye) 1: Wasar tashe ta yara maza inda ɗaya daga cikinsu ke shigar dattawa ya rataya jaka ya kuma riƙa dogara sanda. Wasan yana tafiya da waƙar da ke nuna cewa, wannan mai shigar dattawa Alhaji ne daga ƙauye wanda ya yi azumi zai je gida ga shi ba shi da kuɗin mota. 2: Sunan da ake kiran yaron da ya yi shigar dattawa yayin wasan.

Aliyar Gwangola: (A cikin wasar O Aliyu) Sunan wadda mijinta ya yi tafiya ya bar ta gida na tsawon lokaci a cikin wasan.

Allah Reni: (A cikin wasar Allah Reni) Wasan dandali na yara maza wanda ake rufe wa yaro guda ido. Sauran masu wasa za su riƙa tsallake shi ɗaya bayan ɗaya. Ga duk lokacin da aka tsallake za a bukaci ya bayyana sunan wanda ya tsallake shi. Idan ya bayyana daidai, wanda aka bayyana ne zai zauna a rufe masa idanu.

Allah Ya Ba Da Sa’a: Furucin da ake yi wa masu tashe a matsayin sallama yayin da ba za a ba su komai ba.

Allah Ya Ba Mu Ruwa: (A cikin wasar Allah Ya Ba Mu Ruwa) Wasar yara maza da mata da ake gudanarwa yayin da hadari ya taso tare da alamun ruwan sama.

Allazi Wahidun: (A cikin wasar Allazi Wahidun) Wasa ne na yara maza wanda ake amfani da takalmi a riƙa bugun ƙwallon goruba zuwa jikin abokan wasa. Duk wanda ƙwallon goruba ya taɓa shi, to zai sha duka.

Allazi: (A cikin wasar Allazi Wahidun) Suna ne da ake kiran duk wanda ƙwallon goruba ya taɓa ƙafarsa yayin da ake wasa.

Alo Na Taro Na Tattaro: (A cikin wasar Alo Na Taro Na Tattaro) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa, inda mai rerawa ke ambaton sunayen ƙawaye da ‘yan’uwanta.

Amali Kande: (A cikin wasar Amali Kande) Wasan dandali na yara mata da ke ɗauke da waƙa mai jan hankali game da auren dole.

Aminun: (A cikin wasar WaranWarash) Ɗaya daga cikin sunayen da masu wasa ke zaɓa.

Arbana: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na biyar a wasan babunna.

Aro: (A cikin wasar Guro) Yayin da ɗaya daga cikin masu wasan guro ya bayar da gida ko gidaje ga wani daban domin ya yi tafiya da su da nufin idan wanda aka ba wa ya jawo wasu gidajen zai miyar wa wanda ya ba shi abinsa, to an yi aro ke nan.

Artabu: (A cikin wasar langa) daidai da gwabza.

Ashobe: Ɗinka kaya iri ɗaya da ake yi (A cikin wasar musamman mata) yayin bukin aure ko na haihuwa.

Audu: (A cikin wasar Rabi Da Audu) Sunan mai yin shigar maza a cikin tashe; wadda kuma ke kasancewa mijin Rabi.

Ayye Mama: (A cikin wasar Ayye Mama) Ɗaya daga cikin wasannnin da ake gudanarwa yayin kai amarya. Yana ɗauke da waƙar bankwana ga amarya.

Ayye Rashidalle: (A cikin wasar Ayye Rashidalle) Wasan yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa mai faɗakarwa game da tsabta.

Ba ‘yar Zubel Ba: (A cikin wasar Babunna) Idan wasa ba ‘yar zubel ba ce, wacce aka ƙwace a arbana ko wani gaɓa na kaɗin wan tu fayif za ta ci gaba daga wurin da aka ƙwace ta idan yin ta ya zagayo.

Ba Dela Ba Kande: (A cikin wasar Ba Dela Ba Kande) Wasan dandali na yara mata da ke ƙunshe da waƙa mai nuna ɗarsashin zuciyarsu.

Ba Ga Shi Ba!: (A cikin wasar Babunna) Furucin da wadda ta ci nasararojo ke yi na nuna, da ma ita ke da gaskiya.

Ba Kya Ci Ba: (A cikin wasar Ni Kura-Kura) Furucin da ’yan wasa ke yi na nuna, kura ba za ta kama ko ɗaya daga cikinsu ba.

Ba Mu Kuɗinmu: (A cikin wasar Ba Mu Kuɗinmu) Wasan tashe na yara maza da ake goya wa ɗaya daga cikinsu matashin kai a baya, sannan su riƙa dukansa a wurin tashe da sunan ya ci musu bashin doya, shekara guda bai biya ba.

Ba Mu Saya Ba: (A cikin wasar Sabis) Furucin da abokan karawar gidan da ke ba da sabis ke yi da ke nuna cewa ba su aminta da sabis da aka ba su ba.

Ba Ta Gagarel: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Furucin da ake yi domin a nuna cewa, dokar wasan ba ta ba da dammar gagarel ba. Saboda haka, wadda ta yi gagarel ta faɗi kai tsaye.

Ba Ta Jira: (A cikin wasar Guro) Furucin da ake yi domin a nuna cewa, dokar gasar guro ta hana jira. Saboda haka, dole ne mai tafiya ya fara ba tare da ɓata wani lokaci ba.

Ba Ta Masar Baba ne: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Furucin da ke nuna dokar wasan ba ta ƙunshi masar baba ne ba.

Ba Ta Ƙirge: (A cikin wasar Guro) Furuci ne da ake yi kafin a fara wasa domin nuna cewa, dokar wasan ta hana ƙirge kafin tafiya.

Ba Ta Ƙonewa: (A cikin wasar Guro) Furucin da ake yi domin nuna cewa, dokar wasa ta ba da damar mai wasa ya ɗebe haihuwarsa ko da ta ƙone.

Ba Ta Sa Baki: (A cikin wasar girjim/Guro/Uku Saɓi/Siri-Santa) Furuci da ke nuna cewa, dokar wasa ta hana sa baki a wasan da ake gudanarwa.

Ba Ta Satar Gaba: (A cikin wasar ’Yar Ramel) Dokar wasa inda mai wasan da ta yi satar gaba ta faɗi.

Ba Ta Sizin: (A cikin wasar girjim) Furucin da ake yi domin nuna cewa, dokar wasan a wannan lokaci ta ba da dama a yi sizin.

Ba Za Ku Ga Tafiyar ’yata Ba: (A cikin wasar Ba Za Ku Ga Tafiyar ’yata Ba) Wasan yara maza da ya shafi ɓoye tsakuwa a cikin ƙasa tare da buƙatar abokin wasa ya nuna wurin da aka ɓoye.

Wandara a Sha Maganin Ƙaba: (A cikin wasar Wandara a Sha Maganin Ƙaba) Wasan tashe na manya maza inda ɗaya daga ciki ke shigar dattawa sannan ya rataya abu cikin riga a matsayin gwaiwa/ƙaba.

Baba Mai Gadi: (A cikin wasar Baba Mai Gadi) Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga cikin yaran ke shigar tsofi ya kuma riƙe sanda. Zai riƙa rawa yayin da sauran yara ke tambayarsa cikin waƙa ko rawar coko zai yi? Shi kuwa zai riƙa ba da amsa da cewa masallaci zai je, kada kuma su sa shi ya haukace. 2: Sunan yaron da ya yi shigar tsofi yayin wasa.

Baba: (A cikin wasar Ba Mu Kuɗinmu) Duk wani mutum da ka iske a wurin tashe.

Baba: (A cikin wasar Wandara a Sha Maganin Ƙaba) Wanda ke shigar dattijo mai ƙaba yayin tashen.

Baba: (A cikin wasar Na Ci Na Kasa Tashi) Wanda ake sanya wa tsummokara cikin riga yayin wasa.

Baban Dudu Zai Gudu: (A cikin wasar Baban Dudu Zai Gudu) Wasan tashe na yara maza inda Baban Dudu ke yin shigar tsofi ya kuma ɗauko faggon kaya. Waƙar wasan na nuna cewa, Baban Dudu zai gudu ne saboda auren Dudu ya matso kuma ba shi da kuɗin aurar da ita.

Baban Dudu: (A cikin wasar Baban Dudu Zai Gudu) Yaron da ke shigar tsofi a cikin wasan.

Babana Ya Sami Min Ƙwallo: (A cikin wasar Babana Ya Saya Min Ƙwallo) Wasan yara maza ne masu ƙarancin shekaru. Yana ɗaya daga cikin wasannin da ake yi da ƙasa.

Babu: (A cikin wasar Jini Da Jini): Furucin da masu wasa ke yi yayin da aka ambaci sunan abin da ba shi da jini, kamar akwati ko randa da sauransu.

Babunna: (A cikin wasar Babunna) 1: Wasa ne mai sigar Ɗan Balum-balum da ake tsalle-tsalle da tafi da kuma buɗe ƙafa da tsukewa. Sai dai waƙar da ake yi ciki ta bambanta da na Ɗan Balum-balum. 2: Kaɗin farko na wasan babunna a cikin kowace randa.

Bafade: (A cikin wasar ’Yar Ganel) Wanda ke ɗauko saƙo daga sarki zuwa ga ‘yan wasa yayin da ake wasan.

Baji: (A cikin wasar Carafke) Barbaza ’ya’ya a ƙasa yayin fara carafke.

Bakwalwa: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke’ya’ya bakwai kafin mayar da saura rami.

Balo-Balo: Wani abin wasan yara da ake sayarwa a kantuna, wanda ake hurawa iska ya kumbura.

Bangaza :(A cikin wasar  langa) Hankaɗe ko turo ɗan wasa da ƙarfi da nufin kasha shi. Misali: Musa ya ~ ƙirjin Sale.

Baran Baji: (A cikin wasar Baran Baji) 1: Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga cikinsu ke shigar mata. Akan yi amfani da kayan aikin gida dangin turmi da taɓarya da faifayi da makamantansu. Yana tafiya da waƙar da ke nuni da cewa, tafiya mabuɗin ilimi ce. 2: Sunan wanda ya yi shigar mata yayin wasan.

Barkwanon Tsohuwa: (A cikin wasar Yaƙi) Toka da dakakken yajin barkwano da ake haɗawa a leda domin baɗa wa abokan karawa wurin yaƙi.

Basha: (A cikin wasar Basha) 1: Wasan mata na dandali da ake gudanarwa da azumi. 2: Mutumin da masu wasan basha suka ƙudurta a rai cewa, tsoronsa ne ke hana’yan mata fitowa wasa.

Ba-taɓe Ce: (A cikin wasar Guro) Furuci da ke nuna cewa, dokar ba-taɓe za a yi amfani da ita a wasan guro.

Ba-taɓe: (A cikin wasar girjim) Dubaba-taɓe (A cikin wasar Guro).

Ba-taɓe: (A cikin wasar Guro) Dokar guro da ke tilasta mai wasa ya yi tafiya da ‘ya’yan gidan da ya taɓa da farko. Wato bai isa ya taɓa’ya’yan wani gida ba, kuma ya fasa ya yi tafiya da ‘ya’yan wani gida na daban.

Bayarwa: (A cikin wasar Langa) Kalma da ke nuna ruwa ta shirya kuma ta yarda a fara langa. Misali: Garin ruwa ne ke ~.

Belbela-Belbela: (A cikin wasar Belbela-Belbela) Wasan yarar maza ne da ke da tsarin shugabanci, wanda kuma ke da sigar salla. Bayan an gama rera waƙar wasan, kowa na ƙamewa ba tare da motsi ba.

Bena: (A cikin wasar Bena) Ɗaya daga cikin nau’ukan wasannin yara mata da ake tsanen gidaje a ƙasa sannan ake amfani da ƙaramin dutse ko fashasshiyar kwalba ko wani abu mai kama da wannan a matsayin ‘yar tafiya. Akan yi tafiya ne da ƙafa ɗaya ta hanyar tsalle. Wasan yana da dokoki da dama.

Bindiga: (A cikin wasar Bindiga) Wasan yara maza inda suke amfani da ƙaramin katako ko falanki su yanke shi zuwa siffar bindiga, sannan su sanya ƙarfe mai kwararo a tsakiya su kuma ɗaure da roba. Akan yi amfani da garin kan ashana wajen ɗuri. Sannan bindigar kan ba da ƙara yayin da aka buga.

Birki: (A cikin wasar Taya) Tsumma ko igiya da ake ƙullawa jikin taya, wadda ake ja yayin da ake so ta tsaya.

Biyar Ko Goma: (A cikin wasar Biyar Ko Goma) Wasan yara maza da mata da ake amfani da ɓawon gyaɗa guda biyu. Akan dunƙule ɓawon gyaɗar cikin tafukan hannu, a kuma jijjiga, sannan a zubar ƙasa. Za a samu maki ko a faɗi, wanda ya danganta da kasancewar ɓawon gyaɗar sun buɗe gaba ɗaya, ko sun kife gaba ɗaya, ko ɗaya ta buɗe ɗaya ta kife.

Biyarwa: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke biyar kafin mayar da saura rami.

Biyulwa: (A cikin wasar ‘yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke ‘ya’ya biyu kafin mayar da saura rami.

Boka Kake Ko Malami: (A cikin wasar Boka Kake Ko Malami?) Nau’in tashe na maza manya inda ɗaya daga cikin masu wasa ke shigar malamai. Wasan na hannunka-mai-sanda kan cewa a yi hankali game da malamai da kuma malaman tsubbu.

Bori: (A cikin wasar gori/koɗi) Kalmar da ake amfani da ita don bayyana halin da koɗi take ciki na rawa da karkarwa da take yi saboda rashin zaƙi.

Bugawa: (A cikin wasar Bindiga) Matsa robar da ta riƙe wayar gareren keke domin ta bugi garin ɗuri; wanda hakan zai sa bindiga ta tashi.

Bugu: (A cikin wasar ‘Yar Cille) Doke‘yar cille da mai cilli zai yi da sanda yayin da mai kamu ya jefo ta.

Bukka Kora Ne: (A cikin wasar Guro) Furuci da ke nuna cewa, dokar guro da ake amfani da ita a lokacin da aka yi wannan furuci ya zartar cewa, duk wanda aka kai shi bukka, to daidai yake da an tatike shi.

Bukka: (A cikin wasar Guro) gida ɗaya da ya rage wa mai wasan guro.

Buƙulu: (A cikin wasar Guro) Yayin da mai wasan guro ya yi tafiya da wani gidan da bai dace ba don kawai kada abokin karawarsa ya haihu, to ya yi wa abokin karawarsa buƙulu.

Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu: (A cikin wasar Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu) 1: Wasan tashe na yara mata da suke kwaikwayon tafiya da ɗabi’un manyan mata masu girman jiki. 2: Sunan da ake kiran ɓakutu a cikin wasan ɓakutu mai babban ɗuwawu.

Ɓakutu: (A cikin wasar Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu) Jagora a cikin wasan ɓakutu mai babban ɗuwawu.

Ɓarawo Me Ka Sata: (A cikin wasar Ɓarawo Me Ka Sata) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa.

Ɓarawo: (A cikin wasar ‘yar Sarki 1) Wanda ya yi sata yayin wasan.

Ɓata: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Lokacin da aka rasa ɗaya daga cikin ‘ya’yan wasa ko sama da haka.

Ɓata: (A cikin wasar Jini Da Jini) Yayin da mai wasa ya furta danja ga halittar da ba ta da jini, ko ya furta babu ga halittar da take da jini, to ya ɓata. Saboda haka zai fuskanci hukunci.

Ɓata: (A cikin wasar Ɓelunge) Wanda ya yi magana ba a daidai lokacin da ya dace ya yi ba, to ya ɓata wasa. Irin wannan yaro zai fuskanci hukuncin duka da rigar da aka nannaɗe.

Ɓelunge: (A cikin wasar Ɓelunge) Wasan dandali na maza da ke da sigar salla. Akan samu liman wanda zai fara gabatar da aiki, sai ladan ya yi sai kuma mamu. Wanda ya ɓata, zai fuskanci hukunci.

Ɓigo: (A cikin wasar Ɓigo) Wasan yara maza na dandali da ake gudanarwa tsakanin ɓangarorin ‘yan wasa biyu. Ya ƙunshi guje-guje da kuma duka da riga.

Ɓoyel 2: (A cikin wasar Ɓoyel 2) Wasan yara maza da mata inda akan yi tsubi-tsubi da ƙasa sannan a ɓoye tsakuwa ciki, a kuma nemi abokin wasa ya nuna cikin tsubin da aka ɓoye ƙasar.

Caccayya: (A cikin wasar Caccayya) Wasan yara maza da mata da ake gudanarwa yayin da hadari ya taso tare da alamun ruwan sama.

Cafewa: (A cikin wasar ‘Yar Ramel/Carafke) Cafke ƙodo da mai wasan ‘yar carafke ke yi bayan jefa wasama.

Cafewa: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Kama ‘yar wasa.

Cafkel: (A cikin wasar Carafke) Tsintar ko ɗaukar ‘ya’ya daga cikin jeri bayan an wurga ƙodo sama.

Cake: (A cikin wasar ‘yar Cake) Kafewar da abu mai tsirin da aka jefa ke yi a ƙasa.

Canji: (A cikin wasar Bena) Sauƙe ƙafar da aka ɗage tare da ɗage wadda ta ke ƙasa cikin gaggawa. Dole ne a ɗage wadda take ƙasa kafin wadda take ɗage ta taɓa ƙasa.

Canjin Gari: (A cikin wasar Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba) Daidai da canjin gida.

Canjin Gida: (A cikin wasar Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba) Shugabanni ne ke canjin gida, inda kowace za ta koma ɓangaren abokan wasansu.

Canjin Gida: (A cikin wasar Jallu Wa Jallu) Juyawa ko musanyen gidaje da akan yi tsakanin masu wasa yayin da aka ƙare rakiyar-kura.

Canka: (A cikin wasar ‘yar Canka) Zaɓen hannun da ake tunanin ciki aka ɓoye tsakuwa.

Canka: (A cikin wasar Ba Za Ku Ga Tafiyar Yata Ba) Nuna wurin da aka ɓoye ‘ya.

Cankuloto-Kuloto: (A cikin wasar Cankuloto-Kuloto) Wasan yara maza da mata da ke da zubi da tsari irin na wasan Lakkuma-Lakkuma Lale. Amma waƙoƙin cikinsu sun bambanta.

Carafke: (A cikin wasar Carafke) Wasan da ake jefa ƙodo sama tamkar na‘yar ramel, sai kuma a riƙa tsinar ‘ya’ya da aka yi baji da su.

Carmama: (A cikin wasar Carmama) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke ɗauke da waƙa mai nuna ɗarsashin zuciya.

Carman Dudu: (A cikin wasar Carman Dudu) 1: Wasan gaɗa na dandali da ke tafiya da waƙa. 2: Sunan waƙar da ake yi a cikin wasan carman dudu.

Casana: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na goma a wasan babunna.

Ci Biyu: (A cikin wasar girjim) Cin‘ya’ya biyu a tafiya ɗaya.

Ci: (A cikin wasar girjim) Tsallake ɗan abokin karawan da akwai gida a bayansa tare da ɗauke shi a matsayin wanda aka cinye.

Ci: (A cikin wasar Lakkuma-Lakkuma Lale) Sakamakon wasa, inda wanda za a ci zai haɗa tafukan hannayensa, saura kuwa su riƙa marin bayan hannuwan.

Ci: (A cikin wasar Ni Kura-Kura) Yayin da kura ta kama ɗaya daga cikin‘yanwasa, ta cinye ta ke nan.

Ci: (A cikin wasar Waran Warash) Duba ci (A cikin wasar Lakkuma-Lakkuma Lale)

Ciki: (A cikin wasar Guro) Yayin da ‘ya’ya suka kasance guda biyu a wani gida bayan an fara tafiya, to an samu ciki a wannan gida.

Ciki: (A cikin wasar Maimuna Ta Yi Ciki Ga Goyo) Tsummokara da aka tura cikin rigar Maimuna aka ɗaure ɗamar da zane domin ya tsaya a matsayin ciki.

Cilli: (A cikin wasar ‘yar Cille) Yin amfani da icen bugu domin a jefa‘yar cilli.

Cilli: (A cikin wasar ‘yar Ramel/Carafke) Jefa ƙodo sama yayin wasa.

Cilli: Tura ‘yar wasa gaba da masu wasa ke yi yayin da ta faɗo jikinta kuma suka cafe ta. Wannan na faruwa ne a wasannin yara mata da ke da tsarin cilli da direwa.

Cillo-Cillo: (A cikin wasar Cillo-Cillo) Ɗaya daga cikin wasannin dandali na yara mata inda ake amfani da kallabi ko zane ko tsumma mai ƙarfi wurin lila ‘yan wasa ɗaya bayan ɗaya.

Cin Dawo: (A cikin wasar Cin Dawo) Wasan yara mata na dandali da ake gudanarwa a zaune. Yana ƙunshe da waƙar da ke tattare da faɗakarwa.

CinFita: (A cikin wasar Gori/koɗi) Cin da ake yi wa ɗan wasan da ya nuna zai fita alhali ba a kamala wasa ba.

Cincin Sakatum: (A cikin wasar Cincin Sakatum) Wasa ne na yara maza da ake gudanarwa a dandali. Yana tafiya da waƙa, wadda yayin da ta ƙare a kan ɗan wasa, to ya fita.

Ciniki: (A cikin wasar Robali) Yayin da mai kanti ya tara robali da yawa a kanti, to ya yi ciniki.

Coge: (A cikin wasar Guro) Yin tsallake ko sanya ‘ya’ya sama da ɗaya a rami guda da gangan domin neman samun nasara.

Cuwa-Cuwa: Ha’inci ko coge ko rashin gaskiya a yayin wasa.

Dabi: (A cikin wasar langa) daidai da gwabzawa.

Daga: (A cikin wasar langa) daidai da gwabzawa.

Dala: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Hukunci a matsayin sakamakon wasa. Akan bisne ‘ya’yan ‘yar ramel cikin ramin ‘yar ramel sannan wanda za a dala ta ɗora hannu bisa kai. Daga nan sauran masu wasa za su riƙa dunƙule hannu suna dukan hannun nata.

Dala: (A cikin wasar Carafke) Duka da takalmi bayan wadda ake dala ta haɗa tafukan hannuwanta, a matsayin sakamakon wasa.

Dala: (A cikin wasar Na Ɗiba) Sakamakon da ake zartarwa ga wanda tsinke ya faɗi yayin da yake ɗibar ƙasa. Za a tara ƙasa sannan ya kifa tafin hannunsa a kai. Masu dala za su riƙa dunƙule hannu suna dukan bayan hannunsa.

Dama Take Yi: (A cikin wasar Guro) Furuci da ke nuna cewa, ta dama ake yin tafiya ba hagu ba.

Damo Riya Damo: (A cikin wasar Damo Riya Damo) Wasa ne da ke da zubi da tsari irin na wasan belbela-belbela. Sai dai a wannan wasa, a maimakon a ƙame bayan an kamala waƙa, akan yi shiru ne kawai. Ma’ana, ba za a ambaci amshin waƙar ba yayin da Jagoran wasa ya rero ɗiyan ƙarshe na waƙar.

Damo: (A cikin wasar Damo Riya Damo) Furucin da masu wasa suke yi a matsayin amshin waƙar wasa. Yaron da ya yi wannan amshi bayan jagora ya rero ɗiyar waƙar ƙarshe, to ya ɓata wasa.

Danda Dokin Kara: (A cikin wasar Danda Dokin Kara) Wasan tashe na yara maza inda yaro guda ke hawa dokin kara lokacin tashe.

Danda: (A cikin wasar Danda Dokin Kara) Laƙabin da ake wa dokin karar da aka shirya lokacin wasan.

Danja: (A cikin wasar Jini Da Jini): Furucin da masu wasa ke yi yayin da aka ambaci sunan halitta mai jini, kamar akuya ko rago da sauransu.

Daƙu Fara: (A cikin wasar Daƙu Fara) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na zaune, da ke ɗauke da waƙa mai nuna muradin zuci na masu wasa musamman ta fuskar aure.

Daudu: (A cikin wasar Ga Mairama Ga Daudu) Yarinyar da take shigar maza a yayin wasan.

Digi-digi: (A cikin wasar Digi-digi) Wasan yara mata da ake yin da’ira sannan a riƙa waƙa. Wanda waƙa ta faɗa kanta, to ta fita.

Dinga-Dinga: (A cikin wasar Dinga-Dinga) Wasan tashe ne na yara mata inda suke jan hankali zuwa ga iyaye game da ɗinka wa ‘ya’yansu kayan salla.

Direwa: Faɗowa jikin masu wasa tare da dira yayin da sauran masu wasan suka cilla‘yar  wasan da ta faɗo gare su. Direwa na faruwa cikin wasannin da ke da tsarin cilli da direwa.

Dirƙe-Dirƙe: (A cikin wasar Dirƙe-Dirƙe) Wasan yara maza da aka fi gudanarwa a rafi da ke da yashi. Yara za su riƙa dira daga wuri mai ɗan tsayi zuwa cikin yashin.

Doguwar Tafiya: (A cikin wasar Girjim) Tsallake gida ko gidaje yayin tafiya. Sarki na da fawar doguwar tafiya.

Dokawa: (A cikin wasar Basha) Buga kafaɗu da masu wasa ke yi cikin ƙoƙarin ka da juna.

Doki: (A cikin wasar Dokin Kara) Karar da aka ƙuƙƙulla wa ƙyallaye da igiya (A cikin wasar linzami) a matsayin doki.

Dokin Almajire: (A cikin wasar Dokin Almajire) Wasa ne na yara maza inda wani ke sunkuyawa, wani yaron kuma ya hau bayansa. Su riƙa tafiya, tare da ɗan jagora wanda shi kuma na sunkuye zai dafa kafaɗarsa. Wasan yana tafiya da waƙa.

Dokin Kara: (A cikin wasar Danda Dokin Kara) Karan dawa mai ƙarfi da ake wa kwalliya da ƙyallaye domin amfani da shi yayin wasan tashe.

Dokin Kara: (A cikin wasar Dokin Kara) Wasa ne na yara maza, inda suke amfani da kararen dawa masu ƙarfi a matsayin dawaki.

Dundu: Dunƙule hannu tare da dukan mutum da hannun a bayansa.

Dundunge: (A cikin wasar Dundunge) 1: Wasan yara maza da mata inda ake rufewa ɗan wasa ɗaya ido da tsumma a kuma ba shi bulala. Duk wanda ya samu zai doka da wannan bulala. 2: Sunan wanda ake rufe wa ido cikin wasan.

Dunguren Kule: (A cikin wasar Dunguren Kule) Yawar yara maza da mata masu ƙarancin shekaru, inda suke kafa kai a ƙasa sannan su wuntsila.

Ɗage: (A cikin wasar Bena) Ɗauke ƙafa guda daga ƙasa.

Ɗagogwarogo: (A cikin wasar Ruwa Mai Malale) Amshin da ake maimaitawa yayin rera waƙar wasan.

Ɗakin Tsuntsu: (A cikin wasar Ɗakin Tsuntsu) Wasan yara maza da mata inda suke gina gidan ƙasa. Yara masu ƙarancin shekaru ne ke wannan wasa.

Ɗan Balum-balum: (A cikin wasar Ɗan Balum-balum) Wasan yara mata wadda suke layi, mai gudanar da wasa kuwa ta fito ta fuskance su. Za su riƙa waƙa tare da buɗe ƙasa da kuma tsukewa.

Ɗan Kurege: (A cikin wasar Ɗan Kurege) Wasan yara maza da mata da ke kama da wasan Na Ɗiba.

Ɗan Lele: (A cikin wasar ƊanLele) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke ɗauke da tsarin gidan aure. Yana nuna hoton yadda mata ke rarrashin miji da abinci iri-iri yayin da ran mijin ke ɓace.

Ɗan Maliyo-Maliyo: (A cikin wasar Ɗan Maliyo-Maliyo) Wasan gaɗa na yara mata da suke gudanarwa a dandali, wanda ke ɗauke da waƙa.

Ɗan Mutumin-Mutumin: (A cikin wasar Ɗan Mutumin-Mutumin) Tashen yara mata inda ake naɗa wa ɗaya daga cikin masu wasa tabarma a sanya hijabi a kai. Wannan yarinya za ta riƙa rawa yayin da aka je wurin wasa.

Ɗan Sanda: (A cikin wasar ‘yar Sarki 1) Wanda ke zartar da hukuncin da sarki ya yanke wa ɓarawo yayin da ya yi sata.

ƊanTsoho Mai Cin Bashi: (A cikin wasar ƊanTsoho Mai Cin Bashi) Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga cikinsu ke shigar tsofi sannan a goya masa matashin kai a baya. Za a riƙa dukan matashin kan tare da tuhumarsa kan ya biya kuɗin bashin da ake bin sa. Shi kuwa zai riƙa ihun neman taimakon a ba shi ya biya wannan bashi.

ƊanTsoho: (A cikin wasar ƊanTsoho Mai Cin Bashi) Sunan wanda ya yi shigar tsofi kuma aka goya masa matashin kai yayin wasan.

ƊanƁera: (A cikin wasar ƊanƁera) 1: Wasan tashe na yara maza inda suke ɗaura wa ɗaya daga cikinsu igiya a ƙugu sannan a shafe masa fuska da bula ko baƙin bayan tukunya. Yayin tashe, zai riƙa ƙoƙarin shiga wani lungu ko matsi, sauran masu wasa za su riƙa jawo shi da igiyar da aka ɗaura masa. Wasan yana ɗauke da waƙa. 2: Sunan wanda aka ɗaura wa igiya a ƙugu yayin wasan.

Ɗana: (A cikin wasar Langa) Kama ƙafa da hannu domin yin lako. Misali: Ya ~ lako.

Ɗanduƙunini: (A cikin wasar Ɗanduƙunini) 1: Wasa ne na tashe da yara maza ke gudanarwa, inda suke ɗaura wa ɗaya daga cikin su igiya a ƙugu sannan su shafe masa fuskar da baƙin tukunya ko bula. Yayin gudanar da tashen, yaron zai riƙa hanƙoron ɗaukar wani abu, amma sai a riƙa amfani da igiyar da aka ɗaura masa ana jawo shi baya. Wasan na tafiya da waƙa. 2: Sunan wanda ake ɗaura wa igiya yayin wasan.

Ɗanduƙununu: (A cikin wasar Ɗanduƙunini) Daidai da Ɗanduƙunini.

Ɗangalafe: (A cikin wasar Dokin Kara) Laƙewa ko maƙalewa a jikin doki lokacin da aka yi taɓarya.

Ɗani: (A cikin wasar Bindiga) Loja na ƙarfen garere da ake yi yadda da zarar an matsa bindiga za ta tashi.

Ɗauka: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Ɗaukar ɗa ko ‘ya’ya kafin mayar da saura rami yayin da dokar wasa ‘yar ɗaukelce.

Ɗaurawa: Lanƙwasa yatsar hannu tamkar ƙugiya tare da laƙawa a jikin na abokin wasa, sannan a ja da niyyar an yi wata yarjejeniya.

Ɗayalwa: (A cikin wasar ‘yar Ramel)

Ɗayalwa: (A cikin wasar ‘yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke ɗa ɗaya kacal kafin mayar da saura rami.

Ɗille: (A cikin wasar ‘Yar Ɗille) Yin amfani da yatsa domin feta ‘yar wasa zuwa cikin rami.

Ɗura-Ɗura: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ake cilla ‘ya’yan wasa sama ana cafewa cikin salo da ƙa’ida, tare da lissafa yawan cafewa da aka yi cikin waƙa.

Ɗuri: (A cikin wasar Bindiga) Sanya garin ashana a cikin bindiga domin bugawa.

Ɗurawa: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Ƙirgen da mai wasa ke yi da ke nuna tana saman abokiyar wasanta. Don haka abokiyar wasan sai ta fanshe adadin ɗura mata da aka yi ta hanyar lissafa adadin ba tare da faɗuwa ba.

Ɗuwawu: (A cikin wasar Ɓakutu Mai Babban Ɗuwawu) Tsummokara ko matashin kai da ake sanya wa ɓakutu sannan a ɗaure ɗamar a matsayin ɗuwawu.

Efa-Efa: (A cikin wasar Efa-Efa) Wasan yara maza da mata da ke da zubi da tsari irin na wasanWaranWarash. Sai dai a wasan ta efa-efa akan ɗauki lambobi ne.

Eskus: (A cikin wasar Sabis) Kalmar da mutum ke furtawa yayin da zai buga sabis alhali tana gidan abokan karawa. Furta wannan kalma zai sa abin da ya yi bai zama sata ba.

Fadar Sarki: (A cikin wasar ’yar Ganel) Wurin da sarki yake zaune.

Fafatawa: (A cikin wasar langa) daidai da gwabzawa.

Fanka: (A cikin wasar Fanka) 1: Wasan yara maza ne inda suke riƙe hannayen juna, su kuma haɗa ƙafafu wuri guda. Daga nan za su riƙa juyawa ta gefe guda (A cikin wasar hagu ko dama) tamkar dai yadda fanka ke juyawa a sama. 1: Jujjuyawa da ake yi yayin wasar fanka.

Fanshewa: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Lissafin da ke nuna ana biyan bashin ɗurawar da abokiyar wasa ta yi.

Farfela: (A cikin wasar Jirgi 2) Suna ne da ake kiran wanda yake kasancewa a gaba yayin wasan.

Farin Zoben Azurfa: (A cikin wasar Farin Zoben Azurfa) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa mai nuna taimakekeniya da ke wakana tsakanin abokai da kuma samari da ‘yan mata.

Fasa Ciki: (A cikin wasar Guro) Yin tafiya da ciki. Misali: A bisa tilas Musa ya ~ saboda bukka ya ke da shi.

Fasa Guro: (A cikin wasar Guro) Yayin da aka yi tafiya da guro, to an fasa guro.

Fasa Mana Guro Mu Sha Lagwada: (A cikin wasar Guro) Furucin da ake faɗa wa abokin wasa musamman domin tsolaya idan ta kasance ba shi da gidan da zai iya tafiya da shi sai guro; wanda kuma idan ya fasa guron dole ne abokin wasansa ya haihu.

Fawa: (A cikin wasar Girjim) Damar da sarki ke da ita na yin doguwar tafiya ko cin ɗa daga nesa ko kasancewar ɗa ba zai iya cin sa ba ko da suna kusa.

Faɗan Layi: (A cikin wasar sabis) Ajiye sabis bisa layi tare da zaɓen mutum ɗaya daga kowane gida. Waɗanda aka zaɓa za su zo jikin layi su sunkuya, kowa daga cikin gidansa. Za a yi ƙirga daga ɗaya zuwa uku. Yayin da ake ƙirgan waɗanda aka zaɓa za su riƙa buga sandarsu ƙasa sannan suna buga sandunan a jikin na juna. Da zarar an karuku, za a rige-rigen buga sabis zuwa gidan abokan karawa.

Faɗi Mana: (A cikin wasar Faɗi Mana) Wasan yara mata na dandali da ke da zubi da tsari irin na wasan Kwalba-Kwalba Dire. A ciki mai direwa takan bayyana sunan masoyinta.

Faɗi: (A cikin wasar ’Yar Ramel/Carafke) Karya dokar wasa wanda zai sa yi ya ƙare. Wato dai, wata da ke layi ta karɓi yi.

Faɗi: (A cikin wasar Belbela-Belbela) Yayin da ɗan wasa ya yi motsi alhali an kamala rera waƙar wasa, to ya faɗi.

Faɗi: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Yayin da mai wasa ta kasa cafe ’yar wasa ko kuma ta cafe ba da hannun da ya dace ba, to ta faɗi.

Faɗuwa: (A cikin wasar ’Yar Ramel) Daidai da faɗi.

Faɗuwa: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Duba faɗi (A cikin wasar Ɗura-Ɗura)

Fes: Wanda zai fara wasa kafin saura.

Feshi: (A cikin wasar Bindiga) Yanayi ne da ɗuri kan fito daga cikin bindiga ya samu hannun mai bugawa.

Filin Daga: (A cikin wasar langa) Iyakar farfajiyar da aka ƙayyade wadda dole ’yan langa ba za su fita daga ciki ba yayin fafatawa.

Fita Waje: (A cikin wasar Afurka-Afurka) Fita daga cikin da’irar da ake wasa sakamakon ɓata tsarin wasa da ‘yar wasa ta yi.

Fita: (A cikin wasar ’Yar Ramel) Kammala yi cikin nasara.

Fita: (A cikin wasar A Fim-Fim-Fim) Barin wasa tare da komawa gefe sakamakon ɓata tsarin wasa.

Fita: (A cikin wasar Babunna) Wadda ta gama dukan randuna to ta fita. Haka ma wadda ta kammalawan to fa yif  ta fita.

Fita: (A cikin wasar Cincin Sakatum) Duk wadda waƙar wasa ta ƙare a kansa, to zai fita.

Fita: (A cikin wasar Gori/Koɗi) Daina yin wasa.

Fita: (A cikin wasar Son Makaru) Komawa gefe wanda ɗaya daga cikin’yanwasa ke yi yayin da ta tafasa uku ba tare da ɓata ba, da wadda ke gefenta na dama.

Ga Kuɗin Toshinki Na Bara: (A cikin wasar Ga Kuɗin Toshinki Na Bara) Ɗaya daga cikin wasannin tashe na mata inda suke kira zuwa ga yawaita ibada cikin watan azumi.

Ga Mairama Ga Daudu: (A cikin wasar Ga Mairama Ga Daudu) Wasan tashe na yara mata inda ɗaya ke shigar maza a matsayin Daudu. Wata daban kuma za ta kasance a matsayin matarsa, wadda kuma ke faman ba shi abinci.

Ga Zabo Zai Mutu: (A cikin wasar Ga Zabo Zai Mutu) Nau’in wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga cikin yara kan sa babbar rigar da ta fi ƙarfinsa. A wurin tashe wannan yaro zai kwanta ƙasa ya mai da kai da ƙafafu da hannuwa cikin rigar sannan ya riƙa shure-shure a matsayin zabo da zai mutu. Wasa ne mai tafiya da waƙa.

Gabana Gaba Nawa: (A cikin wasar Gabana Gaba Nawa) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ake gudanarwa a zaune, wanda ke tafiya da waƙa da tafi.

Gadan Jaɓa: (A cikin wasar Taɓarya) Ɗaya daga cikin abubuwan da yara ke samarwa yayin wasan.

Gagarel: (A cikin wasar ‘yar Ramel) 1: Tsayawar da ɗa ke yi ya ƙi shiga rami yayin da mai wasa ta yi ƙoƙarin tura shi yayin masar babane. 2: Dama da ake ba wa mai wasa ta sake gwadawa yayin da ta faɗi a gewaya ɗan wake. Akan ba da gagarel ɗaya ko biyu ko sama da haka.

Gamuna: (A cikin wasar Gamuna) Wasan yara mata na dandali da ke tafiya da waƙa. Akan gudanar da ita tsakanin ɓangarori biyu na yara.

Gardama: (A cikin wasar langa) rashin yarjejeniyar tsakanin ’yan wasa kan wani abu da ya faru yayin wasa. Wato kamar ruwa ta sha ko ba ta sha ba, ko lakon ɗan wasa ya taɓa ƙasa ko bai taɓa ba da makamantan su. misali: ’yan gidan ruwa ne suka ta da ~.

Gare: Daidai da garere

Gare-Gare: Daidai da garere.

Garere: (A cikin wasar Garere) Wasan yara maza da ke da zubi da tsari irin na wasan taya. Sai dai a wasan garere, akan yi amfani ne da garere musamman na keke a maimakon tayar mashin.

Gari: (A cikin wasar girjim) Jimillan’ya’yan mai wasa (A cikin wasar 12 ko sauran da suka rage idan an cinye wasu daga ciki) su ne ’yan garinsa.

Gari: (A cikin wasar Jallu Wa Jallu) Ɗaya daga cikin ɓangarori biyu na masu wasa.

Gari: (A cikin wasar sabis) 1: (A cikin wasar suna) ɗaya daga cikin rukunen yara da ke buga sabis tsakaninsu. Misali: Musa yana ~nmu. 2: (A cikin wasar suna) bagiren da yake ɓantaga ’yan gari ɗaya, wato daga inda layi ya fara zuwa bayansu. Misali: Musa ya yi sata a garinmu.

Gariye: (A cikin wasar Gariye) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke ɗauke da waƙa. Mai waƙa takan bayyana sunan ɗaya daga cikin manyan ƙawayenta.

Gewaya Ɗanwake: (A cikin wasar gori/koɗi) salon wasan gori wanda ɗan wasa ke shan abokan wasa ɗaya bayan ɗaya da zaran ya kife. Wato da zaran ya kife sai ya sha ɗaya daga cikinsu, idan ya sake kifewa kuma ya sha wani.

Gida: (A cikin wasar girjim) Kowane ɗaya daga cikin gidajen dara talatin da shida (A cikin wasar 36) da aka zana domin wasan girjim.

Gida: (A cikin wasar girjim) Zane da ake yi ko tonon gurabu talatin da shida (A cikin wasar 36), shida a tsaye, shida kuma a kwance domin zuba ’ya’yan girjim.

Gida: (A cikin wasar Guro) Kowane daga cikin ramukan da aka tona domin guro yana matsayin gida. Misali: Su Musa suna wasan guro mai ~ goma.

Gida: (A cikin wasar Jallu Wa Jallu) Daidai da gari.

Gida: (A cikin wasar Langa) kowanne daga cikin rukunnen masu wasan langa da za su fafata da juna.

Gidaje: (A cikin wasar Bena) Zanen da ake yi a ƙasa na manyan gidajen dara, waɗanda cikinsu ake tsalle da ƙafa ɗaya yayin wasa.

Gidan Kurciya: (A cikin wasar Gidan Kurciya) 1: Wasan yara maza da mata da ake da’ira a bar tazara tsakanin juna tare da riƙe hannayen juna. Masu wasa za su riƙa shiga ta ƙasan hannayen cikin bin doka da ƙa’idar wasa. 2: Sunan tazara da ake samu tsakanin ɗan wasa da ke tsaye da kuma na gefensa.

Girgiza: (A cikin wasar Carafke) Rawa ko matsawar da ɗa ko ’ya’ya suke yi yayin da mai wasa ke faman cafkel.

Girjim: (A cikin wasar girjim) 1: Wasa dangin dara da ake zana gidajen dara talatin da shida (A cikin wasar 36) cikin layuka shida a tsaye, shida kuma a kwance. Akan yi amfani da ƙwadagon goruba da na taura ko duwatsu ko makamantansu a matsayin ’ya’ya. 2: Furucin da mai wasar girmin kan yi yayin da zai yi tafiya, musamman domin zolayar abokin karawarsa cewa zai cinye shi.

Gociya: (A cikin wasar Lakkuma-Lakkuma Lale) Zamewa da wanda ake ci zai yi yayin da aka kawo duka da niyyar ci.

Gociya: (A cikin wasar Waran Warash) Duba gociya (A cikin wasar Lakkuma-Lakkuma Lale).

Goga: (A cikin wasar goga) 1: (A cikin wasar suna) wasan da ake rami a jikin gaɓar kara domin a samu dammar lanƙayawa a jikin gaɓar karan abokin wasa, sannan a ja har sai kan gaɓar karar ɗaya daga cikin’yan wasa ya ɓalle. 2: (A cikin wasar suna) Gaɓar karan da aka yi ta wasan goga da ita ba ta karye ba. Misali: Wa zai ja da ~ ta?

Gomalwa: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta mayar ɗa ’ya’ya cikin rami ɗaya bayan ɗaya. Shi ne matakin ƙarshe na kowace randa.

Gomanna: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na biyu a wasan babunna.

Gora-Gora: (A cikin wasar Gora-Gora) Wasan gaɗa ne na mata da ake gudanarwa a dandali, wanda kuma ke ɗauke da waƙa.

Gori: (A cikin wasar Godi/koɗi) 1: (A cikin wasar suna) suna da ake kiran wasan gori da shi. Daidai da koɗi. 2: (A cikin wasar suna) ƙoƙon dodon koɗi da aka gyara, ko marfin biro da aka sanya wa fayafayen babban batirin rediyo domin yin gori da shi. 3: (A cikin wasar aikatau) jujjuyawa ko wainuwa da gori ke yi yayin da aka gara ta.

Goron: (A cikin wasar WaranWarash) Ɗaya daga cikin sunayen da masu wasa ke zaɓa.

Goruba: (A cikin wasar Waran Warash) Ɗaya daga cikin sunayen da masu wasa ke zaɓa.

Goɗiyallare: (A cikin wasar Goɗiyallare) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke ɗauke da waƙar da ta ƙunshi baƙar magana ga uwar miji.

Goye-Goye: (A cikin wasar Goye-Goye) Wasan yara mata ne inda ɗaya daga cikin masu wasa za ta goyi ‘yaruwarta ta yi tafiya da ita zuwa wani ƙayyadadden wuri. Yayin da ta gama, ita ma za ta rama mata. Wato za ta goye ta yi daidai wannan tafiya da ita.

Goyo: (A cikin wasar Maimuna Ta Yi Ciki Ga Goyo) ’Yar tsana da Maimuna ke goya yayin wasa.

Goyon Baya: (A cikin wasar Goyon Baya) Wani nau’i ne na wasan goye-goye inda mai goyo da wanda aka goya ke haɗa bayansu.

Goyon Kura: (A cikin wasar Goyon Kura) Wani nau’i ne na wasan goye-goyen inda wanda aka goya ke kasancewa a ranga-ranga kan bayan mai goyo.

Gula: (A cikin wasar Langa) Yayin da ɗan wasa ya harbi abokin karawarsa da dunduniyar ƙafar da ya yi lako da ita, to ya masa ƙulli. Wannan laifi ne a dokar langa.

Gulum-Babu: (A cikin wasar Noti-Noti) Furucin da ake yi wanda ke nuna cewa, abin da aka ambata ba ya ɗauke da noti.

Gulum-Noti: (A cikin wasar Noti-Noti) Furucin da ake yi wadda ke nuna cewa, abin da aka ambata yana ɗauke da noti.

Guro: (A cikin wasar Guro) 1: (A cikin wasar suna) wasa dangin dara da ake amfani da duwatsu ko ‘ya’yan kanya ko makamantansu. Akan toni ramuka goma sha biyu sannan a sanya uku-uku a kowanne rami. Wani lokaci akan kira ta da ‘yar guro. 2: (A cikin wasar suna) ‘ya’ya uku na ƙarshe da ake ba wa wanda ya yi tafiya bayan an kamala tafiya. Misali: Musa ne ya yi tafiya yanzu, saboda haka  shi za a ba wa ~. 3: Gidan da aka yi ta tafiya ba tare da an kwashe shi ba. Saboda haka ‘ya’yan gidan sun yi yawa sosai.

Gwabzawa: (A cikin wasar langa) fafatawar da ake yi yayin da ruwa ta bayar har zuwa ruwa ta sha ko a kashe ta ko a yi jaga ko zubel. Misali: Ruwa ta tsinke ta sha a yayin da ake ta ~.

Gwanjo-Gwanjo: (A cikin wasar Gwanjo-Gwanjo) Wasan yara maza da suke haɗa rigunansu wuri guda sannan su jefa sama. Za a yi wawan cafewa tun suna sama. Duk wanda ya cafe rigarsa, zai nannaɗa ta daɗin duka. Za a rufe na ƙarshe da bai ɗauki irgarsa ba da duka har saiya je ya sha.

Gwauro: (A cikin wasar Gwauro) 1: Wasan tashe na manya maza inda sarkin gwauro ke kama gwagware. 2: Sunayen waɗanda sarkin gwauro ke kamawa sakamakon ba su da aure.

Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba: (A cikin wasar Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ake rabuwa gida biyu kafin fara ta. Yana tafiya da tsarin shugabanci. Akan rufe wa ɗaya daga cikin masu wasa ido, sannan wata daga ɓangaren abokan karawa ta zo ta bugi kanta ta koma ta zauna cikin sauran‘yanuwanta. Yayin da aka buɗe mata ido, za a tambayi ta nuna wadda ta zo ta buge ta.

Hagu Take Yi: (A cikin wasar Guro) Furuci da ke nuna cewa, ta hagu ake yin tafiya ba ta dama ba.

Haihuwa: (A cikin wasar Guro) yayin da ‘ya’yan gida suka kasance uku baya ga an riga an fara tafiya, to an haihu a wannan gida.

Hajijiya: (A cikin wasar Hajijiya) Wasan yara maza da mata, inda mai wasa zai riƙa dawurwuri wuri guda har sai jiri ya ɗebe shi.

Hajiyar Ƙauye: (A cikin wasar Hajiyar Ƙauye) 1: Wasan yara mata ta tashe inda ɗaya daga ciki ke shigar ‘yan ƙauye. Wasan na ɗauke da waƙar da ke nuna wannan yarinya hajiyar ƙauye ce wadda ta yi kwalliya ranar salla. 2: Sunan wadda ke yin kwalliyar ‘yan ƙauye yayin wannan wasa.

Hamsana: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na shida a wasan babunna.

Hankaɗa: (A cikin wasar langa) daidai da bangaza.

Harbi: (A cikin wasar Robali) Yin amfani da yatsa manuniya da kuma babbar yatsa wajen naɗe robali da ɗame shi yadda idan aka janye babban yatsa, robali ɗin zai tafi da ƙarfi zuwa wurin da ake buƙatar ya je.

Huce: (A cikin wasar girjim) Yayin da mai girjim ya dace ya ɗauki sizin, sai kuma bai ɗauka ba ya yi tafiya, to sizin ɗin ta huce ke nan, don haka ba zai ɗauka ba.

Hure: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Furucin da mai yi ke ko sauran‘yan wasa suke furtawa yayin da ɗa ko ‘ya’ya ba su shiga rami ba bayan an ture su zuwa cikin ramin.

Huɗulwa: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke ‘ya’ya huɗu kafin mayar da saura rami.

Ina Da ‘yata: (A cikin wasar Ina Da ‘yata) Wasan ‘yan mata na dandali da ke ɗauke da waƙar da ta ƙunshi tsokaci kan halayen masu wasu sana’o’i, musamman ta fuskar zamantakewar aure.

Ina Da Cikin Ɗan Fari: (A cikin wasar Ina Da Cikin Ɗan Fari) Ɗaya daga cikin wasannin dandali na yara mata mai tafiya da waƙa da tafi.

Inna: (A cikin wasar Ba Mu Kuɗinmu) Duk wata mace da aka iske a gidan da aka shiga tashe.

Innaleliya: (A cikin wasar Innaleliya) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa mai nuna halayen matan aure ga danginsu da dangin miji da kuma kishiya da danginta.

Innan Bakkwato: (A cikin wasar Carafke) Wanda aka tashi wasa ba ta gama biyan bashin da ke kanta ba.

Ishina: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na uku a wasan babunna.

Iya: (A cikin wasar To Iya) Sunan wadda take fitowa a matsayin uwa yayin wasan.

Iyaka: (A cikin wasar ‘yar Cille) Layin da ake zanawa gaban da’ira wanda dole cilli ya wuce layin. Yayin da aka yi cillin da bai wuce layin ba, mai wasa ya faɗi.

Iye Nanaye: (A cikin wasar Iye Nanaye) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke tafiya da waƙa mai nuna cewa samarinsu na biya musu kuɗaɗen wasu abubuwan buƙata.

Ja: (A cikin wasar Guro) Samun nasarar ƙarin gida ko gidaje bayan an yi tafiya.

Ja: (A cikin wasar Wur-Wur) Jan zaren wur-wur daga gefen dama da hagu da kuma tsuke tsaren yayin da ake wasa.

Jaga: (A cikin wasar Langa) Gidan ruwa sun yi jaga yayin da suka kasha dukkanin abokan karawar su, wanda a wannan yanayi ba sai ruwa ta sha ba. Yayin da aka yi jaga, to ‘yan garin ruwa suna da maki biyu a maimakon maki ɗaya.

JalluWaJallu: (A cikin wasar Jallu Wa Jallu) Ɗaya daga cikin wasannin dandali da ke tafiya da waƙa. Akan rabu zuwa gari biyu yayin gudanar da wasan.

Jambaɗa: (A cikin wasar sabis) yin amfani da sandar sabis domin a doki ƙwallon sabis da nufin aika ta zuwa gidan abokan karawa.

Jamilun: (A cikin wasar WaranWarash) Ɗaya daga cikin sunayen da masu wasa ke zaɓa.

Janye: (A cikin wasar Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba) Yayin da aka yi ta jawo ‘yan ɓangare guda, har suka ƙare, to an janye su.

Jar Miya: (A cikin wasar Jar Miya) Ɗaya daga cikin wasannin mata na dandali da ke ɗauke da waƙa mai nuna hoton ɗabi’un wasu matan aure zuwa ga‘yanuwansu da ‘yanuwan miji da kuma na kishiya tare da ‘yanuwanta.

Jatau Mai Magani: (A cikin wasar Jatau Mai Magani) Wasan tashe na manya maza inda ɗaya daga ciki ke shigar bokaye ya kuma ɗauki kayan sassaƙe-sassaƙe da ganyaye, a matsayin mai ba da magani.

Ja-tau: (A cikin wasar Gori/koɗi) fitowar jini daga bayan hannun wanda aka sha shi da gori. Misali: Ya fitar masa ~.

Jatau: (A cikin wasar Jatau Mai Magani) Sunan wanda ke shigar boka tare da ɗaukar kayan magani na wasa a lokacin tashen.

Jawowa: (A cikin wasar Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba) Yayin da wadda aka rufe wa ido ta nuna wadda ta buge ta (A cikin wasar bayan an buɗe idanun), to ta jawo ta. Saboda haka wadda aka nuna za ta dawo garin wadda ta nuna ta.

Jifa: (A cikin wasar Bena) Wurga ‘yar jifa zuwa wani gida da ake buƙata yayin wasa.

Jifa: (A cikin wasar Robali) Ɗora robali bisa tafin hannu tare da wurga shi yayin da ake wasan robali ‘yar jifa ko ‘yar kanti.

Jiki: (A cikin wasar langa) Yin amfani da gefen kafaɗa domin ture ɗan wasa da niyyar kashe shi. Misali: Musa yayi wa Idi ~ sai da ya faɗi.

Jini Da Jini: (A cikin wasar Jini Da Jini) Wasa ne na yara maza na tsaye. Shugaban wasa na ambaton sunayen halittu masu jini da marasa jini, sauran masu wasa na amsawa danja ko babu daidai da kasancewar abin da aka ambata mai jini ko marar jini.

Jira: (A cikin wasar girjim) Duba jira (A cikin wasar Guro).

Jira: (A cikin wasar Guro) Wanda yake jira a guro, yana ɓata lokaci kafin ya yi tafiya. Ma’ana idan tafiyarsa ta zo, sai ya yi jinkiri kafin ya fara.

Jirel: (A cikin wasar Babunna) Dakatawa kaɗan yayin kaɗi har sai mai wasa ta ga abokiyar kaɗinta ta buɗe ko ta rufe sannan ita ma ta yi, domin ta ƙwace ko kuma ta kauce wa ƙwacewar abokiyar wasa.

Jirgi 1: (A cikin wasar Jirgi 1) Leda da ake ƙullawa jikin tsinkaye masu kauri, a kuma ɗaura dogon zare sannan a jefa sama a matsayin jirgi. Iska za ta riƙa kaɗa ta har ta je sama sosai, yayin da yaro kuma ke riƙe da dogon zaren.

Jirgi 2: (A cikin wasar Jirgi 2) Wasan yara maza na dandali inda yaro guda kan tsaya wani ya hau bisa kafaɗunsa ya zauna. Wani daban kuma zai kasance ta gaba, ƙafafunsa harɗe da cikin wanda ke tsaye, sannan wanda ke zaune bisa kafaɗun na farko zai tallafe shi da ƙafafu ta hanyar sanya ƙafafunsa ta hamatar na gaban.

Ka Yi Rawa: (A cikin wasar Ka Yi Rawa) Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga ciki ke shigar malamai. Yara sukan sa shi a gaba da cewa ya yi rawa, shi kuwa zai haƙiƙance kan cewa bai yi ba. Daga ƙarshe dai yakan ce zai taɓa kaɗan, sai kuma ya ɓuge da rawar.

Kallo Da Ido: (A cikin wasar Kallo Da Ido) Ɗaya daga cikin wasannin tashe na yara mata inda yarinya guda take fitowa a matsayin mai ba da magani.

Kama: (A cikin wasar ‘yar Cille) Yayin da mai kamu ya cafke ‘yar cille kafin ta taɓa ƙasa, to ya kama.

Kamu: (A cikin wasar Cincin Sakatum) Kura ke yin kamu. ‘yan wasa za su gudu, duk wadda kura ta kama to zai yanka. Idan aka yanka ɗan wasa, shi ma ya zama kura. Saboda haka masu kamu za su zama biyu.

Kamu: (A cikin wasar Digi-gidi) Bin waɗanda suka fita da mai kamu take yi da niyar ta shafa kan ɗaya daga cikinsu.

Kanda: (A cikin wasar Guro) Yayin da mai tafiya ya ajiye ɗan a ƙarshe a hannunsa a wani gida wanda kuma babu wani ɗa da zai haɗa da shi domin ci gaba da tafiya, to ya yi kanda.

Kande Mahaukaciya: (A cikin wasar Kande Mahaukaciya) Wasan yara mata da ke faɗakarwa zuwa ga tsafta.

Kande: (A cikin wasar Kande Mahaukaciya) Sunan wadda ke fitowa a matsayin ƙaramar yarinya lokacin wasan.

Kanti: (A cikin wasar Robali) Suna da ake kiran robalin da mai kanti ya tara.

Karan Tsallake: (A cikin wasar Karan Tsallake) Wasan yara maza da ya danganci tsallake igiya ko kara ko wani abu mai kama da wannan. Yara sukan taho da gudu sannan su riƙa tsallakewa.

Karya Gaɗiɗi: (A cikin wasar Karya Gaɗiɗi) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata mai tsarin cilli da direwa.

Kash: (A cikin wasar WaranWarash) Ɗaya daga cikin sunayen da masu wasa ke zaɓa.

Kashe Ruwa: (A cikin wasar Langa) An kashe ruwa ne yayin da aka tsinka lakonta ko lakonta ya taɓa ƙasa. Kowa ya sake lakonsa domin an ~.

Kasoko-Kasko: (A cikin wasar Kasko-Kasko) Wasan yara maza da mata da ke da zubi da tsari irin na wasan Lakkuma-Lakkuma Lale.Waƙoƙin wasannin biyu sun bambanta.

Kasuwar Ƙudaje: (A cikin wasar Taɓarya) Ɗaya daga cikin abubuwan da yara ke samarwa yayin wasa.

Kaɗa: (A cikin wasar Kaɗa) Ɗaya daga cikin wasannin dandali na yara mata da ke ɗauke da waƙa mai nuna muradin zuciyarsu tare da addu’a.

Kaɗawa: (A cikin wasar gori/koɗi) gara gori da ɗan wasa ke yi domin ta yi ta juyawa.

Kaɗi: (A cikin wasar Babunna) ‘yan tsalle-tsalle da tafi da ake yi kafin a ware ƙafa ko a tsuke.

Kaɗi: (A cikin wasar Babunna) Tsalle-talle da waƙa da tafi da ake yi har zuwa lokacin da aka buɗe ko aka tsuke ƙafafu. Kaɗi uku ake buƙata kafin a ƙwace mai yi ko mai yi ta ci nasara.

Kaɗi: (A cikin wasar Odada) Duba kaɗi (A cikin wasar Babunna)

Ke Kika Je Ki Gidan Su Direba: (A cikin wasar Ke Kika Je Ki Gidan Su Direba) Tashen yara mata da ke faɗakarwa game da yadda kwaɗayi kan jefa mata zuwa ga halaka.

Kibiya :(A cikin wasar langa) kalmar da ke nuna ɗan wasa maguji ne wanda ba ya kamuwa da garaje. Misali: Musa ~ ne.

Kifewa: (A cikin wasar gori/koɗi) kifar da gori da ɗan wasan gori ke yi da ke nuna ya ci wasa.

Kifi-Kifi: (A cikin wasar Kifi-Kifi) Wasar yara mata ce ta dandali mai zubi da tsari irin na wasan Kwalba-Kwalba Dire. Sai dai a wasan kifi-kifi, akan samu rukuni biyu ne na masu cilli da kuma masu direwa guda biyu.

Kin Zama: (A cikin wasar Kin Zama) Waƙar da yara mata musamman abokan amarya suke gudanarwa a gidan biki ko yayin da za a raka amarya ɗakinta.

Kira: Kiran ‘yan wasa ɗaya bayan ɗaya da shugabannin gida suke yi domin a raba dukkanin‘yan wasa zuwa gida-gida. Misali: Mutane uku ne masu ~ saboda haka za a samu gidaje uku.

Kis-Kis-Kis An Kas-Kas-Kas: (A cikin wasar Kis-Kis-Kis An Kas-Kas-Kas) Wasan yara mata ne mai kama da bena. Sai dai shi yara biyu ne suke tafiya a tare.

Kofi: (A cikin wasar Kofi) 1: Wasan yara maza inda suke yin zanen layi guda a wuri mai danshi. Zanen na kasancewa yana da ɗan gurbi. Za a rufe wa mai tafiya idanuwa. Shi kuwa zai ɗora yatsa bisa farkon layin ya fara bin sa a hankali har zuwa ƙarshe. Yayin da ya kuskure, ya fita a layi, to ya faɗi. 2: Furucin da mai tafiya ke yi da ke matsayin tambayar ko yana tafiya daidai.

Konsef: (A cikin wasar Ƙwanƙwalati) Yayin da aka buga ƙwalluwa ta doki wani abu daban ya canza mata hanyar da da ta bi, to an yi konsef ke nan.

Kora: (A cikin wasar girjim) Yayin da aka cinye ‘ya’yan mai wasan girjim, to an kore shi.

Kora: (A cikin wasar Guro) Daidai da tatike.

Kulle: (A cikin wasar girjim) Yayin da mai wasa ya sanya ‘ya’yan wasa gaban ɗa ko ‘ya’yan abokin karawarsa, suka tare wannan ɗa ko ‘ya’ya yadda da zarar an yi tafiya da ɗaya daga cikinsu za a cinye shi, to an kulle masa ‘ya’ya ke nan.

Kumbukululu: (A cikin wasar Kumbukululu) 1: Wasan yara maza da mata inda ake rufewa ɗaya daga cikin masu wasa idanu da tsumma ko kallabi. Sauran yara kuma za su gudu. Duk wanda kunbukululu ta yanka, to shi zai zama kumbukululu. 2: Sunan wanda ake rufe wa ido yayin wasan.

Kura: (A cikin wasar Cincin Sakatum) Wanda kowa ya fita a wasa ya bar shi.

Kura: (A cikin wasar Ni Kura-Kura) Wadda ke fiskantar uwa yayin wasa. Hanƙoron tashi ne ta kama ɗaya daga cikin‘yan wasa.

Kura: (A cikin wasar Odi-Odi) Wanda ke bin ‘yan wasa domin yankawa. Duk wadda aka yanka, shi zai zama kura.

Kusa: Ɓera

Kwabo A Bayan Banki: (A cikin wasar Taɓarya) Ɗaya daga cikin abubuwan da yara ke samarwa yayin wasa.

Kwabo: (A cikin wasar Taɓarya) Ɗaya daga cikin abubuwan da yara ke haɗawa yayin wasa. Yana da siffar kwabo a tsakiya, wato zagaye.

Kwalba-Kwalba Dire: (A cikin wasar Kwalba-Kwalba Dire) Wasan yara mata na dandali wanda ke ɗauke da waƙa da kuma tsarin direwa da cilli.

Kwalliyar La’asar: (A cikin wasar Kwalliyar La’asar) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na gaɗa da ke ɗauke da waƙa mai nuna muhimmancin kwalliya.

Kwanciyar Karuwa: (A cikin wasar sabis) wani yanayi ne da ƙwallon sabis ke tsayawa cak ta daina motsi amma ba ta kwanta ƙasa ba. A maimakon haka, ta ɗan karkace ne kawai. A irin wannan yanayi, akan ba wa ‘yan gidan da ƙwallon sabis ta musu kwanciyar karuwa damar su ɗauko tasu a ajiye a ƙasa sannan su buga da sanda.

Kwanciyar Magirbi: (A cikin wasar sabis) daidai da kwanciyar karuwa.

Kyauro: (A cikin wasar Robali) Daidai da robali.

Kyauta: (A cikin wasar Guro) Yayin da wani mai wasan guro ya bayar da gida ko gidaje ga wani daban domin ya riƙa tafiya da su, to ya yi kyauta ke nan.

Ladan: (A cikin wasar Ɓelunge) Wanda ke tsaye a gaban mamu, bayan ladan; shi ke magana bayan liman ya yi.

Ladidin Baba: (A cikin wasar Ladidin Baba) Ɗaya daga cikin wasannin gaɗa na dandali da ke ɗauke da waƙa.

Lagwada: (A cikin wasar Guro) Haihuwa da ko samun ciki da mutum zai yi yayin da aka yi wata tafiya, musamman idan aka fasa guro.

Lakkuma-Lakkuma Lale: (A cikin wasar Lakkuma-Lakkuma Lale) Wasan yara maza da mata da ake gudanarwa a zaune inda yara kan zauna su miƙe ƙafafunsu. Sai kuma guda ɗaya ya riƙa waƙa tare da taɓa guiwowinsu. Duk guiwar da waƙar ta ƙare a kanta, za a cire wannan ƙafa.

Lako: (A cikin wasar langa) kama ƙafar da ɗan wasan langa ke yi da hannunsa, wanda idan hannun ya rabu da ƙafar, to ya mutu.

Langa: (A cikin wasar langa): wasan da ake riƙe ƙafa ɗaya da hannu ta baya sannan a riƙa tsalle da ƙafa ɗaya. A haka za a tunkari abokan karawa domin a gwabza. Duk wanda ya sake ƙafarsa ko kuma ya faɗi har lakonsa ya taɓa ƙasa, to ya mutu.

Lasko: (A cikin wasar Lasko) 1: Wasan yara maza da mata inda mai lasko yake dukan abokin wasansa sannan ya gudu. 2: Sunan dukan da ake yi yayin wasan.

Laula Amarya: (A cikin wasar Laula Amarya) Ɗaya daga cikin waƙoƙin da yara mata ke gudanarwa yayin Bukukuwan aure. Waƙar tana ɗauke da faɗakarwa kan cewa aure makaranta ce mai zaman kanta.

Layi: (A cikin wasar ‘yar Ramel/Carafke) Mai bi wa wadda ta faɗi da yi.

Layi: (A cikin wasar sabis) shata layi da ake yi tsakanin garuruwa biyu da ke wasan sabis.

Leleya: (A cikin wasar langa) irin dawurwura da zilliya da ruwa ke yi wa abokan karawarta domin kada a kashe ta. Misali: Ruwa tana ta ~ su.

Liman: (A cikin wasar Jini Da Jini) Wanda ke kasancewa a gaban sauran yara yayin wasa. Shi ke ambaton sunayen halittu, sauran yara kuma su riƙa fayyace mai jini ne ko marar jini.

Liman: (A cikin wasar Ɓelunge) Wanda ke tsayuwa gaban duk sauran masu wasa. Shi ke fara aikata aiki ko furta magana kafin ladan ko mamu.

Linzami: (A cikin wasar Dokin Kara) Igiyar da ake ɗaurawa a jikin doki wadda da ita ake riƙe shi.

Lokos: (A cikin wasar Lokos) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ake gudanarwa tsakanin yara uku. Biyu sukan yi wa ɗaya lilo. Yayin da suka ƙare mata, za ta sauka wata ma ta hau. Haka za a yi ta gawa.

Macukule: (A cikin wasar Macukule) Wasan tashe na manya maza inda ɗaya daga cikin masu wasa ke shiga irin ta Gwari, tare da magana irin ta Gwarawa yayin tashe.

Mai Ciki: (A cikin wasar Mai Ciki) 1: Wasan tashe ne na yara mata inda akan cusa wa ɗaya daga cikin su tsummokara a cikin riga domin ya yi tulu kamar mai ciki. Waƙar wasan na ɗauke da irin barkwancin ko tsokala da ake wa mai ciki. 2: Sunan wadda aka sanya mata tsummokara a cikin riga yayin wannan wasa.

Mai Cunkus: (A cikin wasar Carafke) Yanayin bajiin da ‘ya’ya suka mannu da juna ƙwarai.

Mai Dawa: (A cikin wasar Mai Dawa) 1: Wasan yara maza na dandali da ake amfani da batirin babban rediyo. Akan jefa batirin a bukaci yara su nemo. 2: Sunan shugaban wasa. Wanda ya nemo batirin da aka jefa, shi ke zama Mai Dawa.

Mai Direwa: Wadda ake cafe ta kuma a cilli a wasannin yara mata da ya shafi direwa.

Mai Kamu: (A cikin wasar Digi-digi) Wadda ta yi ta ƙarshe a fita a wasan digi-digi da za ta bi saura da gudu domin kamu.

Mai Kanti: (A cikin wasar Robali) Sunan wanda ke tararo balin duk da ba ta shiga cikin gidan dara tsulum ba ya yin da aka jefo ta, a wasan robali ‘yar taru.

Mai Kwaɗayi: (A cikin wasar Tasihi Mai Kwaɗayi) Wanda ke zaman dirshan yayin wasa, ya kuma haƙiƙance ba zai tashi ba sai an ba shi.

Mai Naƙiye: (A cikin wasar Mai Naƙiye) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa da ke hannunka-mai-sanda game da maza ɓata-gari.

Mai Ƙiriniya: (A cikin wasar Mai Ƙiriniya) 1: Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga cikin yara ke ayyukan ƙiriniya daban-daban yayin wasa. Wasan yana tafiya da waƙar da ta ƙunshi tambaya ga mai ƙiriniya kan wanda ya sa shi. Mai ƙiriniya kuwa zai riƙa ba da amsa. 2: Sunan wanda yake aikata ayyukan ƙiriniya yayin wasan.

Mai Tafiya: (A cikin wasar Kofi) Wanda aka rufe wa idanu domin ya yi tafiya.

Maimuna Ta Yi Ciki Ga Goyo: (A cikin wasar Maimuna Ta Yi Ciki Ga Goyo) Wasan tashe na ‘yan mata wanda suke kwaikwayon mace mai goyo da kuma ciki.

Maimuna: (A cikin wasar Maimuna Ta Yi Ciki Ga Goyo) Wadda take ɗauke da goyo da kuma ciki yayin wasa.

Mairama: (A cikin wasar Ga Mairama Ga Daudu) Matar Daudu a cikin wasan.

Malam Ka Ci Kusa: (A cikin wasar Malam Ka Ci Kusa) Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga ciki ke shigar dattawa, sauran yara kuma na tuhumarsa cewa ya ci ɓera.

Malam: (A cikin wasar Ka Yi Rawa) Suna ne na wanda ya yi shigar malamai a cikin wasan.

Mama Ta Ƙi Shillona: (A cikin wasar Mama Ta Ƙi Shillona) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke tafiya da waƙa da ke hannunka-mai-sanda ga iyaye kan lura da buƙatun‘ya’yansu, tare kuma da bayyana sunayen ƙawaye da ‘yanuwa.

Mamin Jatau: (A cikin wasar Mamin Jatau) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke tafiya da waƙa tare da tafi.

Mamu: (A cikin wasar Jini Da Jini) Yaran da ke gudanar da wasa, waɗanda ba liman ba.

Mamu: (A cikin wasar Ɓelunge) Dukkanin sauran yaran da ke wasa koma bayan liman ko ladan.

Masar Babanne: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Dokar wasa inda kafin mai wasa ta fita sai ta jera ‘ya’yan ramel a bakin rami sannan ta riƙa jefa ƙodo tana ture su ɗaya bayan ɗaya cikin rami. Yayin daɗa ɗaya ya yi rawa yayin da take tura wani, to ta faɗi.

Masu Bayarwa: (A cikin wasar A Cikin Wannan Rana) Duba masu bayarwa (A cikin wasar Gamuna).

Masu Cilli: (A cikin wasar ‘yar Cille) Ɓangaren ‘yan wasa da su za su yi cilli.

Masu Cilli: Waɗanda ke cafe mai direwa tare da tura ta gaba a wasannin mata da ya ƙunshi cilli da direwa.

Masu Kamu: (A cikin wasar ‘yar Cille) Ɓangaren ‘yan wasa da za a yi wa cilli, su kuma su yi ƙoƙarin kamawa.

Masu Ɗauka: (A cikin wasar A CikinWannan Rana) Duba masu ɗauka (A cikin wasar Gamuna).

Matar Na Karofi: (A cikin wasar Matar Na Karofi) 1: Wasan tashe na ‘yan mata wanda ake kwaikwayon gidan aure. 2: Sunan yarinyar da take fitowa a matsayin amarya a cikin wasan.

Motar Kara: (A cikin wasar Motar Kara) Wasan yara maza da suke ƙera motar wasa ta hanyar amfani da sillen karan dawa.

Motar Langa-Langa: (A cikin wasar Motar Langa-Langa) Wasan yara maza da suke ƙera motar wasa ta langa-langa.

Mummuna: (A cikin wasar sabis) Kalmar da ke nuna sabis da aka yi wa abokan wasa ba mai kyau ba ce, don haka ba za su saya ba. Misali: Ba mu saya ba, ~.

Mun Saya: (A cikin wasar sabis) furucin da abokan karawar gidan da ke ba da sabis ke yi da ke nuna cewa sun aminta da sabis da aka bayar.

Musu :(A cikin wasar  langa) Daidai da gardama.

Mutuwa: (A cikin wasar langa) tsinkewar lakon ɗan langa ko faɗuwar wa ƙasa.

Mutuwa: (A cikin wasar sabis) yayin da ƙwallon sabis ta kwanta ta dena motsi to ta mutu. A wannan yanayi, an yi nasara kan gidan da ƙwallon ta mutu a ciki. Misali: ~ ɗin ta mutu kafin Musa ya kai gare ta.

Mutuwar Kasko: (A cikin wasar langa) yayin da ‘yan wasa biyu da ke fafatawa tsakaninsu suka kasha juna a tare, to sun yi mutuwar kasko.

Na Ci Na Kasa Tashi: (A cikin wasar Na Ci Na Kasa Tashi) Wasan tashe ne na yara maza inda ake sanya wa Baba tsummokara a cikin riga. Rigar za ta yi tulu kamar mai ciki. Wasan na tafiya da waƙar da ke nuna Baba ya ci ne ya kasa tashi, sannan ana nusantar da shi cewa, ya cika zari ne da rashin haƙuri ya sa ya ci abincin da ya fi ƙarfinsa.

Na Jej Je: (A cikin wasar Na Jej Je) Wasan yara maza da mata da ke da zubi da tsari irin na wasan Lakkuma-Lakkuma Lale.

Na Karofi: (A cikin wasar Matar Na Karofi) Yarinyar da take fitowa a matsayin ango a cikin wasan.

Na Ƙale: (A cikin wasar Na Ƙale) 1: Wasan yara maza da mata da ta shafi ɗaurawa. Yayin da yara suka ɗaura, duk wanda ya hango abinci a hannun abokinsa, idan ya furta: “Na ƙale,” to abincin ya zama nasa. 2: Furucin da mai wasa ke yi domin mallake abin ci da ke hannun abokin wasa.

Na Ɗaura Kallabi: (A cikin wasar Na Ɗaura Kallabi) Wasan dandali ne na yara mata da ke ɗauke da waƙa.

Na Ɗiba: (A cikin wasar Na Ɗiba) Ɗaya daga cikin wasannin gamayya tsakanin yara maza da mata, inda ake tara ƙasa a sanya tsinke a sama; sannan masu wasa su riƙa ɗiban ƙasar a hankali, ɗaya bayan ɗaya. Ba a so wannan tsinke ya faɗi yayin da wani ke ɗiban ƙasar.

Na Yaya? (A cikin wasar Na Yaya?) Ɗaya daga cikin wasannin mata na dandali da ke tafiya da waƙar da ta ƙunshi zuga da kirari ga samarinsu.

Nasara: (A cikin wasar Yaƙi) Yayin da ɓangare ɗaya daga cikin masu wasa suka gudu, to an ci nasa a kansu.

Naɗa Sarki: (A cikin wasar girjim) Ƙasa ɗora ɗa ɗaya a kan ɗan da ya shiga sarki domin su kasance biyu a gida guda.

Ni Cadi Zan Tafi: (A cikin wasar Ni Cadi Zan Tafi) Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga ciki ke shigar dattawa sannan ya ɗauki jakar faggon kaya. Zai riƙa nuni cikin waƙa cewa Cadi zai tafi saboda fatara ta masa yawa, sauran yara kuwa za su riƙa nuna masa ba shi kaɗai fatarar ta takurawa ba.

Ni Karkashi: (A cikin wasar Ni Karkashi) Wasan yara mata na dandali da ke tafiya da waƙa. Yana kama da wasan Goyon Baya. Sai dai shi ba tafiya ake yi ba yayin da aka yi ta.

Ni Kura-Kura: (A cikin wasar Ni Kura-Kura) Wasan dandali na yara inda yara kan yi layi tare da kama bayan juna. Uwarsu kuma za ta kasance a gaba. Sannan kura za ta kasance tana fuskantarsu. Uwa za ta riƙe tare kura yayin da kura ke ƙoƙarin kama ɗaya daga cikin‘ya’yan.

Ni Madara Ni Zuma: (A cikin wasar Ni Madara Ni Zuma) Wasan yara mata da ke ɗauke da waƙa mai nuna danƙon zumunci da ke tsakaninsu.

Ni Mota Nake So: (A cikin wasar Ni Mota Nake So) Wasan yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa mai bayyana muradin zucinsu, musamman ta ɓangaren aure.

No: (A cikin wasar Kofi) Amsar da wanda ya rufe wa mai tafiya ido zai bayar yayin da mai tafiyar ya kuskure hanya.

No: (A cikin wasar sabis) furuci da abokan wasa ke yi yayin da gidan da za su ba da sabis suka ambaci: “sabis.” Wannan furuci na nuna cewa, ba su shirya a fara wasa ba.

Noti-Noto: (A cikin wasar Noti-Noti) 1: Wasan yara maza ne na dandali wanda ke da zubi da tsari irin na wasan jini da jini. Shugaban wasa zai riƙa lissafo sunayen abubuwa. Sauran masu wasa kuwa za su riƙa tantancewa tsakanin abubuwa masu noti da marasa noti. 1: Furuci na farko da shugaban wasa ke yi yayin da za a fara wasa.

O Aliyo: (A cikin wasar O Aliyo) Ɗaya daga cikin wasannin gaɗa na yara mata da ke ɗauke da waƙa mai faɗakarwa game da doguwar tafiya da maza kan yi su bar matansu na aure a gida.

O Maciji: (A cikin wasar O Maciji) Wasan yara maza da mata na dandali inda yara sukan haɗa hannayensu yaro guda kuma ya hau, a riƙa lila shi.

Odada: (A cikin wasar Odada) Wasa ne na yara mata da ke kama da wasan babunna.

Odi-Odi: (A cikin wasar Odi-Odi) Ɗaya daga cikin wasannin yara maza da mata. Yana kama da wasan Ɓuye-Ɓuye. Abin da ya bambanta su shi ne waƙar da ke cikin kowace wasa. Sannan a wasan rodi-odi, ba dole ne a ɓuya ba.

Odiye: (A cikin wasar sabis) Yayin da mai ba da sabis ya bayar sai kuma sabis ɗin ta mutu a gidansa, to ya yi odiye. A wannan yanayi, abokan karawarsu sun samu maki, su kuma sun faɗi.

Ojo: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi ɗaya da ake yi yayin da aka samu musu ko jirel.

Oriyo: (A cikin wasar Babunna) 1: Wacce ta faɗi a wasan babunna; ta ƙarshen fita. 2: Waƙar zolaya da ake yi wa oriyo.

Ƙeta: (A cikin wasar Carafke) Yayin da mai baji ta yi mai cunkus da niyyar mai yi ta faɗi, to ta yi ƙeta.

Ƙeta: (A cikin wasar langa) yin gula ko ƙulli yayin langa. Idan haka ta faru akan kira saranda sannan a yi wa mai wannan hali gargaɗi.

Ƙirge: (A cikin wasar Guro) Lissafa ‘ya’ya da mai wasan guro ke yi (A cikin wasar mafi yawanci da idanu) domin gane wurin da zai yi kanda kafin ya fara tafiya.

Ƙirji: (A cikin wasar langa) kalma da ke nuna bankaɗar ɗan wasa da ƙirji a maimakon hannu da niyyar kasha shi. Misali: Musa ya yi wa Audu ~ sai da ya kai ƙasa.

Ƙodo: (A cikin wasar ‘yar Ramel /Carafke) Dutsin da ake amfani da shi wurin jefawa da cafewa yayin wasa.

Ƙonewa: (A cikin wasar Guro) Ƙara ɗa a kan ‘ya’yan gidan da aka riga aka haihu ba tare da an ɗebe haihuwar ba.

Ƙulli: (A cikin wasar langa) daidai da gula.

Ƙwacewa: (A cikin wasar Ɗan Balum-balum) Karɓar wasa daga hannu mai gudanarwa.

Ƙwallo: (A cikin wasar Babana Ya Saya Min Ƙwallo) Mulmulen ƙasa mai damshi da yara ke ɗauka a hannu domin su buga da ƙafa a matsayin ƙwallon da babansu ya saya masu.

Ƙwanƙwalati: (A cikin wasar Ƙwanƙwalati) 1: Wasasa ne na yara maza inda ake kwaikwayon yadda ake wasan ƙwallon ƙafa ta hanyar amfani da ƙwanƙwalati a matsayin ‘yan ƙwallo. 2: Marfin ababan sha na kwalba kamar fanta da mirinda da maltina da makamantansu.

Ƙwanƙwalati: Marfin ɗaya daga cikin ababan sha na kwalba, kamar fanta ko mirinda da makamantansu.

Ƙwaƙwale: (A cikin wasar Ƙwaƙwale) Wasan yara maza da mata inda ake ɓoye abubuwa daban-daban (A cikin wasar dangin ƙwallon dabino da na aduwa da na ɗinya da na kanya da makamantansu) a cikin ramuka, a nemi da masu wasa su bayyana abin da aka ɓoye cikin kowane rami.

Rabali: (A cikin wasar Robali) Ɗaya daga cikin jerin nau’ukan wasanni da ake gudanarwa ta hanyar amfani da robali.

Rabi Da Audu: (A cikin wasar Rabi Da Audu) Wasan tashe na yara mata inda yara biyu ke fitowa a matsayin mata da miji, sannan dattawa. Wadda ta fito a matsayin miji za ta yi shigar maza dattijai. Za kuma su riƙa tiƙar rawa a wurin tashe. Tashen na ɗauke da waƙa.

Rabi: (A cikin wasar Rabi Da Audu) Sunan wadda ke fitowa a matsayin matar Audu a cikin tashen.

Ragadada: (A cikin wasar Ragadada) Wasan tashe na yara mata da ke faɗakarwa game da kwaɗayi da ɓatar da kuɗi kan bubuwan ƙwalama.

Raguwa: (A cikin wasar Basha) Wadda ta faɗi yayin da ake dokawa da juna.

Ragwas: (A cikin wasar Belbela-Belbela) Furucin ƙarshe na cikin waƙar wasan. Da zarar an furta, dole ne kowa ya ƙame.

Rakiyar-Kura: (A cikin wasar Jallu Wa Jallu) Rake-rake da akan yi tsakanin ‘yan gari biyu yayin wasa. Ma’ana idan ‘yar gari guda ta raka ‘yar wata gari, ɗaya daga cikin ‘yan garin da aka raka tasu za ta rako wadda ta yi rakiyar.

Rami: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Gurbin da ake zuba ‘ya’ya yayin wasa.

RaminCilli: (A cikin wasar ‘yar Cille) Ƙaramin rami da akan tona tsakiyar da’ira, wanda kasa ake gitta ‘yar cilli yayin da za a cilla.

Rana Ta Fito Gabas: (A cikin wasar Rana Ta Fito Gabas) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke tafiya da waƙa.

Randa Bakwai: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Yin mai wasa da ɗayalwa zuwa gomalwa sau bakwai.

Randa Biyar: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Yin mai wasa daga ɗayalwa zuwa gomalwa sau biyar.

Randa Biyu: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Yin mai wasa daga ɗayalwa zuwa gomalwa sau biyu.

Randa Huɗu: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Yin mai wasa daga ɗayalwa zuwa gomalwa sau huɗu.

Randa Shida: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Yin mai wasa daga ɗayalwa zuwa gomalwa sau shida.

Randa Takwas: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Yin mai wasa da ɗayalwa zuwa gomalwa sau takwas.

Randa Tara: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Yin mai wasa da ɗayalwa zuwa gomalwa sautara.

Randa Uku: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Yin mai wasa daga ɗayalwa zuwa gomalwa sau uku.

RandaƊaya: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Yin mai wasa daga ɗayalwa zuwa gomalwa sau ɗaya kacal.

Randa: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Yawan‘ya’ya da za a riƙa jawowa daga rami.

Randa: (A cikin wasar Babunna) Babunna zuwa riɗana shi ne randa ɗaya. Mai wasan da ta ci daga babunna zuwa riɗana to ta ci randa ɗaya.

Randa: (A cikin wasar Bena) Yawan zagaye gidaje da za a yi kafin a yi talle.

Rata: Tazara da ake bayarwa domin masu wasa su gudu kafin mai kamu ya bi su.

Rawa: (A cikin wasar sabis) daidai da suma.

Rawa: (A cikin wasar Wur-Wur) Kalma ce da ake amfani da ita wurin bayyana cewa, wur-wur ba zan-zan take ba. Ma’ana tana kaɗawa ko karkarwa yayin da ta tashi.

Reno: (A cikin wasar sabis) yin amfani da hannu domin garo ƙwallon sabis a hankali har a zo dab da layi sannan a jambaɗe ta da sanda da nufin yin waju ga abokan wasa. Misali: Ya yi wa Jummai nisa bayan ya ~ sabis ɗin zuwa jikin layi.

Rijiya: (A cikin wasar Rijiya) 1: Wasan yara maza da ake gudanarwa kan yashi. Akan toni rami mai ɗan faɗi bisa yashi sannan yara su sanya ƙafafu ciki a bunne. Sai kuma su yi rige-rigen fitar da ƙafafun nasu. Duk wanda ya riga fitarwa zai riƙa dukan saura da riga, har sai sun fitar. 2: Sunan ramin da aka tona bisa yashi yayin wasan.

Riɗana: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na goma sha ɗaya a wasar babunna.

Rurujina: (A cikin wasar Rurujina) 1: Wasan yara mata na dandali da ake gudanarwa a zaune. Ya shafi kifa hanu da buɗewa a ƙasa tare da waƙa. 2: Furucin da ke nufin a kifa hannu a ƙasa.

Ruwa ba ta Bayar ba: (A cikin wasar Langa) Furuci da gidan da ke da ruwa ke yi yayin da abokan karawarsu suka far musu ba tare da sun (A cikin wasar gidan ruwa) ba da sanarwar a fara wasa ba. Misali: ~ kuka taho.

Ruwa Biyu: (A cikin wasar langa) duba ruwa ɗaya.

Ruwa Mai Malale: (A cikin wasar Ruwa Mai Malale) Nau’in wasan yara mata na dandali da ke tafiya da waƙa.

Ruwa ta Bayar: (A cikin wasar Langa) Furuci da gidan da ke tare da ruwa suke yi domin a fara langa.

Ruwa ta Tsinki: (A cikin wasar langa) furuci da ke nuna da cewa, ruwa ta arce domin ta je da sha. Misali: Kai! Ku tare, ~.

Ruwa ta Yi Saranda: (A cikin wasar langa) furucin da ruwa ko ‘yan gidan ruwa suke yi domin a dakata da wasa ba tare da ‘yan wasa sun sake lako ba.

Ruwa Uku: (A cikin wasar langa) duba ruwa ɗaya.

Ruwa Ɗaya: (A cikin wasar langa) Furucin da ke nuna yawan ruwan da ‘yan gida za su yi kafin a karɓe su a ruwa. Wato sai sun yi rashin nasara a ruwa misali ɗaya ko biyu ko uku ko sama da haka, kafin a karɓe su daga ruwa. Misali: Ku zo mu yi langa ‘yar ruwa uku.

Ruwa: (A cikin wasar Langa) 1 (A cikin wasar suna) Wanda yake tamkar sarki a rukunin langa. Shi ne ke zuwa domin sha. Yayin da aka kasha ruwa, to tamkar an kasha kowa ne daga wannan gida; saboda haka wasa ya ƙare. Misali: Abubakar ne ~nmu. 2 (A cikin wasar suna) Turmi ɗaya ko zagaye ɗaya na wasa. Wato daga bayarwar ruwa zuwa lokacin da aka kasha ruwa ko ruwa ta sha. Misali: Sun yi ~ huɗu a jere ba a kashe su ba.

Ruwan Jiya Ba Ta Tsami: (A cikin wasar langa) furucin da ‘yan gidan ruwa suke yi yayin don nuna wa abokan karawarsu cewa, ruwar da ta yi a rowan baya, ita za ta sake yi yanzu.

Ruwan Jiya: (A cikin wasar langa) ruwa da ta yi nasara ta hanyar sha ko jaga, sannan ta zarce a matsayin ruwa a ruwa na gaba.

Ruwan Ƙauye: (A cikin wasar Ruwan Ƙauye) Daya daga cikin wasannin mata na dandali da ke da tsarin cilli da direwa.

Ruwaye: (A cikin wasar Ruwaye) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa mai nuna amfanin ruwa tare da bayyana sunayen abokai da ‘yanuwa na mai rera waƙar.

Sa Baki: (A cikin wasar girjim/Guro/Uku Saɓi/Siri-Santa) Idan wani wanda ba da shi ake wasa ba ya riƙa ba da shawarar wuraren da za a yi tafiya, to yana sanya baki ke nan.

Sa Hanu: (A cikin wasar sabis) furucin da ‘yan wasa ke yi wa ɗan gidansu da nufin su ankarar da shi domin ya yi amfani da hannu wajen rayar da sabis da ta suma. Misali: Musa ~ kar ta mutu.

Sabana: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na takwas a wasan babunna.

Sabis: (A cikin wasar sabis) 1: (A cikin wasar suna) Wani wasa da ake amfani da ƙaramin sanda mai lanƙwasasshen kai da kuma takalmi silifa da aka yanke aka gyara zuwa rawul. Wannan wasa na gudana tsakanin garuruwa biyu. Misali: Yara suna wasar ~ a dandali. 2: (A cikin wasar suna) Silifa da na yanke aka gyara zuwa rawul domin a yi amfani da shi a matsayin ƙwallon sabis. Wani lokaci akan haɗa wannan rawul na yankakken silifa biyu ko uku a ɗinke da zare da allura domin ya yi kauri da nauyi. Misali: Musa ya jambaɗi ~. 3: (A cikin wasar aikatau) garawa abokan karawa ƙwallon sabis da hannu domin a fara wasa. Misali: Musa ya yi ~ mai kyau. 4: (A cikin wasar suna) kasancewar wani gari su ne za su ba da sabis (A cikin wasar gara sabis) domin a fara wasa. Misali: Yanzu ~ ɗinmu ne. 5: Furucin da mai bayar da sabis ke yi kafin ya bayar. Wannan na matsayin tambayar abokan wasa ko sun shirya a ba su sabis.

Sadaka: (A cikin wasar Afajana) Yayin da sarki ya ba da damar a ɗauki riga ba tare da ya yi hanƙoron taɓa mai ɗauka ba, to ya ba da sadaka.

Sadam: (A cikin wasar Sadam) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata mai zubi da tsari irin na babunna.

Sai Ka Yi Rawa A Nan: (A cikin wasar Sai Ka Yi Rawa A Nan) Wasan tashe na yara maza da mata inda akan ɗaya daga cikin masu tashe ke yin shigar dattijo tare da riƙe sanda domin dogarawa yayin tafiya. Yakan yi rawa a wurin tashe bayan sauran yara sun matsa kan cewa sai ya yi rawa, cikin waƙar tashen.

Sakel: (A cikin wasar Bena) Sake jifa yayin da ‘yar da aka jefa ta hau layi.

Salamatu: (A cikin wasar Salamatu) 1: Wasan gaɗa na dandali da ke tafiya da waƙa. 2: Mace a romonka da ta samu ɗaukaka zuwa gidan sama tare da samun abinci iri-iri na walwala da jin daɗi.

Sallar Kwaɗi: (A cikin wasar Sallar Kwaɗi) Wasa ne na yara maza da ke da sigar salla. Akan samu liman da ladan da kuma mamu. Liman zai yi abin dariya cikin zance ko aiki. Ladan kuma zai maimaita ba tare da kuskure ba. Bayan ladan sai mamu ma su maimaita. Yayin da wani ya yi kuskure, to zai fuskanci sakamakon wasa.

Salo-Salo: (A cikin wasar Salo-Salo) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa, inda mai rerawa ke nuna ƙawayenta na ƙut-da-ƙut.

Sama Indo: (A cikin wasar Sama Indo) Ɗaya daga cikin wasannin gaɗa da ke ɗauke da waƙa mai cike da jinjina da kirari ga samarin yara mata da ke gudanar da wasan.

Samodara: (A cikin wasar Samodara) 1: Wasan tashe na mata wanda jagora ke sanya tufafi marasa kyau tare da yin kwalliya marar tsari. Takan yi tinƙaho da kaya da kuma kwalliyarta yayin tashe. 2: Sunan jagora a wasan tashe na samodara.

Sandar Sabis: (A cikin wasar sabis) ɗan ƙaramin sanda ne mai ƙauyayyen kai da ake amfani da shi wajen wasan sabis.

Saranda: (A cikin wasar girjim) Janye ‘ya’yan wasa baya.

Saranda: (A cikin wasar langa) furucin da ake yi domin a dakata da wasan langa amma ba tare da kowa ya sake lako ba.

Sarki: (A cikin wasar ‘yar Ganel) Wanda ke keɓewa daga sauran ‘yan wasa. Shi ke faɗin sunayen abubuwan da za a gano.

Sarki: (A cikin wasar ‘yar Sarki 1) Wanda ke yanke hukuncin da za a zartar wa ɓarawo yayin da ya sake sata.

Sarki: (A cikin wasar Afajana) Wanda ba ya aje rigarsa yayin wasa. Duk wanda ya ɗau rigarsa, zai riƙa bugun sarki, har sai sarkin ya taɓa wani daga cikin masu wasa.

Sarki: (A cikin wasar girjim) 1: Ɗaya daga cikin gidaje huɗu da ke kusurwowi a wasan girjim. 2: Ɗan mutum da ya shiga ɗaya daga cikin gidaje biyu na kusurwa a ɓangaren abokin karawa, da aka ɗora wa ƙarin ɗa (A cikin wasar suka zama biyu a gida ɗaya); wanda kuma yake da dammar tsallake gidaje yayin tafiya.

SarkinGwauro: (A cikin wasar Gwauro) Shugaban wasan gwauro.

Sat: Mai wasa da zai yi da zarar sekon ya gama.

Sata: (A cikin wasar ‘yar Sarki 1) Yayin da ɓarawo ya jefa takalma, sai ɗaya ya kife ɗaya kuma ya ɓuɗe, to ya yi sata.

Sata: (A cikin wasar sabis) yayin da ɗan wani gari ya doki sabis alhali tana tsallaken layi, bagiren abokan karawarsu, ba tare da ya ambaci eskus ba.

Satar Gaba: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Tura ɗa ko ‘ya’ya su tsallake rami zuwa gaban wata‘yar wasa.

Saya: (A cikin wasar sabis) kalmar da ke nuna aminta ko rashin aminta da sabis da aka bayar.

Sayen Gida: (A cikin wasar Bena) Yin zane a gidan da ‘ya ta faɗa bayan an jefa ta yayin da aka ga ba talle. Akan yi wannan jifa alhali an juya wa gidajen baya.

Sekon: Mai wasan da zai yi wasa da zarar fes ya gama.

Sha: (A cikin wasar Gori/koɗi) rankwaɗawa ɗan wasan da ya faɗi gori a bayan hannunsa, a matsayin sakamakon wasa.

Sha: (A cikin wasar Langa) 1: (A cikin wasar suna) Wurin da ya zama dole ruwa ta taɓa kafin ta yi nasara. Misali: Bishiyar can ce ~ 2: (A cikin wasar aiki) Taɓa wurin sha da ruwa take yi. Misali: Ruwa ta ~.

Shanyar Kuliri: (A cikin wasar Shanyar Kuliri) Wasan yara mata ne mai sigar goye-goye cikin wani salo na daban.

Shanye: (A cikin wasar Guro) Yayin da mai wasan guro ya sanya dutsin ƙarshe da ke hannunsa yayin tafiya a gidan abokin karawarsa wanda kuma ciki ne, to ya shanye cikin. Saboda haka zai ɗebe ‘ya’yan sun zama haihuwarsa a maimakon haihuwar abokin karawarsa. Idan kuma a gidan mai tafiyar ne haka ta faru, to ya shanye cikinsa da kansa.

Sharel: (A cikin wasar Robali) Lokacin da mai dukan robali ya murza takalmi ko ya ja bayan ya riga ya buga a wasan robali ‘yar sharel, to ya yi sharel. Dokar robali ba ta yarda da sharel ba.

Shaye: (A cikin wasar Digi-digi) Shafa kan masu ɗaya daga cikin waɗanda suka fita da mai kamu take yi domin wadda aka shafa kan ma ta zama mai kamu.

Shidalwa: (A cikin wasar ‘yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke ‘ya’ya shida kafin miyar da saura rami.

Shiga Sarki: (A cikin wasar girjim) Saka ɗa a ɗaya daga cikin gidaje biyu na kusurwa da ke ɓangaren abokin karawa.

Shiga: (A cikin wasar A Fim-Fim-Fim) Shigowa cikin masu wasa tare da gudanar da ita tare da masu yi.

Shugaba: (A cikin wasar Gyara Zamanki Kamar Ba Ke Ba) Jagorar ɗaya daga cikin ɓangarori biyu da ke wasa tsakanin juna.

Shunku: (A cikin wasar Guro) Daidai da coge.

SiginaUkuDanja: (A cikin wasar Sigina Uku Danja) Wasan yara maza da mata inda mai wasa ke dukan abokin wasansa bayan ya yi sigina uku ba tare da abokin wasan ya farga ba.

Sigina: (A cikin wasar Sigina Uku Danja) Tsuke yatsun hannu da buɗe su.

Sillen Kara: (A cikin wasar Sillen Kara) Wasan yara mata na dandali da ke tafiya da waƙa. Yana kama da wasan Goyon Baya. Sai dai shi ba tafiya ake yi ba yayin da aka yi shi.

Sitanda: (A cikin wasar sabis) daidai da kwanciyar karuwa.

Sittana: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na bakwai a wasan babunna.

Sizin: (A cikin wasar girjim) 1: Ɗauke ɗan abokin karawa da ya samu damar ci, kuma bai cin ba; ko dai bisa kuskure ko kuma gudun ci biyu ko makamancin haka. 2: Furucin da mai wasa ke yi yayin da zai ɗauki sizin.

Son Makaru: (A cikin wasar Son Makaru) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke tafiya da waƙa da tafi da ke kan tsari da ƙa’ida.

Soyayya Iri-Iri Ce: (A cikin wasar Soyayya Iri-Iri Ce) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke tafiya da waƙa mai hannunka-mai-sanda game da soyayya.

Sukuta: (A cikin wasar Dokin Almajire) Wannan furuci ya kasance amshin da yara za su yi ta maimaitawa yayin da ake waƙar wasan.

Suma :(A cikin wasar  sabis) yayin da ƙwallon sabis ta kwanta amma ba ta daina motsi ba. A irin wannan yanayi, ɗan wasa na gaggauta bugun ta domin ta bar gidansu. Misali: Har sabis ɗin ta ~ amma Musa ya yi gaggawar jambaɗar ta kafin ta mutu.

Sunkuya Dundu: (A cikin wasar Sunkuya Dundu) Wasan yara maza da mata inda duk wanda ya sunkuya, abokin wasansa zai fake shi ya ɗira masa dundu.

Ta Girgiza: (A cikin wasar Carafke) Furucin da ake yi domin a ja hankalin mai wasa cewa an samu girgiza a lokacin da take faman cafkel.

Tafa-Tafa: (A cikin wasar Tafa-Tafa) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ake gudanarwa tare da tafi da waƙa.

Tafiya: (A cikin wasar Ba Za Ku Ga Tafiyar ‘yata Ba) Tura tsakuwa a cikin ƙasa da ‘yan yatsu yayin da ake faman ɓoye ta.

Tafiya: (A cikin wasar Bena) Yin tsalle da ƙafaɗa ya cikin gidajen bena tare da bin ƙa’ido jin wasa.

Tafiya: (A cikin wasar girjim) 1: Matsar da ɗa zuwa gaba ko baya ko gefe ko ci.

Tafiya: (A cikin wasar Guro) 1: Zagayen wasa ɗaya na guro. Wato daga lokacin da aka fara ɗiban‘ya’yan gidan farko zuwa lokacin da aka bai wa mai tafiya guro. Misali: Idan an ƙare wannan ~r a ba ni bukka. 2: Ɗaukar ‘ya’yan wasa da mai wasan guro zai yi ya kewaye ramuka gabaɗaya har zuwa wurin kandarsa. Misali: Musa ya ƙona haihuwarsa a ~r da ya yi.

Tafiya: (A cikin wasar Kofi) Tura yatsa gaba cikin layin kofi, da nufin kai wa ƙarshensa.

Ta-huce: (A cikin wasar girjim) Furucin da ake wa abokin wasa domin jan hankalinsa kada ya ɗauki sizin domin ta huce.

Taka Ɓurme: (A cikin wasar Taka Ɓurme) 1: Wasan yara maza inda suke tonon rami madaidaici sannan su sanya tsinkaye da leda a sama, su kuma mayar da ƙasa a hankali yadda zai yi kamar ba rami a wurin. Za kuma su yaudari wani yaro har sai ya zo ya taka, ramin ya ɓurma da shi. 2: Sunan ramin da aka tona yayin wasan.

Takwaswa: (A cikin wasar ‘yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke ‘ya’ya takwas kafin mayar da saura rami.

Talana: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na huɗu a wasan babunna.

Talili-Tali Yambo: (A cikin wasar Talili-Tali Yambo) Wasan yara maza da mata da ake gudanarwa a zaune, inda kowane yaro ke ɗora ƙafarsa ɗaya bisa cinyar ɗanuwansa. Yana tafiya da waƙa mai addu’a game da samun amfanin gona mai kyau.

Talle: (A cikin wasar Bena) Ɗora ‘yar jifa a bayan hannu tare da yin tafiya da ita zuwa dukkanin gidaje ba tare da ta faɗi ba.

Tama Yaki Tama: (A cikin wasar Tama Yaki Tama) Wasan gaɗa na yara mata da ke ɗauke da waƙa mai nuna sana’o’in Hausawa daban-daban.

Tamana: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi na tara a wasan babunna.

Tambo: (A cikin wasar Tambo) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata mai zubi da tsari irin na babunna.

Tana Gagarel: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Furuci da ke nuna cewa, dokar wasa ta ba da dama ko tsaɓin gagarel.

Tana Ƙonewa: (A cikin wasar Guro) furucin da ake yi domin nuna cewa dokar wasa ba ta ba da damar mai wasa ya ɗauki haihuwa ba bayan ta ƙone.

Tana Sa Baki: (A cikin wasar girjim/Guro/Uku Saɓi/Siri-Santa) Furucin da ke nuna cewa, dokar wasa ta ba da damar a sa baki a wasan da ake gudanarwa.

Tana Satar Gaba: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa inda mai wasan da ta yi satar gaba ba ta faɗi ba.

Tana Sizin: (A cikin wasar girjim) Furucin da ake yi domin nuna cewa, dokar wasan a wannan lokaci ta ba da dama a yi sizin.

Taralwa: (A cikin wasar ‘yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke ‘ya’ya tara kafin mayar da saura rami.

Tarko: (A cikin wasar girjim) Ajiye ɗa a hanyar shiga sarki saboda a yi sizin ɗin ɗan abokin karawa yayin da ya wuce ba tare da ya ci ɗan ba, dalilin hankalinsa ya karkata zuwa ga mararin shiga sarki.

Tarkon Horon Wawa: (A cikin wasar Tarkon Horon Wawa) Wasan yara maza da masu wasa za su tara rigunansu wuri ɗaya. Za kuma a ɗaura wa mutum ɗaya igiya a ƙugu. Wani daga cikin‘yan wasa zai riƙe igiyar. Yaron da aka ɗaura wa igiyar kuwa zai nannaɗa riga ya riƙe hannunsa. Duk wanda ya zo ɗaukar rigarsa, yaron zai riƙa dukansa da wannan riga da ya nannaɗa. Wanda ke riƙe da igiya da aka ɗauke shi da ita kuwa zai riƙa jansa baya.

Tashi Mai Kwaɗayi: (A cikin wasar Tasihi Mai Kwaɗayi) Wasan tashe na yara maza inda mai kwaɗayi ke yin zaman dirshan. Sauran masu wasa za su riƙa kiransa da ya tashi cikin waƙa, shi kuwa zai riƙa amsawa da ba zai tashi ba sai an ba shi.

Tashi Wali: (A cikin wasar Tashi Wali) Wasan yara maza ta tashe inda Wali ke shiga irin ta malamai, sannan ya riƙa ƙoƙarin tashi sama yayin da ake tashe. Wasan na tafiya da waƙa wadda a cikinta Wali ke cewa zai tashi, saura kuwa na masa magiyar kada ya tashi.

Tashi: (A cikin wasar Bindiga) Ƙara da bindiga takan yi yayin da aka buga.

Tashi: (A cikin wasar Wur-Wur) Fara wainuwa da ci gaba da wainuwar wur-wur yayin da ake jan ta.

Tatike: (A cikin wasar Guro) kalmar da ke nuna an janye gidajen mai wasan guro gaba ɗaya. Misali: An ~ gidajen Musa.

Tatike: (A cikin wasar Robali) Wanda aka ƙarar masa robalin da ya mallakar yayin wasa, to an tatike shi.

Tattaba-Tattaba: (A cikin wasar Tattaba-Tattaba) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa inda mai rerawa ke ambaton sunayen ƙawaye da ‘yan’uwanta.

Taɓarya: (A cikin wasar Dokin Kara) Kafa doki a ƙasa tare da ɗangalafe shi.

Taɓarya: (A cikin wasar Taɓarya) 1: Wasan yara mata da ya shafi amfani da zaren buhu domin sarrafa shi da yatsun hannu tare da mayar da shi wata siffa da yaran suke ba wa suna daban-daban. 2: Ɗaya daga cikin abubuwan da yara ke haɗawa yayin wasa.

Taɓaɓɓe: (A cikin wasar taɓaɓɓe) wasan tashe wanda yara kan ɗaura wa ɗaya daga cikinsu igiya a ƙugu. Shi kuma zai shafe fuskarsa da gawayi ko baƙin bayan tukunya sannan ya riƙe taɓarya ko sanda. Zai riƙa barazanar dukan mutane da sunan shi taɓaɓɓe ne, yaran kuma za su riƙa janye shi ta hanyar amfani da igiyar da ke ɗauke a ƙugunsa. Yaron zai riƙa waƙa sauran yara suna amsawa.

Taya: (A cikin wasar Taya) Wasan yara maza inda suke amfani da taya rabin hawa musamman mashin. Akan gara tayar ta hanyar amfani da kara ko gajeren itace marar kauri sosai.

Timiri: (A cikin wasar sabis) daidai da aike.

To Iya: (A cikin wasar To Iya) Wasan tashe na yara mata inda ake nuna uwar ‘ya’ya tana tattara ‘ya’yanta kan su tafi, su bar gida kasancewar mijinta ya kore ta a dalilin cin abinci sama da ƙima (A cikin wasar babbar loma).

Toye: (A cikin wasar Bindiga) Ƙaramar ƙara tare da hayaƙi da bindiga takan yi yayin da aka buga.

Toye: (A cikin wasar Guro) Daidai da ƙone.

Tsakiyata Ta Tsinke: (A cikin wasar Tsakiyata Ta Tsinke) Wasan yara mata da ke tafiya da waƙa mai nuna ɗabi’a da al’adar kunya.

Tsallake: (A cikin wasar Guro) wuce wani gida ba tare da an ajiye masa ɗa ba yayin da ake tafiya.

Tsalle: (A cikin wasar girjim) Daidai da doguwar tafiya.

Tserel: (A cikin wasar Terel) Wasan yara maza da mata inda ake rige-rigen gudu daga wani wuri zuwa wani wuri.

Tsinkewa: (A cikin wasar langa) fita da gudu da ruwa take yi domin ta je ta sha.

Tsintowa: (A cikin wasar Carafke) Nemo wasu adadin‘ya’ya daidai da na juna kafin fara wasa.

Tsoho Da Gemu: (A cikin wasar Tsoho Da Gemu) Wasan yara maza na tashe inda ɗaya daga cikinsu ke shigar tsofi. Wasan yana ɗauke da waƙar da ke nuna cewa, mai shigar tsofi tsoho ne ɗauke da gemu wanda ya yi tsufar da ke buƙatar a taimaka masa.

Tsoho: (A cikin wasar Tsoho Da Gemu) Wanda ya yi shigar tsofi yayin wasan.

Tsohuwa ta HauMota: (A cikin wasar Taɓarya) Ɗaya daga cikin abubuwan da yara ke samarwa yayin wasan.

Tsuguno: (A cikin wasar Babunna) Duƙawa ƙasa da masu kaɗa oriyo ke yi gudun kada a yanka su.

Tunkuɗa: (A cikin wasar langa) daidai da bangaza.

Turawa: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Mayar da wasu adadin ‘ya’ya da barin wasu a wajen rami yayin da dokar wasa ‘yar turel ce.

Turawa: (A cikin wasar girjim) Ba wa abokin wasa dammar ya ci ɗa ɗaya saboda a masa ci biyu ko sama da haka.

Turke: (A cikin wasar Afajana) Wanda suke tsayawa gaban riguna da aka tara su riƙe riga guda daga gefe da fefenta shi da sarki.

Turke: (A cikin wasar Robali) Robali guda ɗaya da ake ajiyewa kafin a fara jifa a wasan robali ‘yar jifa.

Tuwon Ƙasa: (A cikin wasar Tuwon Ƙasa) Wasan tarayya tsakanin yara maza da mata, inda suke kwaikwayon yadda ake abinci da kuma raba abincin.

Ukulwa: (A cikin wasar ‘yar Ramel) matsayin da mai yi za ta kai wadda ake buƙatar ta ɗauke ‘ya’ya uku kafin mayar da saura rami.

Uwa: (A cikin wasar Kande Mahaukaciya) Wadda take fitowa a matsayin mahaifiyar Kande yayin wasan.

Uwa: (A cikin wasar Ni Kura-Kura) Wadda ke kasancewa kan gaba a layi. Ita ke tare kura don kada ta kama ɗaya daga cikin ‘yan wasa.

Wagina: (A cikin wasar Rurujina) Furucin da ke nufin a buɗe hannun da ke kife a ƙasa.

Waju: (A cikin wasar sabis) daidai da aike.

Wali: (A cikin wasar Tashi Wali) Wanda ya yi shiga rmalamai da kuma ke ƙoƙarin tashi sama yayin wasa.

Wan Tu Fayif: (A cikin wasar Babunna) Kaɗi da ake sake yi bayan an kamala wasa. Akan kaɗa daga babunna zuwa hamsana, sannan a sauko daga babunna zuwa arbana, zuwa talana, zuwa ishina, zuwa gomana. Daga ƙarshe sai a kaɗa babunna kaɗai.

Waran Warash: (A cikin wasar Waran Warash) Wasan yara maza da mata inda kowane ɗan wasa ke ɗaukar suna. Daga nan za a sanya yatsu ƙasa, a kuma lissafa. Duk wanda lissafi ya ƙare kan sunan da ya zaɓa, to ya ci nasara.

Wargaje: (A cikin wasar Fanka) Faɗuwa da rugujewar riƙe hannaye da haɗa ƙafafu da aka yi yayin da ake fanka.

Wa-Ta-Gangano: (A cikin wasar gori/koɗi) salon wasan gori ne wanda ake gara gori a jira ta har ta faɗi da kanta. Duk wanda ta fuskanta yayin da ta faɗi, to shi za a sha a matsayin wanda ya faɗi.

Waye Ruwa?: (A cikin wasar langa) Tambayar da ‘yan gidan da ba su ke da ruwa ba suke yi domin a fayyace musu ruwa.

Wur-Wur: (A cikin wasar Wur-Wur) 1: Wasa ne na yara maza inda suke ƙwanƙwasa ƙwanƙwalati har sai ya zama mai faɗi da kaifi. Sai kuma a sanya masa zaren buhu a tsakiya yadda za a sarrafa shi ya riƙa wainuwa. Akan kara tsakanin yara da tsummar tsinka wur-wur ɗin juna. 2: Sunan kayan aikin wur-wur.

Yanka: (A cikin wasar Babunna) Sanya hannun da oriyo ke yi a wuyan ɗaya daga cikin masu kaɗa mata oriyu, wadda idan ta yi haka, yarinyar da aka sanya wa hannu ita ce ta koma oriyo.

Yanka: (A cikin wasar Cincin Sakatum) Yayin da kura ya sanya gerin hannunsa a wuyan ɗan wasa, to ya yanka shi.

Yanka: (A cikin wasar Kumbukululu) Yayin da Kumbukululu ta sanya hannu a wuyar mutum, to ta yanka shi.

Yaƙi: (A cikin wasar Yaƙi) Wasan yara maza, inda suke kwaikwayon yadda ake yaƙi. Akan gudanar da ita tsakanin ɓangarorin yara biyu da suka fito daga unguwanni daban-daban.

Yaraye Dije: (A cikin wasar Yaraye Dije) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata na dandali da ke ɗauke da waƙa mai nuna ƙarya fure ta ke ba ta ‘ya’ya.

Yashe: (A cikin wasar Robali) Yayin da robalin da ke cikin kanti suka ƙare, to an yashe kanti.

Yau Na Zama Barar Mata: (A cikin wasar Yau Na Zama Barar Mata) Ɗaya daga cikin wasannin tashe na yara mata inda yarinya guda ke riƙe tsintsaya tare da yin shara a wurin da suka je tashe da sunan ta zama barar mata.

Yes: (A cikin wasar Kofi) Amsar da wanda ya rufe wa mai tafiya ido zai riƙa bayarwa don nuna cewa mai tafiya na kan daidai.

Yes: (A cikin wasar sabis): furuci da abokan wasa ke yi yayin da gidan da za su ba da sabis suka ambaci: “sabis.” Wannan furuci na nuna cewa, sun shirya a fara wasa.

Yi: (A cikin wasar ‘yar Ramel/Carafke) Yayin da layi ya zagayo kan mai wasa domin ta fara cilli, to yin ta ya zo.

Yi: (A cikin wasar Ɗan Balum-balum) Lokacin da mai wasa ta kasance jagora to yin ta ke nan. Idan aka buɗe ko tsuke tare sau uku, to ita aka ƙwace. Idan aka yi saɓanin buɗewa da tsukewa kuma, to mai yi ta ci. A haka za ta yi ta ci gaba har sai ta fita, ko kuma an ƙwace ta.

Yin: (A cikin wasar ‘yar Ramel) Dubayi.

‘Ya: (A cikin wasar Ba Za Ku Ga Tafiyar ‘Yata Ba) Tsakuwar da ake ɓoyewa cikin ƙasa yayin wasar.

‘Ya’ya: (A cikin wasar girjim) Ƙodagon goruba ko taura ko ƙwallon mangwaro ko duwatsu ko tsinkaye da ake amfani da su a matsayin abubuwan wasan girjim.

‘Ya’ya: (A cikin wasar Guro) Ƙananan duwatsu ko ‘ya’yan kanya ko makamantansu da ake amfani da su wajen guro. Misali: Mu yi amfani da duwatsu a matsayin ~.

‘Ya’ya: (A cikin wasar Ni Kura-Kura) Ɗaya daga cikin masu wasa wadda ba uwa ba kuma ba kura ba.

‘Ya’ya: (A cikin wasar To Iya) Sauran ‘yan wasa bayan uwa; sukan kasance a matsayin ɗiya ga wadda take uwa a cikin wasan.

‘Yan Asali: (A cikin wasar Kis-Kis-Kis An Kas-Kas-Kas) Masu tafiyan da suka fi sauran rukunonin masu tafiya iya wasa da samun nasara.

‘Yar Akuyata: (A cikin wasar ‘Yar Akuyata) Wasan da yara maza da mata ke yi ta hanyar amfani da balo-balo.

‘Yar Ato: (A cikin wasar ‘Yar Ato) Ɗaya daga cikin wasannin yara mata da ke da zubi da tsari irin na wasan Kwalba-Kwalba Dire.

‘Yar Baji …: (A cikin wasar Carafke) Dokar wasa da ke nuna cewa, da an ƙare cafkel ɗin wani adadin baji, to an kai ƙarshen wasa. Za a iya ‘yar baji ɗaya ko biyu ko sama da haka.

‘Yar Baji Ɗaya: (A cikin wasar Carafke) Dokar wasa da ke nuna cewa, da zarar an ƙare cafkel ɗin baji ɗaya to wasa ta kai ƙarshe.

‘Yar Cake: (A cikin wasar ‘Yar Cake) Wasan yara maza da mata inda ake amfani da kibiya ko wani abu mai tsini a riƙa cakewa a cikin gidajen dara da akan zana a ƙasa.

‘Yar Canjel: (A cikin wasar Bena) Dokar wasa da ta ba da damar a yi canji yayin wasa.

‘Yar Canka: (A cikin wasar ‘Yar Canka) Wasan yara maza da mata inda mai wasa ke ɓoye tsakuwa a ɗaya daga cikin hannayensa, sannan ya bukaci abokin wasansa ya canki hannun da aka ɓoye dutsen a ciki.

‘Yar Cille: (A cikin wasar ‘Yar Cille) 1: Wasa ne da ake gudanarwa tsakanin ɓangarori biyu. Na maza ne wanda kuma ake zana da’ira sannan a yi ƙaramin rami tsakiya, wanda daga nan ne za a riƙa cilla ƙaramin itace ko kara. Ɓangare guda na masu wasan za su yi ƙoƙarin kama wannan kara da aka cilla. 2: Kara ko ƙaramin itace da ake cillawa yayin wasa.

‘Yar Cilli: (A cikin wasar ‘Yar Cille) Daidai da ‘yar cille.

‘Yar Dutse Biyu: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Yin amfani da duwatsu biyu a matsayin ‘ya’yan wasa.

‘Yar Dutse Uku: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Yin amfani da duwatsu uku a matsayin ‘ya’yan wasa.

‘Yar Gagarel ~: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Furucin da ke nuna yawan gagarel da dokar wasa ta tanadar. Zai iya kasancewa ‘yar gagarel ɗaya ko biyu ko uku ko sama da haka.

‘Yar Gagarel: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ke nuna cewa, wadda ta yi gagarel za a ba ta dama ta sake gwadawa. Yawan damarmakin da za a ba ta ya danganta da gagarel nawa aka ba wa mai wasa.

‘Yar Gala-Gala: (A cikin wasar ‘Yar Gala-Gala) Wasa ne na yara mata da ke kama da wasan bena, sai dai ita gidajen da ake zanawa ba na dara ba ne. Sannan akan yi su ne bisa layi guda.

‘Yar Ganel: (A cikin wasar ‘Yar Ganel) Wasan yara maza na danali da ya ƙunshi sarki da bafade da kuma ‘yan wasa. Sarki kan aiko da bafada ɗaya ya faɗa wa ‘yan wasa sunan wani abu, su kuwa za su yi ƙoƙarin fayyace wane abu ne. Misali, idan bishiyar kuka ce, wace kuka guda ɗaya?

‘Yar Gociya: (A cikin wasar Lakkuma-Lakkuma Lale) Dokar wasa da ke ba da dama a mai ci ya yi gociya.

‘Yar Jifa: (A cikin wasar Robali) Nau’in wasan robali wanda masu wasa suke kafa turke sannan su ja baya su fara jefo robali. Duk wanda ya jefo robali kan wanda aka riga aka jefa, to zai ɗebe dukkanin waɗanda aka jefa ban da turke kaɗai.

‘Yar Kamfi: (A cikin wasar gori/koɗi) Doka a wasan koɗi da ke ba da dama mutum ya yi amfani da salo mai tsauri wurin kifewa domin samun maki sama da salo marar tsauri. Misali a yayin da doka ta nuna sai mutum ya kife koɗi sau ashirin a jere kafin ya ci, zai iya amfani da salon kifewa mai wuya, wanda kifewa ɗaya na daidai da kifewa goma ko biyar da makamantan haka.

‘Yar Kanti: (A cikin wasar Robali) Daidai da ‘yar taru.

‘Yar Masar Baba ne: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Furuci da ke nuna dokar wasan ta ƙunshi masar baba ne.

‘Yar Ƙwado: (A cikin wasar ‘Yar Ƙwado) Nau’in wasa na yara mata da ke kama da ‘yar ramel.

‘Yar Ramel: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Wasa ne da ake tona ƙaramin rami a zuba ‘ya’yan ramel, sannan a riƙa wurga ƙodago sama ana jawo‘ya’yan ramel tare da mayar da su daidai da dokar wasan.

‘Yar Rami: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Daidai da ‘yar ramel.

‘Yar Randa Bakwai: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ke nuna cewa, idan mai wasa ta yi ɗayalwa zuwa gomalwa sau bakwai to ta fita.

‘Yar Randa Biyar: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ke nuna cewa, idan mai wasa ta yi ɗayalwa zuwa gomalwa sau biyar to ta fita.

‘Yar Randa Biyu: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ke nuna cewa, idan mai wasa ta yi ɗayalwa zuwa gomalwa sau biyu to ta fita.

‘Yar Randa Huɗu: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ke nuna cewa, idan mai wasa ta yi ɗayalwa zuwa gomalwa sau huɗu to ta fita.

‘Yar Randa Shida: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ke nuna cewa, idan mai wasa ta yi ɗayalwa zuwa gomalwa sau shida to ta fita.

‘Yar Randa Takwas: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ke nuna cewa, idan mai wasa ta yi ɗayalwa zuwa gomalwa sau takwas to ta fita.

‘Yar Randa Tara: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ke nuna cewa, idan mai wasa ta yi ɗayalwa zuwa gomalwa sau tara to ta fita.

‘Yar Randa Uku: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ke nuna cewa, idan mai wasa ta yi ɗayalwa zuwa gomalwa sau uku to ta fita.

‘Yar Randa Ɗaya: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ke nuna cewa, idan mai wasa ta yi ɗayalwa zuwa gomalwa sau ɗaya to ta fita.

‘Yar Sarki 1: (A cikin wasar ‘Yar Sarki 1) Wasan yara maza da mata inda ake amfani da tsarin shugabanci na Sarki da Ɓarawo da kuma Ɗansanda.

‘Yar Sharel: (A cikin wasar Robali) Nau’in wasan robali wanda ake zana da’ira sannan yara su zuba robali ciki. Za a riƙa duka da takalmi, duk wanda yayin duk kansa robali ɗaya ko sama da haka suka keɓanta daga jikin saura, zai ɗauke su (A cikin wasar waɗanda suka keɓanta)

‘Yar Tafiya: (A cikin wasar Bena) Dutse ko tsingaro ko fashasshiyar kwalba da ake jefawa zuwa ɗaya daga cikin gidaje yayin tafiya.

‘Yar Taru: (A cikin wasar Robali) Nau’in wasan robali wadda ake zana gidajen dara sannan a musu lambobi. Duk gidan darar da mutum ya jefa robali, za a ba shi yawan adadin lambar da ke jikin gidan.

‘Yar Taɓawa: (A cikin wasar Tserel) Yayin da dokar tserel ‘yar taɓawa ce kawai, masu gudu za su tsaya da zarar sun kai ga taɓa abin da ake buƙata a taɓa. Wato dai ba sai sun komo da gudu ba.

‘Yar Tsana: (A cikin wasar ‘Yar Tsana) Wasan da yara ƙanana ke gudarwa da ya ƙunshi kwaikwayon rayuwar yau da gobe na tsarin zamantakewa. Mata sun fi gudanar da wasar, amma wani lokaci akan samu cuɗanyar su da maza yayin gudanar da ita.

‘Yar Turel: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da  ta ba wa mai wasa damar ɗaukar ɗa ba kafin tura sauran ‘ya’ya rami. A maimakon haka, mai wasa za ta tura ‘ya’yan ne rami sannan ta bar adadin wadda ya dace ta bari a waje.

‘Yar Wasa: (A cikin wasar ‘Yar Ɗille) Ƙwayar tsakuwa da ake ɗillawa zuwa cikin rami.

‘Yar Wasa: (A cikin wasar Ɗura-Ɗura) Ɗaya daga cikin duwatsu ko wani abu mai kama da wannan da mai wasa ke amfani da su lokacin wasan.

‘Yar Ɗaukel: (A cikin wasar ‘Yar Ramel) Dokar wasa da ta ba da dama ga mai wasa ya ɗauke ‘ya’ya daidai da yin sa kafin ya mayar da saura rami.

‘Yar Ɗille: (A cikin wasar ‘Yar Ɗille) Wasan yara maza na zaune, inda suke zana babban gidan dara sannan su raba tsakiyarsa biyu. A tsakiyar za a toni wani ƙaramin rami. Masu wasa za su zauna gefe-da-gefe. Sannan za su riƙa ɗilla‘yar wasa daga layin da ke gabansu zuwa cikinwannan rami.

‘Yar Zubel: (A cikin wasar Babunna) Idan wasa ‘yar zubel ce, wacce aka ƙwace a arbana ko wata gaɓa ta wan tu fayif to sai ta sako daga farko idan yin ta ya sake zuwa, wato ta sako daga babunna.

‘Yar Zuwa Da Dawowa: (A cikin wasar Tserel) Idan dokar wasa ‘yar zuwa da dawowa ce, masu tserel sai sun dawo wurin da suka fara gudu bayan sun kai wani wuri da aka ƙayyade. Wato wanda ya je wurin da ake buƙatar a je, zai kuma sake komowa da gudu. Duk wanda ya riga dawowa shi ya yi nasara.

Za Ni Za Ni Ye: (A cikin wasar Za Ni Za Ni Ye) Wasan yara maza da mata da ke da zubi da tsari irin na wasan Lakkuma-Lakkuma Lale. Abin da ya bambanta su shi ne waƙar da ke cikin kowacce.

Zabo: (A cikin wasar Ga Zabo Zai Mutu) Wanda aka sanya wa rigar da ta fi ƙarfinsa a yayin tashe. Shi ke kwanciya a matsayin zabon da zai mutu.

Zan-Zan: (A cikin wasar Wur-Wur) Kalma ce da ake amfani da ita wurin bayyana cewa, wur-wur tana wainuwa yadda ya kamata ba tare da rawa ba.

Zaƙi: (A cikin wasar gori/koɗi) Ku ce mini na ci kusa?

kalma da ke nuna gori tana da kyau, kuma takan daɗe ba ta kwanta ba yayin da aka kaɗa ta. Misali:Gorin na da ~.

Zaɓe: A wasanni da dama ana zaɓe. Wannan wani yanayi ne da ƙwararrun ‘yan wasa biyu ko sama da haka za su keɓe. Daga nan za su riƙa kiran ‘yan wasa ɗaɗ ɗaya. Wato idan na farko ya kira ɗan wasa ɗaya, sai na biyu ya kira wani. A haka har su kira ‘yan wasan gaba ɗaya. Wato dai an raba ‘yan wasa zuwa gida-gida ta hanyar kira ɗaya bayan ɗaya. Waɗanda suka yi kira sukan kasance shugabannin gida.

Zilliya: (A cikin wasar langa) sulluɓewa da kaucewa ciki hikima da ruwa ke yi wa bokan karawa. Misali: Har Adamu ya kai hannu zai tsinka lakon ruwa sai ta ~.

Zubawa: (A cikin wasar girjim) Jera ‘ya’ya a layi biyu na farko da ke gaban mai wasa domin a fara wasa.

Zubawa: (A cikin wasar Guro) Sanya ‘ya’ya uku-uku a gidaje domin a fara tafiya.

Zubel: (A cikin wasar langa): yayin da ruwa ta mutu tare da ɗan wasan ƙarshe da ke gidan abokan karawarsa. Misali: A sake wannan wasa domin an yi ~.

Zubi: (A cikin wasar Guro) Dubi zubawa.

Zuciyar Mai Tsumma: (A cikin wasar Zuciyar Mai Tsumma) Wasan tashe na yara maza da mata da ke hannunka-mai-sanda game da ɗinka wa yara kayan salla.

Zule: (A cikin wasar Zule-Zuleyya) Wanda ke fitowa a matsayin dabbar da ta gagari sauran namun daji a cikin wasan.

Zule-Zuleyya: (A cikin wasar Zule-Zuleyya) Wasan tashe na yara maza inda ɗaya daga ciki da ake kira zule ke shigar ban tsoro tamkar dabbar daji. Wasan yana tafiya da waƙar da ke nuna zule dabba ce da ta gagari sauran dabbobin dawa gaba ɗaya.

 

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Post a Comment

0 Comments