iv) Rashin Yarda: Wannan ma na daya daga cikin dalilan da suke janwo kishi, lokacin da mace ta tabbatar cewa maigidanda baida zarafin da zai ƙara mata kishiya ba za ta damu ba ko kadan, ko da kuwa a makarantar mata yake koyarwa inda za a sami kyawawan mata, zarata, farare masu iya magana da takwarkwasa, amma da wahala ka ga ta damu. Daga lokacin da shakku suka fara samun mazauna a zuciyarta nan take za ta fara nunawa a fuskarta ko lafazinta ko a ayyukanta.
Sai kuma saƙar
zuci: Inda za ta fara cewa "Zai iya samun wace ta fi ni haske" in mai
tunani ce sai ka ga ta fara gyara kanta, irin su dilkannan ba tare da ta furta
masa ko kalma ba, ba ma za ta zarge shi ba kar a yi na 'yan uwan annabi Yusuf
AS da babansu AS. Ba su san kyarkeci na cin mutum ba, amma tunda ya ce yana
tsoron kar kyarkeci ya cinye shi, sai suka ce "Ai kyarkecin ya cinye
shi" mace mai kishin gaskiya ba za ta yi masa maganar kishiya ba bare
shedan ya rada masa a kunne.
Tunda
makaranta yake wurin masu ilimi, in ta ga yana sha'awar mai ilimi nan take za
ta fara nemansa kan jiki kan ƙarfi. Amma in aka ce babu yarda to dole kishi ya
yi ƙarfi a tsakanin masoya ko kuma ma'aurata. Sai ka ga kowa ya fara shakkun
cewa wani abu zai iya faruwa. Me ke sa mace ta fara yi wa maigidanta maƙe don
jin maganar da yake yi a waya? Duk mai irin wannan dabi'ar gani take ko
maigidanta yana neman wata ne, anan rashin yarda ya ratso tsakiya. Duk da cewa
halas ne ya ƙara hana shi ba huruminta ba ne.
Wata macen
wayarsa za ta dauka kacokan ta fara duba history dinsa ko zavta ga ya buga wa
sunan mata, ko kuma wata macen ta bugo masa. Wata da ƙarfin hali ma za ta dauki
lambar ta kira in ta ji budurwa ta amsa ta zazzage ta kuma ta ce ta rabu mata
da miji. Akwai aurarrakin da suka mutu da dama a kan daukar wayar miji. Wani ko
maigidan ya garƙama wa wayarsa kwado sai ta san yadda ake budewa ta kallo wa
kanta hawan jini ko ta yanki tikitin da zai kai ta gidansu.
Idan aka sami
rashin yarda shi ne za ka ga mace na saka wa a riƙa bibiyar mijinta me yake yi?
In tsayuwa ya yi da wata mace sai an zo an gaya mata, wata kan yi abin kunya ma
daga baya ta fara neman yadda za ta gyaro. Kar ki taba yarda ki sa maigidanki a
gaba kina bibiyarsa da sunan kishi. ko da wasu ne suka kawo miki gulmar sun gan
shi wuri kaza da wance, ki nuna musu kin sani, ko da kuwa za ki bibiyi maganar.
Domin a lokacin in suka gaya miki sun wuce kenan, wata ma ba za ta sake tunawa
ba, sun barki da zullumi sun wuce.
Akwai wace
take bin mijin sau da ƙafa, don ganin ina zai je? Da wa zai yi magana? A ƙarshe
ta same shi yana magana da ƙanwarsa da suke dan-mace da 'yar namiji. Ta zaci
budurwarsa ce ta yi mata zagin fitar arziƙi. Wannan ya sa ya fara nemanta don
dai kawai su baƙanta mata rai, a ƙarshe wasa ta zama gaskiya ya auro ta ma gaba
daya.
Kuskure ne
namiji ya sanya rashin yarda ya sami wurin zama a zuciyarsa, duk da cewa kishin
namiji ibada ne domin shari'a ne, amma rashin yardar da zai kai shi ga zargi
zai iya wargaza gidansa cikin dan ƙanƙanin lokaci. An yi wani namijin da in
matarsa ta fita unguwa ko bai bi ta a baya ba sai ya je inda ta je don
bincikawa: Ta zonan? Yaushe? Me ta yi? Daganan ina ta ce za ta? Ba wai ya taba
kamata ne da rashin gaskiya ba a'a tsabar rashin amincewa ne da abin da za ta iya yi.
Wani ko abu
matarsa ta je sayowa sai ya bi diddigi don jin wace magana ta yi da mai shagon?
Na ji wani malami da yake cewa "In matarka za ta je awo a asibiti ka bi ta
kar a yi maka sakiyar da ba ruwa" ba cewa nake kar ka bi ta ba amma ka dauki
lamarin sese-sese yadda ba zai gallabe ka ba. Na san mutumin da in matarsa za
ta unguwa sai dai ya kama mashina guda biyu ya goya ta a baya, su kuma
direbobin su goyo kawunansu. In ya kai ta inda za ta sauka masu mashina su
karbi abinsu. Wannan ba rashin yarda da matarsa ne ba shari'a ce amma Allah ya
sa mu dace.
Ka tsare
matarka iya iyawarka amma kar ka yarda ta ji cewa akwai rashin yarda a
tsakaninku, haka ita ma macen. Babu laifi a tsakaninsu su so juna irin yadda
kowa zai ji dadin dan uwansa ya amince cewa yana son sa. Ba kuma yadda mutum
zai ji cewa zaman ya ishe shi a rabu kawai ba. Ko hotunan mata mace ta ga
mijinta da su ta bi a hankali wajen warware matsalarta, mummunan kishi bai taba
zama hanyar nuna soyayya ba.
Anan Zan
Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba.
**************************
Daga: ✍ Baban Manar Alƙasim
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.