Ticker

Kishi Rahama Ne Ko Azaba //06

MATSALOLIN KISHI

Kusan wannan babin shi ya fi kowanne muni a wannan littafin, domin mummunan kishi na da cutarwa sosan gaske, wanda yakan kai mace cikin matsaloli ita da kanta kafin ma ya shafi wani, yakan jefa ta cin damuwa da zullumi a kowani lokaci, da ma zai bar ta haka to da da sauƙi, amma yakan bi ta cikin gidanta ya ba ta alaƙarta da kowa ba ma maigidan da zai riƙa kallonta a matsayin mai son kai ba hatta 'ya'yanta wani lokaci za su riƙa magana a gefe cewa mama kaza-kaza. Wani sa'in ya kamata a ce da ita za a yi wani abin, ko da ita za a tafi wani wurin, amma dole a boye mata sabida sanin halinta.

Don da a ce mace mai mummunan kishi ta san matsalolin da cutarta ke haifar mata da ita da kanta za ta fara neman magani kafin wasu su ba ta shawarar hakan. ko da yake wasu lokutan takan sani, kuma da kanta ma takan ce "Ni fa mace ce mai zafin kishi" kuma takan ga wasu matan ba haka suke ba me ya sa ta zama daban? Da kanta ta ga yadda kishin kan sa ta yi asarar abubuwa da dama, ciki har da  abin da take kishin a dalilinsa to meye amfanin badi ba rai, misali kwanannan wata ta kusa kashe dan kishiya a ƙarshe mijin ya kasa haƙurin zama da ita, tana ji tana gani ta bar nata 'ya'yan a hannun wancan maigaida ya kore ta.

1) KUSAKURAI: A dalilin  abin da mata ke kira kuskure wata kan yi  abin da zai yi ta damunta har ƙarshen rayuwarta. Don mace mai kishi ba ta girma, ayyukanta na yara ne har ƙarshen rayuwarta, amfanin girma aiki da hankali ko ilimi, ko tana aiki da su a wasu abubuwan indai za a dawo maganar kishi an gama. Mai ilimi kan manta da karatun gefe guda, babbar kuma kan koma daidai da yaranta ta yi duk  abin da ta ga dama a gabansu har su yi fatar da ma ba ta a wurin, tunda hankali bai aiki a wurin ba bare ilimi.

Mai mummunan kishi ko mafarki take wai mijinta ya yi aure sai ta farka cikin salati, in wata ƙawarta da kuskure ta shiga gonanta tana iya mantawa da komai ta sauke mata fushinta gaba daya. Na sha ganin mai batawa da ƙawayenta da suka fi kowa kusa a kan  abin da ba ta ma da tabbas, alabashi daga baya ta ba da haƙuri ko a zo a yi musu sulhu, wata har abada ba ta yin nadama kan  abin da ta yi, matuƙar yana da alaƙa da  abin da take wa kishi. Tun muna yara nake ganin ƙawaye na dambe a kan namiji, kuma kishin ne dalili, a ƙarshe ka taras bai ma san suna yi ba.

Akan sami lokacin da mace za ta sha kuka a yi ta ba ta baki ta ƙi, don dai kawai ta kai ga cimma burinta, kuma a shirye take ta yi zage-zage da cin mutunci a gaban kowa da kuma kowaye, ciki har da mahaifanta bare surukanta, ba ta damu da  abin da za a ce a kanta ba matuƙar za ta kai ga cimma burinta. Wata kuwa zargin mijin za ta yi da wasu ƙarairayi marasa kan-gado, ko kwanannan da wata ta baro gidan mijin ta ce yana neme-nemen mata ne, alhali an san shi da kamun kai kuma malami ne ma, ko ta ina ta sami labaran oho.

Akwai wace in ta tashi haukan kishinta gani take kowa a kan kuskure yake, ita ce kadai a kan gaskiya, don haka take daga murya a lokacin da za ta yi magana don kowa ya ji tunda da shi take, ta riƙa fadin an yi mata kaza-kaza da kaza don an ga ba wanda zai taimake ta, kullum a ce ita ce ba ta da gaskiya. Waɗanda suka so shiga maganar sukan yi iya bakin ƙoƙarinsu wajen gano masabbabin rigimar amma ba sa iyawa, asalin matsalar kishi ne kawai na banza ba a kan  abin da take magana ne ba.

Abinda zai ba ka haushi ko mamaki shi ne wace za ta yi kishi, kuma a zahiri tana cutar da maigidan ne wai hakan wata alama ce da za ta nuna tsabar ƙaunar da take masa, har ka ji tana cewa "Ai duk macen da take kishinka wallahi ƙaunarka take!" A lissafinta duk wace ba ta goyi bayanta a kan  abin da take kai ba to munafuka ce, in budurwa ce to akwai alamar zargi tare da ita, ƙila tana da wata alaƙar tsakaninta da maigidanta. Kenan mummunan kishi ya zama ma'auni da za a iya auna ƙaunar mace ga maigidanta.

A duk abubuwan da mace ke yi ita ba za ta taba sanin cewa tana rushe ginin soyayyarta ne da mijinta ba, ba za ta san ko 'ya'yanta na yi mata kallon maras gaskiya ne ba kuma a ƙarshe  abin da ba ta so din shi yake faruwa. I mana, an yi wace ta kwana da wuƙa ita da mijin a hannu kuma sai da ya yi aurensa. Wata ta je gidan wata yarinya sun sha dambe duk da haka sai da yarintar ta shigo. Akwai wace ta zagi uban surukinta, maigidan ya sallame ta kuma ya yi aurensa, nan gaba ba za ta auri wanda bai taba aure ba to ita ya za a yi kenan ta auri mai mata?

Da haka za ka ga wata da mijinta malami ne mai kamun kai, tana zuba wa wata zagi wai ta yi shigar banza, ko ba ta yarda da kwalliyar da take yi ba ai maigidanta na aiki a wurin in ya ganta fa? Ko ta fara zargin cewa wallahi duk kwalliyar da take yi don maigidanta take yi, ko ka dauka da wasa a ƙarshe za ka ga ne tabbas da gaske take yi ba wata alama dake nuna wasa ne, ba kuma za ta saka a zuciyarta cewa ya kamata ta kwaikwayi  abin da take ganin maigidanta zai yi sha'awa ba.

Anan Zan Dakata Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba

**************************
Daga:  Baban Manar Alƙasim
**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin rubuce-rubuce da ke cike da faɗakarwa da ilimantarwa, waɗanda ake samarwa daga Zauren Markazus Sunnah. Ku bibiye su a kafafensu na sada zumunta domin samun ƙarin bayani. Amsoshi ba ta da haƙƙin mallakar waɗannan rubuce-rubuce, amma tana ɗora su ne da izinin Baban Manar Alƙasim.

Kishi Rahama Ne Ko Azaba

Post a Comment

0 Comments