Ticker

Marigayi Mai girma Sarkin Sudan na Wurno, Alhaji Shehu Malami tare da surunkinsa Marigayi Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Ɗanbaba

 

Marigayi Mai girma Sarkin Sudan na Wurno, Alhaji Shehu Malami tare da surunkinsa Marigayi Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Ɗanbaba
"Ba a gwada maku halin da can, Shehu ba a gwada maku zamani" inji Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun a cikin Waƙarsa mai amshi 'Ba da kai aka wargi ba, ginshiƙin Marafa abag gasa da kai' wacce ya yi wa Marigayi Sarkin Sudan na Wurno Alhaji Shehu Malami. Na farko daga gefen dama, Marigayi Mai girma Sarkin Sudan na Wurno, Alhaji Shehu Malami tare da surunkinsa Marigayi Marafan Sakkwato, Alhaji Ahmadu Ɗanbaba yayin da suke gabatar da addu'a a Hubbaren Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi dake Wurno, Jihar Sakkwato a wani lokaci da ya shuɗe. Allah ya jiƙan magabatanmu ya sa mu wanye lafiya mu cika da kyau da imani, amin.

Daga
Muryar Adabi

Post a Comment

0 Comments