Shin Mai Juna-Biyu Za Ta Iya Yin Sallah A Zaune?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum, malam Allah ya kara fahimta, tambayata ita ce ina da juna biyu ne to kuma kullum ba na jin daɗi, idan na tashi zan yi sallah sai ina jin jiri kamar zan faɗi, to malam duk lokacin da nake jin hakan zan iya yin sallah a zaune?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, ‘yar uwa yin sallah a tsaye rukuni ne daga cikin rukunnan sallah, wanda ingancin sallah ba ya kammaluwa sai da shi. Wajibi ne ga mutumin da ke da ikon yin sallah a tsaye ya yi ta a tsayen, idan ko ya yi ta a zaune alhali yana da ikon yi a tsaye, to sallarsa ba ta inganta ba da ijma'in malamai.

Amma wanda ke da lallura na rashin lafiya ko gajiyawar da ba zai yiwu masa ya yi sallah a tsaye ba, to ya halasta ya yi ta a zaune gwargwadon yadda zai iya, saboda ya tabbata daga Sahabi Imrana ɗan Husaini ya tambayi Manzon Allah ﷺ game da sallah, saboda yana fama da cutar basir, sai Manzon Allah ﷺ ya ce masa: "Ka yi sallah a tsaye, idan ba za ka iya ba sai ka yi a zaune, idan ba za ka iya ba ka yi a ɓarin jikinka". Bukhariy (1117).

Wannan hadisin ya nuna halascin yin sallah a zaune ga mutumin da tsayuwa ba zai yiwu masa ba a sallah saboda wata lallura da yake fama da ita, sai hakan ya halasta wa mai juna biyun da take fama da jiri yin sallah a zaune a lokacin da take sallah ta ga ba zai yiwu mata cigaba a haka ba. Amma duk mai juna biyun da ta yi sallah a zaune alhali tana da ikon yi a tsaye, to sallarta ba ta yi ba sai ta sake.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments