Shimfiɗa: Waƙenga an kurum, ba an yi don nufin daɗi ba,
A sanya hankula a kai ga mannufa don riba,
Ba sautin kiɗi ko raujin amon ALA ba,
A san abin nufi tsamin ruwa fa ba banza ba.
Amshi: Kawalwalniya ta aure idon dubana,
Allah Ubangiji ka zamma mi jagorana.
Ranar Litinin ranar ta Balantayin ne,
Ranar sha huɗu ga wata na Fabrairu ne,
Rana ta masoyan duk duniya mu yi aune,
Wannan Litinin Kaduna ta riske ni ne.
Na baro masauƙi domin nufin shan iska,
Da ni da Mu’azu da Abubakar ɗan barka,
Ɗanladin Abubakar da L. Mu’azu na shan iska,
Mun je Gamji Gate mata da maza na harka.
Dama da hagu duk inda ka duba haka,
Mata da maza sun shassha adon san barka,
Wasu sun ci ado abin sha’awa ɗas haka,
Wasu ko ado su kai da tsiraici haka.
Gefen La’asar iska na kaɗawa haka,
Sannan ga furanni da bishiyoyin barka,
Can ga ƙorama na ambaliya ɗan iska,
Ga mata da maza na rishi da jin kai haka.
Wai abin tambaya ya ALA yake war haka,
Mai ji na ya ce nishaɗi yake shan iska,
Haƙiƙa haka ya kyautu a ce shan iska,
Amma zuciya kawalwainiya na saka.
Cikin zuciya na ci da wuta ta gyara,
Tanyo nake so Allah Ubangiji tabara,
Labari a zuci babu kunnuwan saurara,
Ina da kunnuwa ina da hankula dan lura?
Tufkawa nake saƙawa nake in wara,
Zanawa nake gogewa nake nai shara,
Saduda nake don babu tsumi dabbara,
Face kaliƙi mai iko da saukar mudira.
Ciwo a zuciya in na ranƙwafa yaƙ ƙaru,
In na yi birkice ko nai rigingine yaƙ ƙaru,
Kullum ina nufin Allahu wahidun sattaru,
Ka taimaka mini ka yaye mini Jabbaru.
Ga abin gani amma ba idon kowa ba,
Aiki na hankali amma ba na kan kowa ba,
Aiki da ilimi amma ba sanin kowa ba,
Aiki da fikkira ba fikkira ta kan kowa ba.
Ga garin zuwa jirgi ba zai iya kai gun ba,
Ga abin faɗi baki ba zai iya furuci ba,
Ga abin faɗi kalma ba sa iya zane ba,
Ga abin a ji kunne ba za ya sauraro ba.
Ga abin a ji kunne ba zai yi sauraro ba,
Ga abin faɗi kalma ba sa yi zane nan ba,
Ga abin faɗi baki ba zai iya furuci ba,
Ga garin zuwa jirgi ba zai iya kai gun ba.
Allah Ubangiji kai ne ka san karatun kurma,
Ƙwarin cikin ruwa da sararin sama har su ma,
Hasken da kaz izo ya rarrabe mana da dama,
Muna rabe kala dan dole ne muna gode ma.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.