2.1 Yadda Bara Yake A Ƙasar Hausa

     Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    2.1 Yadda Bara Yake A Ƙasar Hausa

    Bara a ƙasar Hausaa ya kasu kashi biyu; na farko shi ne wanda almajirai suke yi (wato yara ƙanana tsakanin shekara shida zuwa tara) waɗanda wasu iyaye kan ɗauke su, su kai su wani wuri don su yi karatun allo, su sami ilimin addinin Musulunci. Wannan nau’in bara ana yin sa ne na wani ɗan lokaci ba na har abada[1] ba, don da zaran sun girma suna dainawa su kama wasu harkokin neman abincinsu kamar sauran jama’a ta hanyar yin ‘yan sana’o’i kamar tallar rakke ko ƙwadago ko dako ko kuma tallace-tallacen mata ko yankan farce ko wankin takalma da sauransu. Wasu daga cikinsu kan riƙe wannan hanyar kawai su nemi ilmi su tara har su zama malamai, su riƙa koyar da wasu. Waɗansu iyaye sukan ɗauki nauyin abinci ko suturar ‘ya’yansu amma saboda sha’awar sauran abokansu da ba su da wannan gata[2] sai su ma su riƙa fita baran.

    Kashi na biyu na bara shi ne wanda manyan mutane waɗanda suka samu kansu cikin wani hali da ya kamata su nemi taimako daga jama’a don su fita cikin ƙuncin rayuwar ko don su sami sauƙinsa. Masu irin wannan nau’i na bara su ne kutare da makafi da guragu da masu mutuwar zuci. Waɗanda ke aiwatar da irin wannan nau’i na bara kan riƙe shi a matsayin sana’a ta har abada, wato sai mutuwa, babu wani lokaci da za su bar yin baran. Sai dai a kula, ba kowane kuturu ko makaho ko gurgu ke bara ba sai wanda ya sa kansa.

    Haka kuma a cikin wannan kaso akwai mutanen da kan shiga wata matsala kamar ta yankewar guzuri ko faɗawa wata ƙaddara ta rashin lafiya babu abin zuwa asibiti ko faɗuwar gini ko gobara ko ambaliya ko dai duk wata ƙaddara da ke iya faɗa wa wani ta sa shi cikin halin ƙaƙa-nika yi da sauransu. Su ma irin waɗannan da zarar sun sami biyan buƙatarsu sai su bar baran da niyyar wata rana su ma su taimaka wa wani mai irin wannan matsalar. Daga cikin irin waɗannan ana samun bar-gurbi waɗanda duk abin da suka faɗi da ƙarya suka faɗe shi don a riƙa tara masu kuɗi suna kwashewa. Wannan su ne irin nau’in mabarata da ake samu a ƙasar Hausa. To amma yaya aka fara baran har ya kai matsayin da yake a yau? Akwai wasu matakai da shi kansa baran ya bi kafin ya zama yadda yake a halin yanzu, saboda canje-cajen da ke faruwa na zamani da sauran wasu dalilai kamar yadda za a gani a nan gaba.



    [1]  Har zuwa ƙarshen rayuwa.

    [2]  Maga’isa/mai ɗaukar ɗawainiyar wani


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.