2.1.2 Belbela-Belbela - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 69)

    Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

    2.1.2 Belbela-Belbela 

    Wannan ma wasa nna dandali da yara maza ke aiwatarwa a lokacin hasken farin wata. Kimanin yara takwas zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Wasan na tafiya da waƙa, sannan yana buƙatar kayan wasa yayin gudanar da shi.

    2.1.2.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Wannan wasa nna dandali.

    ii. An fi aiwatar da wasada dare, musamman lokacin hasken farin wata.

    2.1.2.2 Kayan Wasa

    i. Riga da aka nannaɗe domin dukan wanda ya faɗi.

    ii. Wurin sha.

    2.1.2.3 Yadda Ake Wasa

    Yara sukan tsaya ba bisa wani tsari ba, wato kara zube. Daga nan kuma sai jagora ya shiga gaba. Jagora zai riƙrera waƙa yayin da saura kuma ke amsawa:

    Jagora: Belbela-belbela,

    ‘Yan Wasa: Jalingo.

     

    Jagora: Ina za ki je ki?

    ‘Yan Wasa: Jalingo.

     

    Jagora: Gidan Audu rimi.

    ‘Yan Wasa: Jalingo.

     

    Jagora: Da ceɗiya da rimi,

    ‘Yan Wasa: Jalingo.


    Jagora: Ala jiƙan maza sun faɗi ragwas!

    Da zarar an kai wannan gaci, kowa zai ƙame a yadda yake ba tare da motsi ba. Duk wanda ya motsa to ya faɗi, don haka za a hau shi da bugu har sai ya sha.

    2.1.2.4 Tsokaci

    Wannan wasa na koyar da yara abubuwa da dama ta taimakon waƙar da ke cikinsa. Da farko dai yana koyar da tsarin shugabanci sannan da bin doka da ƙa’ida. Ɗan wasa bai isa ya yi magana ba tare da shugaba ya yi ba, ko kuma ba tare da lokacin da ya dace ya yi magana ya yi ba. Sannan wanda ya karya ƙa’idar wannan wasa (ƙamewa) zai fuskanci hukunci. Waƙar wasan na ɗauke da sunayen wasu bishiyoyi da ake samu a muhallin Bahaushe, wato ceɗiya da kuma rimi.

    WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.