Fara Bara

    Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa 

    2.2 Fara Bara

    Bara ya fara samuwa a ƙasar Hausa tun lokaci mai tsawo kafin zuwan Musulunci, saboda camfe-camfe da nau’ukan bauta da ke akwai a tsakanin al’ummar Hausawa. Tun kafin zuwan Musulunci Hausawa suke da camfin cewa idan mutum yana da wata naƙasa wai wani aljani[1] ne yake da shi wanda ya mayar da shi haka nan, kuma kyautata masa, wato ba shi sadaka na iya sa a dace. Wannan shi ya sa kake ganin ba a cika tsangwamar masu naƙasa ba, kuma ana tsawatar yara idan suna yi.

    Wani camfi da ya haifar da bara a tsakanin Hausawa tun kafin zuwan Musulunci shi ne, martaba tagwaye da ɗaukar su masu wata daraja da ƙwahi[2] na idan aka saɓa masu wani abu maras kyau na iya biyowa, don haka kyautata masu kamar wajibi ne (wannan camfi ya ƙara samun karɓuwa ga Hausawa bayan zuwan Musulunci a dalilin Hasan da Husaini jikokin Annabi (SAW). Wannan ya sa duk matar da ta haifi ‘yan biyu sai ta yi bara da su, idan ba haka ba suna iya mutuwa.

    Haka ma akwai camfin cewa mai naƙasa irin ta kuturta ko ta makanta ko shan Inna to sai ya yi bara, domin ta haka ne mutane za su sami albarkar da ke tattare cikinsa kasancewar Hausawa na camfa duk wani mai naƙasa da cewa akwai wata hikimar mahallici a cikinsa. Waɗannan dalilai da suka kawo yin bara a cikin al’ummar Hausawa tun lokaci mai tsawo da ba iya ƙayyadewa su suka sa Fransis (1972) ya ce:

    Abin da ya kawo yin bara a ƙasar Hausa tun kafin kafuwar daular Musulunci shi ne camfe-camfen al’umma na cewa idan mutum yana da wata naƙasa a jikinsa ko wata baiwa daga Allah (S.W.) to lallai sai ya yi bara. Naƙasar ta haɗa da kuturta da makafta. Haka kuma idan mace ce ta sami tawaye to sai ta yi bara da su (Fransis, 1972:14).

    Shigowar Musulunci da irin kyautata zaman tare da yake karantarwa shi ya ƙara kawo wa Bahaushe ya bayar da wani abu na taimako ga wani mutum da sunan sadaka yana mai neman samun ladar yin haka daga Allah gobe Ƙiyama. Kafin Musulunci, duk wani abu da wani ya bayar don neman biyan wata bukatar duniya yake bayar da shi, kuma ga wani abun bauta ake bayar da wannan ko da kuwa mai bara ne wani abu ake ganin yana tare da shi. Musulunci ne ya zo da tsarin bayar da Zakka ga talakawa da sunan sadaka, har ya faɗi mutum takwas waɗanda ake bayar da ita gare su. Allah ya ce:

    “Abin sani kawai, dukiyoyin sadaka na fakirai ne da miskinai da masu aiki a kansu, da waɗanda ake lallashin zukatansu, kuma a cikin fansar wuyoyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da Ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah. Kuma Allah ne masani, mai hikima”(Qur’an 9:60).

    Haka ma Musulunci ne ya zo da kwaɗaitar da mutane ko bayan Zakka su bayar da sadaka ga masu bukata domin samun sakayya daga Allah. Akwai ayoyi da hadisai masu yawa da ke nuna haka. Misali, Allah na cewa:

    “Ya ku waɗanda suka yi imani ku ciyar[3] daga abin da Muka arzurta ku daga gabanin wani yini ya zo babu ciniki a cikinsa, kuma babu abota, kuma babu ceto, kuma kafirai su ne azzalumai” (Qur’an 2:254).

    A wani hadisin kuma na cikin littafin Riyadus Salihina Annabin rahama (SAW) yana cewa:

    Daga Ɗan Umar (Allah ya yarda da shi) ya ce lalle Mazon Allah(SAW) ya ce Muslmi ɗan’uwan Musulmi ne kada ya zalunce shi; duk wanda ya biya wa ɗan’uwansa buƙata to Allah zai biya masa tasa buƙata. (Bukhari da Muslim suka ruwaito)

    Wannan tsari na zamantakewa da Musulunci ya zo da shi tare da shigowar malamai baƙi masu yaɗa addinin Musulunci a ƙasar Hausa da kwaɗayin taimakawa kamar yadda addinin ya umurta, shi ya zaburar da Hausawa ga bayar da sadaka ga irin waɗannan baƙin malamai da ma almajiransu da suke tafe da su. Daga nan sai Hausawa suka riƙa ba irin waɗɗannan malamai ‘ya’yansu domin su sami ilmin addini. Sai malaman suka riƙa yawo da su, su ko suna bara domin neman sadakar abinda za su ci. Wannan ma shi ya sa Bahaushe yake da aƙidar ganin abincin bara albarka gare shi, kuma ma mai neman ilmin da bai yi bara ba ilminsa ba ya amfaninsa, kamar yadda Khalid (2006) ya ruwaito a cikin maƙalarsa yana cewa:

    “Bara wani babban ɓangare ne a cikin almajirci wanda wasu ke ƙarfafa shi da cewa idan ba a yi shi ba to karatun da almajirai suka samu ba zai yi albarka ba (Khalid 2006:6).

    A haka bara ya fara a ƙasar Hausa tun kafin zuwan Musulunci ta hanyar bayar da sadaka ga wasu jama’a da aka camfa da kuma daga baya ga malamai masu yawon yaɗa[4] addinin Musulunci da kuma almajiransu da suke tafe tare da su da kuma waɗanda suka saba bara tun kafin zuwan Musulunci da ma waɗanda daga baya suka shigar da kansu cikin harkar. A haka bara ya ci gaba da wanzuwa har zuwa yau, gwargwadon[5] ƙaruwar yawan jama’a gwargwadon ƙaruwar malaman da almajiransu da sauran mabarata a cikin al’ummar Hausawa.



    [1]  Wata halitta wadda ba a gani.

    [2]  Ƙofi/kwari- idanan suka yi nufin wani abu ya sami wanda ya saɓa masu sai ya faru.

    [3]  Bai wa wani abinci.

    [4]  Bazawa/isarwa.

    [5]  Daidai yawan abu.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.