2.2.5 Ni Mota Nake So - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 78)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

2.2.5 Ni Mota Nake So

Wannan waƙa ana rera ta ne yayain wasannin gaɗa na dandali, musamman da dare lokacin hasken farin wata. Adadin yara mata da ke wannan wasa, za su kai shida zuwa sama da haka.

 

Bayarwa: Ni mota nake so,

Amshi: Yayin mota ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni mashin nake so,

Amshi: Yayin mashin ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni keke nake so,

Amshi: Yayin keke ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni jirgi nake so,

Amshi: Yayin jirgi ya wuce ki da aure.

 

Bayarwa: Ni allura nake so,

Amshi: Je ki gidan Malam Nagajere,

 Ya iya allura talatin,

 Wanda Bature bai iya ba,

 Jish kankana jish kankana.

 Jish kankana jish kankana.

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments