Wasannin Tashe Na Yara Maza - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 80)

    Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

    2.3 Wasannin Tashe Na Yara Maza 

    Tashe dai daɗaɗɗiyar al’ada ce a ƙasar Hausa wadda ta samu tun lokacin da addinin Musulunci ya shigo ƙasar Hausa. Za a iya hasashen lokacin da Bahaushe ya fara tashe ta la’akari da lokacin da ya fara azumi. Domin kuwa a cikin watan azumi ne ake gudanar da tashe. Akan gudanar da shi da dare (a mafiya yawan lokuta) bayan an sha ruwa da zummar a faranta wa waɗanda suka kai azumi rai tare da nishaɗantar da su. A wannan ɓangare na aikin, za a kawo bayanin yadda ake gudanar da wasu wasannin tashe a ƙasar Hausa domin fito da waƙoƙin cikinsu fili. Daga ƙarshe kuma za a kawo wasu waƙoƙin tashen ba tare da bayanin tashen da ke ɗauke da waƙoƙin ba.

    2.3.1 Ba Mu Kuɗinmu

    Wannan wasa ne na tashe wanda yara maza ke gudanarwa. Kimanin mutane biyar ne zuwa sama da haka suke gudanar da shi. Sannan akan yi amfani da kayan wasa yayin gudanar da wannan wasa. Kasancewarsa wasan tashe, an fi yin sa da dare, bayan an sha ruwa.

    2.3.1.1 Kayan Wasa

    i.  Filo/matashin kai

    ii.  Sanduna marasa nauyi sosai ko tsumagu

    2.3.1.2 Yadda Ake Wasa

    Yara za su goya wa ɗaya daga cikinsu filo guda ɗaya ko biyu. Wannan ya danganta da girman filon. Domin buƙata shi ne, yayin da aka doki wannnan yaro, kada ya ji zafin dukan. Kowanne daga cikin sauran yara kuwa zai nemi ƙatuwar tsumagiya, ko ma sanda marar nauyi ya riƙe.

    Yayin da ake wurin wasa, waɗannan yara za su hau dukan wannan da suka goya wa filo. Shi kuwa zai riƙa sanya waƙa, saura na amsawa. Ga yadda waƙar take:

    Bayarwa: Wayyo Allah!

    Amshi: Ba mu kuɗinmu.

     

    Bayarwa: Wanne kuɗinku?

    Amshi: Kuɗinmu na bashi.

     

    Bayarwa: Bashin mene?

    Amshi: Bashin doya?

     

    Bayarwa: Na doyar yaushe?

    Amshi: Na doyar bara.

     

    Bayarwa: Ta nawa kuka ba ni?

    Amshi: Ta dala muka ba ka.

     

    Bayarwa: A ina kuka ba ni?

    Amshi: Ɗakin baba.

     

    Bayarwa: Ina shaidarku?

    Amshi: Mu je gun inna.

    Wannan ɗa na ƙarshe akan faɗe shi ne idan a cikin gida ake wasan. Idan kuwa a dandali ne, wurin maza, yaran kan ce:

    Bayarwa: A ina kuka ba ni?

    Amshi: Ɗakin inna.

     

    Bayarwa: Ina shaidarku,

    Amshi: Mu je gun baba.

    Hikimar hakan shi ne, yayin da aka ce a je wurin inna a cikin gida, za a je wurin da mata ko matan gidan suke tsaye ko zaune ne. A dandali kuwa, idan aka ce mu je gun baba, to za a matsa ne kusa da wurin wanda ake wa tashe. Daga nan kuma sai su ci gaba da waƙar:

    Bayarwa: Wayyo Allah!

    Amshi: Ba mu kuɗinmu.

     

    Bayarwa: Ku tsaya in ba ku,

    Amshi: Sai ka ba mu.

     

    Bayarwa: Ni fa ɗan gata ne,

    Amshi: Ina gatanka?

    Bayarwa: Ga shi ubana?

    Amshi: To ya ba ka ka ba mu.

     

    Bayarwa: Baba ba ni in ba su,

    Amshi: Da dai ya fi.

     

    Bayarwa: Baba za su kashe ni,

    Amshi: Sosai-sosai.

     

    Bayarwa: Baba  na fa jigata,

    Amshi: Sosai-sosai.

     

    Bayarwa: Baba har da gumi fa,

    Amshi: Sosai-sosai.

    2.3.1.3 Tsokaci

    Waƙar wannan wasa na samar da nishaɗi musamman ga masu kallo. Sannan tana nuni ga munin wani ɗabi’a ko hali, wato cin bashi. Wanda wannan hali na kai mutum ga wulaƙanta kamar dai yadda mai cin bashin doyan nan ya wulaƙanta. Baya ga haka, waƙar wasan na tabbatar da kasancewar iyaye gata ga ‘ya’yansu.

    WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.