2.4 Wasannin Tashe Na Yara Mata - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 87)

    Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

    2.4 Wasannin Tashe Na Yara Mata

    Kamar yadda aka ba da taƙaitaccen bayani game da tashe a sama, wannan ɓangare na ɗauke da misalan waƙoƙin tashe na yara mata. An kawo bayanin wasu daga cikin wasannin tashen, ta fuskar yadda ake gudanar da su. Daga nan kuma sai aka ba da misalan wasu waƙoƙin wasannin tashen ba tare da mai da hankali zuwa ga yadda ake gudanar da wasannin tashen ba.

    2.4.1 Kallo Da Ido

    Wannan wasan tashe ne da yara mata ke yin sa. Yana da sigar wasan tashe na maza mai suna Jatau Mai Magani. Wasan sananne ne, don haka waƙar da ake gudanarwa a ciki, da kuma shirin wasan ya bambanta daga wuri zuwa wuri. Sannan masu wasan sukan sauya wasu daga cikin kalaman waƙar, kasancewar tana da tsawo. Kimanin mutane bakwai zuwa sama da haka ne suke gudanar da wannan wasa.

    2.4.1.1 Kayan Wasa

    Garin sabara ko lalle ko kuka ko dai gari makamancin waɗannnan

    i. Ledoji

    ii. Kwanuka ko ƙore

    iii. Layun wasa

    2.4.1.2 Yadda Ake Wasa

    Ɗaya daga cikin ‘yan wasa za ta kasance mai maganin gargajiya. Wannan yarinya ita ce shugabar wasa. Za ta sanya layu a hannunta, ko dai ta ɗora su a cikin tarkacen kayan maganinta. Kayan maganin kuwa bai wuce garin sabara ko na lalle ko kuka, ko dai makamancin waɗannan. Wani lokaci akan ƙuƙƙulla wannan garin magani cikin ledoji, sannan a bar wani gari cikin ƙwarya ƙarama ko wani kwano.

    Yayin da aka shiga gida domin tashe, jagora za ta baje kayan maganinta. Daga nan kuma za ta fara waƙa sauran kuma suna amsawa. Wani lokaci za ta riƙa ba wa abokan wasan nata garin magani a hannu, tamkar mai ba da maganin gaskiya. Waƙar kuwa ita ce:

    Bayarwa: Kallo na ido,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Mata ga garin magani,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Mata ku fito ga magani,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Duk ku fito ga magani,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: A yau ni zan ba ku shi,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: In har ba ku san ni ba,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Ni ce mai magani,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: A nan kin ga na kishiya,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Idan kika karɓi na kishiya,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Baɗi ya war haka,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Kin kore kishiyoyi ɗari,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Nan kin ga na mai gida,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Idan na ba ki na mai gida,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Kullum ba ya ƙi ta taki ba,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Nan kin ga na arziki,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Domin ki kore tsiya.

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: A nan kin ga na haihuwa,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Idan kin karɓi na haihuwa,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Ya war haka in mun je baɗi,

    Amshi: Ɗan gajere.

     

    Bayarwa: Kin haife ‘ya’ya ɗari.

    Amshi: Ɗan gajere.

    Za ta riƙa wannan waƙa tana ƙoƙarin bayar da maganin, kamar dai da gaske abin da take faɗi duka gaskiya ne. Haka za su ci gaba da yi har sai an sallame su.

    2.4.1.3 Tsokaci

    Wannan wasa yana nuni ga wata al’adar Bahaushe, musamman kafin ya karɓi addinin Musulunci. Wato al’adar karɓar magani domin samun biyan wata buƙata. Wannan ya haɗa da mallake miji da kuma korar kishiya.

    WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.