Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.
2.5 Waƙoƙin Raino
Raino na nufin rarrashi ko lallaɓin jariri yayin da yake kuwwa domin ya yi shiru ko kuma domin kada ya yi kuka ko ya ƙosa da yanayin da yake ciki. Za kuma a iya kallon ma’anar raino da “Kulawa da jariri na gaba ɗaya.” Wato lura da al’amura da yanayi ko halin da jariri yake ciki, tare da samar masa da buƙatunsa. A lokutan raino, mai raino na rera wa jariri ko yaro waƙoƙi daban-daban tare da rausaya shi (yi masa rawa). Daga cikin misalan waƙoƙin raino akwai:
Gusau, (2008: 225) ya kawo misalin waƙar raino da aka samar a wajajen shekarar 1952 da ta kasance kamar haka:
2.5.1 Bari Kuka Sa’idu - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 92)
Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.
Yi shiru bari kuka Sa’idu,
Me kake wa kuka Sai’du?
Mai kuɗɗi Sa’idu,
Ku taho ku gane shi,
Ku yo ziyara.
Ɗan yaro ya buwaya,
Ɗan yaro sai dai a bi ka,
Amma ba ka bi su ba.
Ɗan Malammai Sa’idu,
Ɗan Alƙalai Sa’idu,
Gidanku an yi gadon karatu.
Ga kuma kuɗɗi barkatai,
Kuma ga shi kun gaji hanƙuri.
Kai yi shiru ɗan yaro Sa’idu,
Yi shiru bari kuka Sa’idu.
2 Comments
Muhimmanci wakokin raino
ReplyDeleteMuhimmancin wakokin raino
ReplyDeleteENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.