Ticker

3.1 Daka - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 96)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.1 Daka - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - )

 

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

Daka na nufin sanya tsabar hatsi ko wani abu makamancin wanann cikin turmi tare da amfani da taɓarya domin lallasa shi har sai ya koma gari. Bayan hatsi akwai abubuwan da ake dakawa da suka haɗa da kayan miya irin su citta da kanamfari da masoro da barkono da da dai sauransu. Mace ɗaya na iya yin daka, sai dai wani lokaci akan samu mata biyu ko ma sama da haka sun haɗu a turmi guda domin daka. An fi samun irin wannan yanayi a gidajen bukukuwa kamar bukin aure ko na haihuwa da makamantansu.

Da yake daka aiki ne na wahala da ke buƙatar amfani da ƙarfi domin gudanarwa, waƙa na kasancewa tamkar sinadarin ƙara ƙaimi ga masu daka. Wannan ya sanya masu dakan ke rera waƙoƙi daban-daban domin ɗebe kewa da annashuwa da kuma ƙarin kuzari da ƙarfin guiwa dangane da aikin da suke gudanarwa. Irin waɗannan waƙoƙi na ɗauke da zambo da habaici a mafi yawan lokuta.

A ɓangare guda kuma, sukan gwama taɓaren da ke hannayensu cikin salon burgewa da sabo da ƙwarewa, wanda hakan ke samar da sautuka tamkar na kiɗa. Akan kira wannan salo da suna lugude ko mama. Lugude kuwa tamkar gishiri ne ga waƙar da masu daka ke rerawa. Gusau, (2008: 224) ya kawo misalin waƙar daka kamar haka:

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments