3.1.1 Almajirai

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    3.1.1 Almajirai

    Almajirai jam’in kalmar almajiri ce wadda ke nufin Æ™ananan yara da ke tsakanin shekaru shida zuwa sha biyar, waÉ—anda iyayensu ke É—aukar su su kai wajen wani malami da ke zaune wani gari da ba garinsu ba domin su yi karatun allo su sami ilimin addinin Musulunci.

    Ƙamusun Hausa wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, na Jami’ar Bayero, Kano ya bayyana ma’anar almajiri da cewakamar haka:

    1.                  “ Mai neman sani ko É—alibi” 2. “Mai bara”

    Wannan ita ce ma’anar kalmar almajirai da ta dace Æ™warai da manufar wannan aikin, saboda ma’anar ta haÉ—a neman ilmi da bara. Masu neman ilmin addini Musulunci ko da sun girma cikin abin sukan kira kansu da suna almajirai domin waiwaye ga matsayin da aka fito lokacin da ake Æ™anana ana neman ilmin saboda Æ™aÆ™an-da-kai[1]. Wato ke nan mai yin bara domin neman ilmi shi ne Almajiri mai jam’i almajirai.

    Khalid kuwa cewa ya yi

    “Almajiri kalmar Hausa ce da ke nufin É—alibi ko É—an makaranta. An samo kalmar ne daga harshen Larabci ‘al-muhajir’ mai nufin wanda ya yi Æ™aura. A tarihance kalmar asalinta daga waÉ—anda suka yi hijira daga Makka zuwa Madina tare da Manzon Allah (SAW) waÉ—anda aka sani da Muhajirun (É—aya muhajir) Khalid, (2006:3).

    Wannan malamin ma ya nuna ma’anar kalmar almajiri da É—an makaranta wanda ke iya zama É—an makarantar boko ko ta allo, sannan ya kawo tushen da aka samo kalmar. A dalilin tasowar yara daga garuruwansu zuwa wasu domin neman ilmi sai aka kira su da sunan, da yake addinance duk wanda ya bar garinsa zuwa wani saboda wani abu da ya danganci addini mai hijira ne.

    Wannan nau’i na mabarata suna aiwatar da bara ne wani É—an lokaci, wato iya lokacin da yaro yake Æ™arami (tsakanin shekaru 6-15) yana karatun allo. Da zaran sun girma ko da sun ci gaba da karatun za su daina bara, su nemi wata sana’a su riÆ™a yi domin samun abinci. Wasu idan sana’ar da suke yi ta É—auke su sai su yi zamansu wannan gari har iya rai. Wannan kaso na mabarata yana da yawa ainun a cikin yankin Æ™asar Hausa, akwai su lugu-lugu, saÆ™o-saÆ™o na Æ™asar.



    [1]  Wahala

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.