3.1.2 Gardawa

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    3.1.2 Gardawa

    Gardawa ma jam’in kalmar Gardi ce wadda ke nufin É—alibin Ƙur’ani da ya kai wani mataki ga karanta Ƙur’ani. Khalid ya bayyana ma’anar kalmar Gardi kamar haka:

    ÆŠalibin da ya karanci alÆ™ur’ani kuma ya kai matsayin rubuta wasu ayoyinsa a kan allo tare da jagorancin malam ko wani É—alibi na gaba da shi a makarantar, ya cigaba da karatun hadda[1] har zuwa aya ta Æ™arshe a lokacin ya zama gardi” (Khalid 1998: 45).

    Wannan ya nuna Gardawa almajirai ne amma waÉ—anda suka girma har suka fara wuce yawon bara a cikin gidaje kamar yadda almajirai Æ™olaye[2] suke yi, amma sun ci gaba da karatun suna Æ™ara samun ilimi. Baran Gardawa ba kullum ba ne, sai mafi yawa ranakun Jum’a ko cikin azumi ko wata rana ta bukin addini kamar daren salla Æ™arama ko babba. Mafi yawa sun fi dogara ga abinda almajirai suka samo suka kawo masu ko É—an abinda suka samu ga ‘yan sana’o’in da suke yi bayan lokacin amkaranta. Gardawa sukan taimaka wa malamai wajen karantar da sauran almajirai Æ™anana, kuma su sukan yi wasu ayyuka na musamman irin na almajirci waÉ—anda malamai ke yi kamar addu’o’i da rubutun sha tare da dukan ayyukan tsibbu da sauransu.



    [1]  Iya yin karatu a ka ba tare da an duba ba.

    [2]  Masu karatun allo amma ba su sauke Ƙur’ani ba


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.