3.1.3 Naƙasassu

     Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    3.1.3 Naƙasassu

    Naƙasassu su ne wani jinsin mutane da Allah Ya nufa da samun wata tawaya[1] ga halittarsu. Tawayar na iya kasancewa ga hannu ko ƙafa ko wani sashe na jiki ko hankali. Ita kalmar daga Larabci Bahaushe ya aro ta ya yi amfani da ita da ma’anar da take a cikin Larabci, wato kasawa.

    Hukumar lafiya ta duniya ta bayar da ma’anar naƙasa kamar haka:

    A disability is may be generally defined as a condition which my restrict a person mental, sensory, or mobility functions to undertake or perform a task in the same way as a person who does not have a disability. (WHO 2012)

    Fassara:

    “Ana iya bayyana ma’anar Naƙasa da cewa wata tawaya a cikin ayyukan jiki ko kuma wahalhalun da ake samu wajen wani sanannen aikin da mutum kan samu wajen gudanar da hidima ko aiki kamar yadda wani wanda bai da wata tawaye ke yi’.

    Wannan ma’anar ta nuna duk wata tawaya da aka samu a wata gaɓa ta jikin mutm ana kiranta naƙasa, wannan kuwa har da taɓin hankali. Irin waɗannan mabarata akwai manya akwai yara, kuma suna bara ne saboda halin naƙasar da suke da ita. Mabarata da ke cikin wannan kaso sun haɗa da kutare da makafi da guragu da masu mutuwar zuci[2].Wasu daga cikin yaran da ke da naƙasa manya ne lafiyayyu ke bara da su. Waɗannan mabarata ba kamar almajirai suke ba, ba su da wani lokaci na daina bara, suna yi ne har iyakar rai, ba wani lokaci da za su daina yin baran.



    [1]  Raguwa, rashin cikakkiyar halitta.

    [2]  Mutanen da suke lafiya ƙalau, kuma suna iya yin komai da kowa yake yi amma sai su zauna su ƙI yin komai sai jiran wani ya taimaka masu.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.