3.1.4 Masu Lalura


    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    3.1.4 Masu Lalura

    Masu lalura a nan na nufin wasu mutane da a dare É—aya suka tsinci kansu cikin wata matsala wadda ta tilasta su neman taimakon jama’a wani lokaci har abin ya kai su ga yin bara domin samun ficewa daga matsalar da suke ciki. Irin waÉ—annan matsalolin da kan tilasta wasu shiga bara sun haÉ—a da yankewar guzuri ko sata ko gobara ko ambaliya ko harin ta’addanci ko wata rashin lafiyar da babu abin zuwa asibiti ko faÉ—uwar gini da sauransu. Da yawa irin waÉ—annan mabarata da zarar sun sami abin biyan buÆ™atarsu sukan daina baran, domin da ma kafin wannan mutane ne su masu harakar yi, baran ya riske su ba shiri.

    Sai dai a kula da cewa, cikin irin waɗannan mabarata ana samun bar-gurbi waɗanda abin da suke faɗa suna bara da shi duk ƙarya ne[1]. To su irin waɗannan ba su daina bara domin da ma ba abin da suke faɗa ne ya sa su bara ba.



    [1]  Akwai wani irin wannan da aka kama yana bara ya liÆ™a hanjin akuya a cikinsa, ko kuma masu Æ™aryar su matafiya ne guzuri ya yanked a sauransu.  

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.