Carafke

    3.15 Carafke

    Wannan ma wasa ne da yara mata ke yi. Yana kama da ‘yar ramel, domin akan yi amfani da ƙodo. Amma yanayi da dokokin wasan sun sha bamban.

    3.15.1 Wuri Da Lokacin Wasa

    i. Akan yi wasan ‘yar ramel a cikin inuwa a dandali ko a ƙofar gida ko a cikin gida. An fi gudanar da wasan a ƙarƙashin inuwar bishiya, kasancewarsa wasan zaune.

    ii. Ana gudanar da wannan wasa da hantsi ko da yamma. Ba a yin sa da dare.

    6.15.2 Kayan Aiki

    i. Duwatsu ƙanana

    6.15.3 Yadda Ake Wasa

    Masu wasa za su tsino ‘ya’ya adadin da aka ƙayyade, misali goma-goma ko ashirin-ashirin ko makamancin haka. Daga nan sekon za ta yi baji. Wato za ta barbaza ‘ya’yan a ƙasa daidai son ranta. Fes kuwa za ta fara yi. Za ta riƙa jefa ƙodo sama sannan ta riƙa ɗaukar ‘ya’yan da aka yi wa baji. Mai wasa za ta iya ɗaukar adadin‘ya’yan da ta ga dama a lokaci guda.

    Yayin da mai wasa ta zo ɗauka, sai kuma ta girgiza, wato ɗaya daga cikin ‘ya’yan da ke ƙasa ta yi rawa, to kuwa ta faɗi. Daga nan mai yi ta gaba za ta karɓa.

    Bayan an gama tsince duwatsun da aka yi baji da su, sai kowace ‘yar wasa ta ƙirga waɗanda ke hannunta. Daga nan wadda ta samu ya’ya fiye da saura za ta ba da aro ga waɗanda suka samu kaɗan. Haka za a yi har sai kowace ta samu aro yadda yawan ‘ya’yan masu wasa zai koma daidai. Misali idan ‘ya’ya goma-goma kowa ta nemo, to, kowace sai ta kasance tana da ‘ya’ya goma kafin a fara. Wanda ‘ya’yanta ba su kai ba, za ta nemi aro a wurin wadda nata suka zarta. Idan aka sake baji kuma aka kammala, masu bashi za su yi ƙoƙarin biya, in har sun samu yawan ‘ya’ya sama da waɗanda aka yi tsintuwa a farkon wasa.

    Yayin da aka gama cafke kowane baji, to wasa ta ƙare. Wadda ta fi kowa yawan ‘ya’ya za ta dali dukka sauran masu wasa. Daga nan kuma mai bi mata a maki ta dali saura. Wannan na nuna cewa, wadda ta fi kowa bashi ba za ta dali kowa ba.

    6.15.4 Sakamakon Wasa

    Sakamakon carafke shi ne dala. Wadda za a dala za ta haɗa tafukan hannunta. Mai dala kuma za ta ɗauki takalmi ta riƙa dukan bayan hannun da shi. Akan yi dala biyar ko goma ko ashirin ko dai yadda masu wasa suka tsara tun farko.

    6.15.5 Dokokin Wasa

    Dokokin Carafke Sun haɗa da:

    i. Dole ne masu wasa su ɗauko‘ya’ya daidai da na juna yayin tsintowa.

    ii. Yayin da ta yi rawa a lokacin da mai wasa ke cafkel, to mai wasa ta faɗi.

    iii. Sekon ce ke da hurumin yin baji a farkon wasa.

    iv. Wadda ba ta samu ‘ya’yan da suka kai adadin tsintowar farko ba, dole ta amshi bashi kafin a yi baji na gaba. 

    6.15.6 Tsokaci

    Wannan wasa na koyar da nitsuwa da kuma lissafi. Dole ne mai wasa ta kasance a nitse yayin cafkel. Sannan a kowane ƙarshen baji, sai an biya basussukan baya ko kuma a ƙara karɓar bashi.

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.