Ticker

3.2 Daɓe - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 100)

Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

3.2 Daɓe 

A al’adance, manyan mata ne suka fi gudanar da daɓe. Daɓe kuwa hanya ce ta gyara ɗaki (musamman sabon ɗakin amarya) da lailaye shi domin ya yi kyau. Bayan ƙara wa ɗaki kyau, wani amfanin daɓe shi ne rage tone-tone da ɓeraye (kusu) ko wasu ƙwari za su iya yi a cikin ɗakin. Da yake daɓe aikin ƙarfi ne, akwai waƙoƙi iri-iri da mata kan yi domin ɗebe kewa da samar da kuzari ga masu wannan aiki. Misalan waɗannan waƙoƙi sun haɗa da:

WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

Post a Comment

0 Comments