3.2.1 Masu Mulki

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    3.2.1 Masu Mulki

    Masu mulki a nan na nufin masu shugabancin al’umma. DaÉ—aÉ—É—iyar al’adar Bahaushe ce a sami shugaba ga duk wata Æ™ungiyar jama’a da ta wanzu a cikin al’umma, kamar yadda Alhassan (1982) ke cewa:

    Idan gari ko tunga ko ƙauye ya kafu sai a sa shugaba wato Sarki ko Hakimi ko Mai unguwa da sauransu. Alhasan (1982:54).

    Akwai irnin wannan shugabanci daban-daban a cikin al’umma. Misali, akwai sarakuna da uwayen Æ™asa da hakimai da masu unguwanni. Haka kuma, a zamanance akwai manyan ma’aikatan gwamnati da kuma shugabannin siyasa da suke mulkin al’umma. Irin waÉ—annan shugabanni mafi yawa sukan kasance masu wadata. Haka ma ko bayan wadatar da suke da ita, suna da hannu ga wasu abubuwa na tallafi da kan shigo zuwa ga mabuÆ™ata ta wasu hanyoyi kamar tallafin gwamnati ko na wasu Æ™ungiyoyi masu zaman kansu na cikin Æ™asa da na waje.

    Mabarata na yi wa waɗannan shugabanni da aka ambata bara, saboda wadatar da suke da ita da kuma hannu da suke da shi a kan abin da ke shigo ma tallakawa daga wasu kafafe. Koyaushe gidajensu da ofisoshinsu maƙil suke da mabarata iri-iri domin neman taimako daga wajensu. Haka kuma, wannan ba zai hana a tare su ga hanya a yi masu bara a nemi sadaka daga hannunsu ba, saboda ko a waje suka fita suna cikin alama mai nuna mawadata ne, wanda kan ƙara jawo hankalin mabaraci zuwa gare su.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.