3.2.2 Attajirai

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    3.2.2 Attajirai

    Attajirai su ne mutane masu hali waÉ—anda tushen samun wadatarsu ya fi ta’allaÆ™a da kasuwanci da fatauci da noma. Ita kanta kalmar attajiri ararra ce daga Larabci mai nuna ma’anar É—an kasuwa[1]. Kodayake an fi nuna cewa masu wadata daga cikinsu a matsayin attajirai a wannan Æ™asa ta Hausa. Kafin shigowar mulkin Turawa da sauye-sauyen da hakan ya haifar ga Æ™asar Hausa, sarakuna da attajirai su ne kawai mawadata da ma wasu malamai a cikin al’umma. Canjin da aka samu na gudanar da mulki a Æ™asar Hausa shi ya kawo a Æ™idaya ma’aikata da ‘yan siyasa a cikin mawadata, domin ma’aikata da ‘yan siyasa sun koma su ne masu mulki.

    Abin nufi a nan shi ne wannan kaso na masu arziki ne ko kuma a ce mawadata waÉ—anda suka mallaki abubuwan biyan buÆ™atunsu da na iyalinsu da ma na taimaka wa wasu idan suna so. Su ma irin wannan rukunin jama’a mabarata na yi masu bara a kowane lokaci, kuma kowane waje. Ana isko su a shagunansu ko gidajensu ko a kowane waje na gudanar da sana’o’insu a yi masu bara. Sau da yawa ana dacewa su taimaka ko da da abu kaÉ—an ne.



    [1]  Wannan na nuna cewa mutumin da ke lamarin saye da sayarwa shi ake kira attajiri.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.