3.2.3 Talakawa

    Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    3.2.3 Talakawa

    Matalauci a nan na nufin mutum wanda ba ya da wadata, wato wanda abin da yake samu bai wuce bukatarsa ta yau da kullum ba ko da shi basarake ne ko malami ko ma’aikacin gwamnati ko É—an siyasa. Wato dai mutane waÉ—anda ba masu hannu da shuni ba waÉ—anda ba su iya biyan bukatun kansu cikin yalwa saboda rashin abin hannunsu. Da yawa daga cikin waÉ—annan jama’a sun dogara ga ‘yan aikace-aikacen hannu domi neman abin biyan buÆ™atu, kamar abin ci da na sha da sutura da sauran ‘yan Æ™ananan bukatocisu. Talaka mutum ne mai wani matsayi a tsarin zamantakewar Bahaushe wanda kankasance cikin yunÆ™urin zama mawadaci a kowane lokaci. Ƙarancin abin hannun wasu daga cikinsu yakan tsananta su kasance cikin halin Æ™aÆ™a-ni- ka-yi har marasa Æ™arfin zuciya daga cikinsu su rikiÉ—a su koma mabarata. To duk da Æ™aramcin abin da ke hannunsu bai hana mabarata su yi masu bara ba. Su kuma sukan É—iba cikin kaÉ—an É—in nan da suke da shi su ba mabarata sadaka. 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.