4.6.1.2 Mu Tai Bara

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    4.6.1.2 Mu Tai Bara

     Jagora: Mu tai bara don Allah,

     Amshi: Saboda Manzon Allah.

     Jagora: Ku taimaka don Allah,

     Amshi: Saboda Manzon Allah.

     Jagora: Allah sa muje gida dan Allah,

     Amshi: Saboda Manzon Allah.

     Jagora: Allah kare tsautsayi da hasara,

     Amshi: Saboda Manzon Allah.

     Jagora: A bamu domin Allah,

     Amshi: Saboda Manzon Allah.

     

     Ita kuwa wannan waÆ™ar in an lura bara ne tsagwaronsa ba tare da surka waÆ™ar da wani bege ba. Ita ma a cikin taro mabarata ke amfani da ita. A mafi yawan lokuta Æ™ungiyar mabarata da ke amfani da wannan waÆ™ar takan haÉ—a masu naÆ™asa dabam-daban, kamar kutare da makafi da guragu da ma wasu gajiyayyu waÉ—anda ba su da wata naÆ™asa. Ita ma wannan waÆ™ar wani daga cikin mabaratan ke bayarwa saura na amsa masa. Ga kuma wata mai suna Maula ta Sidi:


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.