4.6.2 Waƙar Ɗan Fari - Daga Littafin WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA (Page - 119)

    Citation: Gobir, Y.A. & Sani, A-U. (2021). Waƙoƙin Hausa Na Gargajiya. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-0-01.

    4.6.2 Waƙar Ɗan Fari

    Wannan waƙa tana da tsarin amshi. Wato akan samu mai ba da waƙa, yayin da saura kuma za su riƙa amsawa. Ga yadda take kamar haka:

    Bayarwa    Amshi

    Ɗan fari gilashina,   Kai yi shunka.

    Kai yi shunka,    Kai yi shunka.

    Mai bi mai ruwan mai na,  Kai yi shunka.

    Na uku fari kamar alli,  Kai yi shunka.

    Gilashi ba na mota ba,  Kai yi shunka.

    Ruwan mai ba na tuya ba,  Kai yi shunka.

    Na uku fari kamar taffa,  Kai yi shunka.

    Ba na zuwa da kai rafi,  Kai yi shunka.

    Kada sanyi ya kama ka,  Kai yi shunka.

    Ba na daka da kai goye,  Kai yi shunka.

    Kada rana ta koɗe ka,  Kai yi shunka.

    Ɗan fari ruwan azurfa,  Kai yi shunka.

    Na Amina ‘yar Indo,  Kai yi shunka.

    Za mu ganin gida gobe,  Kai yi shunka.

    Ga lalle a ɗaura ma,   Kai yi shunka.

    Ga man shafi a shafa ma,  Kai yi shunka.

    Za mu mu iske farar kaka,  Kai yi shunka.

    Farar kaka ta sa leshi ta goyaka, Kai yi shunka.

    Ta sa majanyi ta tsuke ka,  Kai yi shunka.

    Ba ni barinka wurin baƙar kaka, Kai yi shunka.

    Ta sa tsumma ta goya ka,  Kai yi shunka.

    Haƙiƙa wannan waƙa ma na ɗauke da yabon jaririn da aka haifa, tare da nuna yadda yake da daraja da yadda ake son sa da kuma yadda za a tarairaye shi. A ciki an yi amfani da sunan mutane wato Amina da Indo. Za a iya hasashen Ibrahim (Mrs) (2000) ta samu ruwayar waƙar ne da waɗannan sunaye, wanda ke nan za a iya samun sauyi yayin da ake rera waƙar a wani wuri daban. Daga ƙarshen waƙar kuma an kawo habaici, inda ake ƙwalelen jariri a baƙar kaka, wadda za ta masa riƙon sakainar kashi. Duk wanda ya yi zagin kasuwa, to ya san da wa yake.

    WAƘOƘIN HAUSA NA GARGAJIYA

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.