4.8.2 Faranta Rai

     Citation: BunguÉ—u, U.H. (2021). Bara da wasu waÆ™oÆ™in bara a Æ™asar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar BunguÉ—u
    (Sarkin Gobir Na BunguÉ—u)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    4.8.2 Faranta Rai

    Mai neman abu daga hannun wani zai yi duba tare da lura da abinda ke faranta ran wanda zai nemi abu daga hannunsa. Mabarata na lura da haka, shi ya sa suke neman waƙoƙi masu ƙunshe da wasu jigogi da suke ganin za su iya faranta wa waɗanda za su yi wa bara su riƙa rera masu su domin samun sadaka daga hannayensu. Misali, kamar begen Annabi, wanda duk Musulmin ƙwarai zai so ya ji ana begensa. Ga misali:

     Jagora: Ya bisimilla Allah,

     Amshi: ÆŠan Amina

     Jagora: Za ni yabon Muhamman

     Amshi: ÆŠan Amina

     Jagora: Mai birnin Madina

     Amshi: ÆŠan Amina

     Jagora: A ba mu domin Allah

     Amshi: ÆŠan Amina

     Jagora: In da rabo da niyya,

     Amshi: ÆŠan Amina

     Jagora: Don Shi ba don mu ba,

     Amshi: ÆŠan Amina

     Jagora: Mai daraja Muhamman,

     Amshi: ÆŠan Amina.

     (ÆŠan Amina)

    Wannan waƙa da ta gabata yabon Annabi ne ƙunshiyarta. Kamar yadda aka faɗa can baya cewa, ɗaya daga cikin dalilan da suke sa mabarata yin amfani da waƙa a wajen bara shi ne faranta wa waɗanda suke yi wa bara. Yabon Annabi na cikin abubuwan da ke faranta wa Musulmi rai. Wannan ya sa da yawa daga cikin waƙoƙin da mabarata ke rerawa a lokacin bara suna ɗauke da yabon Annabi ne, da zimmar saka farin ciki ga zukatan waɗanda suke yi wa bara har su ba su sadaka. Ga wani misali daga rubutattar waƙa.

    1.                     Almiski har kafur ku san duka ba su kai,

     Æ˜amshi na al’udin jiki na Muhammada.

    2.                     Hakanan ga kyawu ko ga zati ba wa shi,

     Don babu ko dukka Kaman na Muhammada.

    3.                     Ba a yo ga tahalikai kama tai nan É—aiÉ—ai,

     Ba za a yi abadan kama tasa, Ahmada.

    4.                     Hakana ga halki masu sha’wa ba wa shi,

     Fara’a da kyawun murmushi na Muhammada.

     (Nana Asma’u: Kirarin Amada)

    WaÉ—annan baitoci da suka gabata yabo ne zuwa ga Annabin rahama Muhammad (SAW). Baitocin suna ambaton daraja da fifiko wanda Annabi yake da shi a kan sauran Annabawa. Haka baitocin sun Æ™unshi mu’ujizojin Annabi da Allah ya keÉ“e shi da su. Ambaton waÉ—annan na shigar da farin ciki ga Musulmi masoya Annabi. Mabarata suna lura da haka Æ™warai, suna aikata ko rera abin da suka san waÉ—anda suke wa bara suna so, domin haka na sa su sami sadakar. Umar (2002) ya ba da irin wannan misali na wani kuturu da ke amfani da tutar NEPU da ta NPC wajen bara. Ya É—aura ta NEPU idan ya je garin da NEPU ta fi yawa, ya kuma É—aura ta NPC idan ya je inda NPC ta fi yawa. Duk wannan domin faranta wa waÉ—anda ake yi wa bara ne. Akwai irin wannan a cikin wata waÆ™ar da mabarata ke amfani da ita wajen bara kamar haka

    6. Ya Ilahil alamina,

     Taimakan ni in je Madina,

     In ji daÉ—i in yi murna,

     In ga Æ™abarin É—an Amina,

     Baban Kulsumu É—an Suwaiba.

     -------------------------------------

    46. Ga mu gun jikanka Shehu,

     Don isar Kakanka Nuhu,

     Rungume mu ka ce madihu,

     Wanda ke da uwa a murhu,

     Ba zai ci tuwonsa ba miya ba.

     (Aliyu Namangi: Imfiraji ta Farko)

    WaÉ—annan baitocin waÆ™ar suna faranta ran duk wani Musulmi a cikin al’ummar Hausawa, a cikinsu ne aka ambaci asalin Manzon Allah (SAW) ta hanyar ambaton iyaye da kakanninsa har ma da garinsa wanda jama’ar Musulmi ke burin su je don su kai ziyara. A lokacin da mabaraci ya rera waÉ—annan baitukan sai masu saurare su ji ransu ya yi daÉ—i har ya É—auki wani abu su bayar sadaka zuwa ga mabaracin.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.