Ƙimar Ilmi/ Ilmantarwa

     Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    4.8.3 Ƙimar Ilmi/ Ilmantarwa.

    Ilmi abu ne mai ƙima ga idon mutane bale ma a ce ilmin addini. Sau da yawa mabarata kan yi amfani da waƙa wani lokaci ma ta Larabci ba tare su kansu sun san ma’anar da ke ƙunshe cikinta ba, haka su ma masu saurare. Da yake masu sauraren sun san waƙar ta ilmi ce sai su riƙa ganin ƙimar mai rera ta. Ganin wannan ƙimar da mabarata suka san mutane na da ita ga ilmi, shi ya sa wani lokaci suke amfani da waƙa wajen bara, domin a dube su da ƙimar ilmi a kuma ba su sadaka. Misali :

    1. Ya arhamar rahamani bani abin nufi,

    Zancen da zan yi kas shi faɗi ga banza.

    2. Kai mai kiran sallah ka san wada zaka yi,

    Ka yi hattara don ba a yi nai banza.

     -----------------------------------------------------

    6. Don na ga ƙattan ƙauye wasa ɗai su kai,

    Sai sun gaza suka fasa kuwwar banza.

     ------------------------------------------------------

    16. Allahu akbar in kiran sallah ka kai,

    Don kak ka ce Ala ka faɗi ga banza.

    17.Wanna alihin ɗamre kablasan shikai,

    Kak ka ce akabar a bar ka ga banza.

    18. Akubar da akabar wanga dud dulginku na,

    Juhala’u kau da ka buɗe baki banza.

     (Maharazu Barmo Kwasare: Waƙar Kiran sallah)

    Wannan waƙa mabarata suna amfani da ita wajen bara tana koyar da ilmin kiran sallah ne, duk wanda ya saurari wannan waƙar yakan ba ta wata ƙima saboda ilmantarwar da take ɗauke da shi. Har saboda hakan sai su riƙa samun sadaka daga masu sauraren baran nasu.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.