5.1 SIGA DA FALSAFAR WAƘOƘIN BARA

 Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

Dr. Haruna Umar Bunguɗu
(Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
Email: harunaumarbungudu@gmail.com
Phone: 08065429369

Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

5.1 SIGA DA FALSAFAR WAƘOƘIN BARA

Kowace waƙa sunanta waƙa, amma kuma sukan bambanta ta wajen abubuwa da dama. Daga cikin abubuwan da ke bambanta waƙoƙi da junansu akwai siga, wato irin tsarin da ake ɗora waƙa a kansa. Wanna babi ya dubi irin sigogin da waƙoƙin bara suke da su waɗanda saura waƙoƙi suka rasa su. Haka ma ko bayan saƙon na sarari da waƙa kan ƙunsa akwai kuma wani darasi da aka iya koya wanda gundarin saƙon waƙar (jigo) bai ambace shi ba. Wannan irin darasi da aka iya fahimta daga waƙoƙin bara ko bayan gundarin jigo,shi ne aka kira falsafar waƙoƙin bara. Wannan babi ya dubi sigogin da waƙoƙin bara suke da su da kuma falsafar da ake samu a cikin waƙoƙin waɗanda suka bambanta da sauran waƙoƙi da ba na bara ba. An kawo bayanin waɗannan tare da misalai daga waƙoƙin bara masu ƙarfafa abin da aka faɗa.


Post a Comment

0 Comments