Ticker

6/recent/ticker-posts

Tababbe

Wannan wasan tashe ne wanda yara maza ke gudanarwa cikin watan azumi. Yawan masu gudanarwar sukan kai misalin biyar ko sama da haka. Ɗaya daga cikinsu zai kasance jagora, wanda kuma shi ne taɓaɓɓe.

 5.1 Taɓaɓɓe

5.1.1 Lokaci Da Wurin Wasa

i. An fi gudanar da wannan wasa da dare, kamar dai sauran wasannin tashe. Amma wasu lokutan akan yi shi da hantsi ko da yamma.

ii. Akan shiga gida-gida domin gudanar da wannan wasan tashe. Sannan sukan yi shi a dandali, wurin da taron jama’a suke. Kamar bakin shaguna ko wurin hutawa da makamantansu.

 

5.1.2 KayanAiki

i. Igiya

ii. Taɓarya ko sanda

iii. Gawayi ko baƙin bayan tukunya

 

5.1.3 Yadda Ake Gudanar da Wasa

Ɗaya daga cikin yaran (Taɓaɓɓe) zai shafe fuskarsa da baƙin tukunya ko gawayi ko dai wani abu makamancin wannan. Fuskar za ta zama gwanin ban tsoro. Daga nan zai nemi taɓarya ko sanda ya saɓa a kafaɗa. Sauran yara kuwa za su ɗaura masa igiya a ƙugu. Haka za su riƙa zuwa gida-gida ko kuma wurin taron maza (idan a dandali ne). Taɓaɓɓe zai riƙa yunƙurin kai wa jama’a bugu, tare da yi musu barazana da zazzare idanuwa. Sauran yara kuwa za su riƙa janyo shi baya ta hanyar amfani da igiyar da suka ɗaura masa a ƙugu. Da zarar sun janyo shi baya, sai kuma ya sake zabura cikin ƙoƙarin kai wa mutanen da ke gabansa farmaki. Sai kuma yaran su sake janyo shi baya. Haka dai za su riƙa yi, taɓaɓɓe yana ba da waƙa sauran yara na amsawa.

 

5.1.4 Waƙar Wasa

Taɓaɓɓe: Ni ne baƙin birin nan da ake faɗi,

Yara: Taɓaɓɓe!

 

Taɓaɓɓe: Ba ga ni ba?

Yara: Taɓaɓɓe!

 

Taɓaɓɓe: A taɓa ni man!

Yara: Taɓaɓɓe!

 

Taɓaɓɓe: In rugurguza!

Yara: Taɓaɓɓe!

 

Taɓaɓɓe: Ba ga ni ba!

Yara: Taɓaɓɓe!

 

Taɓaɓɓe: A taɓa ni man!

Yara: Taɓaɓɓe!

 

Taɓaɓɓe: In bubbuga!

Yara: Taɓaɓɓe!

5.1.5 Tsokaci

Wannan wasa yana ƙunshe da nishaɗi. Sannan yana nuni ga wani hali na taɓaɓɓen mutum, wato mahaukaci.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.

Post a Comment

0 Comments