Ga Zabo Zai Mutu

    5.11 Ga Zabo Zai Mutu

    Wannan ma wasan tashe ne da yara maza ke gudanarwa cikin watan azumi. An fi yin wasan da dare bayan an sha ruwa. Kimanin yara biyar ne suke gudanar da wannan wasa. Sannan kayan aikin da ake buƙata kawai shi ne riga mai girman da ta fi yaron da zai sanya ta.

     

    5.11.1 Yadda Ake Wasa

    Ɗaya daga cikin yara yakan sanya riga babba wanda ta fi ƙarfinsa. Wannan yaro shi ake kira zabo. Yawanci akan zaɓi mai ƙaramin jiki ne a matsayin zabo. Yayin da aka je wurin wasa, zabo zai kwanta ƙasa, ya mayar da hannaye da ƙafafu da kuma kansa cikin rigar da ya sanya. Sai kuma ya fara mutsuttsukuwa. Ɗaya daga cikin sauran yaran kuwa zai riƙa ba da waƙa, ragowar na amsa masa. Ga yadda waƙar take:

    Bayarwa: Kurket-kurket ga zabo zai mutu,

    Amshi: Ga zabo zai mutu.

     

    Bayarwa: Babanmu ko da ɗan hatsi?

    Amshi: Ga zabo zai mutu.

     

    Bayarwa: Innarmu ko da ɗan hatsi?

    Amshi: Ga zabo zai mutu.

     

    Bayarwa: Goggonmu ko da ɗan hatsi?

    Amshi: Ga zabo zai mutu.

     

    Bayarwa: Kakanmu ko da ɗan hatsi?

    Amshi: Ga zabo zai mutu.

     

    Bayarwa: Kawunmu ko da ɗan hatsi?

    Amshi: Ga zabo zai mutu.

     

    Bayarwa: Yayanmu ko da ɗan hatsi?

    Amshi: Ga zabo zai mutu.

     

    5.11.2 Tsokaci

    Wannan wasa yana nuni ga tausaya wa da Bahaushe ke da shi kan dabbobi da tsuntsaye. Sannan yana kundace wasu sunayen dangantaka ta jini da Bahaushe ke amfani da su. Baya ga haka, wasan na samar da nishaɗi. Domin kuwa an gina shi kan raha da ban dariya. Ko ba komai dai, Allah Ya yi babban zabo. To idan ba hatsin a nemo wuƙa kawai …

    WASANNI A ƘASAR HAUSA

    Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.