5.1.1 Sigogin Waƙoƙin Bara

     Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    5.1.1 Sigogin Waƙoƙin Bara

    Siga tana nufin kama, wato wata sifa da ake bambance wani abu ita daga sauran danginsa masu kama da shi. Siga na nufin kama. Wato kamnnin wani da ake iya sanin abun da su waɗanda suka bambanta shi da sauran abubuwa, Bergery (1934).

    A bisa ma’anar da aka samo daga ƙamusun Bergery wanda aka ambata, ana iya cewa, siga na nufin tsari, wato irin tsarin da abu yake da shi wanda ya bambanta shi da sauran abubuwa masu tsari bamban da shi. Sigogin waƙoƙin bara a nan na nufin tsarin da waƙoƙin suke da shi wanda wasu waƙoƙi da ba su ba ba su da su. Yana da kyau a kula da cewa sigogin da ake zance na waƙoƙin bara sun fi dangantaka da waƙoƙin bara na baka, domin su ne tun farko aka tsara domin a yi bara da da su. Rubutattu waɗanda ake bara da da su ba domin bara aka tsara su ba, mabarata ne ke aron su su yi bara da su. Duk da haka, su ma mabarata na ƙara masu wata siga domin ta ɗauki kama irin ta waƙoƙin bara na baka. Ba dukan sigogin waƙoƙin bara na baka ake iya samu a rubutattun da ake bara da su ba. Fitattun sigogin da aka san waƙoƙin bara da su sun haɗa da gajartawa da rawa da amshi na musamman da kuma surkulle.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.