5.1.1.1.2 Gajarta Yawan Ɗiyan A Cikin Waƙa

     Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    5.1.1.1.2 Gajarta Yawan Ɗiyan A Cikin Waƙa

    Wannan yana nufin waƙoƙin bara ba su da tsawo. Wannan rashin tsawo ga waƙoƙin bara ya haɗa har da rubutattun waƙoƙin da mabaratan ke amfani da su wajen baran waɗanda ba domin bara aka wallafa su ba, amma su mabaratan suka zaɓi su riƙa yin bara da su. Waƙoƙin bara na baka kusan dukansu gajeru tun daga waɗanda Almajirai ke amfani da su har zuwa waɗanda sauran mabarata ke amfani da su. Su kuwa rubutattu da ake bara da su ko da masu tsawo ne za ka tarsa mabarata sun gutsure su sun mayar da su gajeru gwargwadon abin da suke iya riƙewa kamar da yadda aka bayyana can baya a cikin babi na uku. Misalin haka a wata waƙar bara ta baka shi ne waƙar “A Tumbulo”:

    A tumbulo Inna a tumbulo.

     A tumbulo a kawo ma gajere.

     Gajere ba abin renawa ba.

     (A Tumbulo)

    Wannan waƙar ba ta da ɗiya da yawa duka-duka ɗiyanta uku ne kuma haka almajirai ke bara da ita. Wannan waƙar ba ta da amshi domin ba a cikin taro ake rera ta ba. Sai dai almajiri na taka ‘yar rawa yayin da yake rera ta. Ga kuma misalin wata waƙar da ake rerawa a cikin taro mai suna “Assalamu Alaikuma Masu Gida”:

    Jagora: Assalamu alaikum masu gida muna muku sallama.

    Amshi: Baka.

    Jagora: Muna muku sallama don ɗai ku ba mu na Annabi.

    Amshi: Baka.

    Jagora: Sai zuciya ta daure in zuciya ta dangana.

    Amshi:Baka.

    Jagora: In bata dangana ba ilmi ya fi ta ya dangana.

    Amshi: Baka.

     Jagora: Inna uwata ce daga duniya hal lahira.

    Amshi: Baka.

     (Baka)

    Wannan waƙa da ta gabata Gardawa ne ke rera ta idan suna bara mafi yawa a daren Jum’a. Ana rera waƙar ne a cikin taro, wani na bayarwa saura suna yi masa amshi. Ita ma duk da yake masu rera ta manya ne amma gajera ce, domin ɗa goma sha biyu kawai take ƙunshe da shi.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.