5.12 Ɓelunge
Wannan wasa ne na dandali da yara maza ke gudanarwa a tsaye. Yana da siga ta shugabanci irin na limanci. Misalin yara goma zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Sannan wasan na tafiya da waƙa. Kuma akan yi amfani da kayan aiki yayin gudanar da shi. Wasa ne na dandali, saboda haka an fi yin sa da dare, musamman lokacin farin wata.
5.12.1 Kayan Aiki
i. Rigar da aka nannaɗe domin dukan wanda ya ɓata wasa.
ii. Bishiya ko garu ko makamancin wannan a matsayin sha.
5.12.2 Yadda Ake Wasa
Wannan wasa yana da sigar salla. Saboda haka yana ɗauke da liman da ladan da kuma mamu. Liman yakan shiga gaba. Ladan kuma yakan kasance a bayansa. Daga nan sai mamu su biyo baya cikin sahu-sahau, daidai da yawansu. Daga nan liman zai fara magana. Yayin da ya yi magana kuwa, to zai yi wata irin lanƙwashewa ko ta gaba ko ta baya, ko kuma ta gefe. Duk abin da ya faɗa, ladan zai maimaita sannan ya yi irin kwalmashewar da liman ya yi. Daga nan mamu ma za su yi tamkar yadda liman da ladan suka yi.
Yayin da ɗaya daga cikin mamu ya yi wani furuci ko wani motsi kafin ladan ya yi (bayan liman ya yi), to ya ɓata, don haka dokar wasa ta hau kansa. Haka ma yayin da mamu ya yi wata lanƙwasa ba irin wanda liman da ladan suka yi ba.
5.12.3 Waƙar Wasa
Ɓeɓɓeɓelunge,
Idan gero ya nuna,
Yara da manya ku tuma ku ci.
5.12.5 SakamakonWasa
Duk wanda ya ɓata wasa, za a bi shi da bugu ta hanyar amfani da riguna da aka nannaɗe. Haka zai yi ta gudu har sai ya je ya sha. Da zarar ya sha, to ya tsira.
5.12.6 Tsokaci
Wannan wasa hanya ce ta motsa jini ga yara. Bayan haka yana koyar da jarumta ga yara tare da juriya. Wani abin burgewa da jan hankali kuma shi ne, wasan yana hannunka-mai-sanda zuwa ga nutsuwa yayin salla. Wannan ya haɗa da daidaituwa yayin salla da kuma kauce wa wuce liman wurin aiki yayin salla.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.