5.12 Rashin Zaɓi Ga Wanda Ake Ba

     Citation: Bunguɗu, U.H. (2021). Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar HausaAhmadu Bello University Press Limited.

    Domin samun cikakken littafi, a tuntuɓi:

    Dr. Haruna Umar Bunguɗu
    (Sarkin Gobir Na Bunguɗu)
    Email: harunaumarbungudu@gmail.com
    Phone: 08065429369

    Bara da wasu waƙoƙin bara a ƙasar Hausa

    5.12 Rashin Zaɓi Ga Wanda Ake Ba

    Wata falsafar da ake iya hangowa a cikin waƙoƙin bara ita ce rashin zaɓi ga wanda ake baiwa. Idan mutum roƙo yake yi, to ba ya da zaɓi ga abin da za a ba shi. Zaɓi na ga hannun mai bayarwa. Misali:

    Ni ne ɗan kwalak-kwalak,

     Ni ne ɗan kulodo mai bara.

     Komi anka ba ni ci nikai.

     Ko kashi anka ba ni ci nikai.

     Amma ban da kashin bulala.

     (Ɗan Kulodo)

    Layi na uku da na huɗun na ɗan waƙar da ya gabata ya nuna almajirai na sane da cewa wanda za ba ba ya da zaɓi, sanin haka ya sa suke ambatawa a cikin waƙoƙin na bara cewa suna sane da haka tare da nuna kada mai ba su ya ga kamar abin da zai ba su ba zai karɓu ba, a’a ya ba su za su yi amfani da shi haka nan yadda yake. Ke nan sun nuna suna sane da maganar hikimar Bahaushe mai cewa “mai jiran a ba shi ya sha tasko.” Haka ma Bature na cewa “a begger has no choice.” Daɗaɗɗar maganar hikima ce cewa duk wanda zai roƙa a ba shi to zai iya fuskantar kowane wulakanci. Sai dai su masu bara musamman Almajirai suna daure ma haka ne domin cim ma wata biyan bukata a nan gaba duk da yake suna sane da wulakanci kuma suna ambaton haka a cikin waƙoƙin nasu na bara. Ga ma ƙarin wani misali:

     Jagora: Inna ki hanƙure ki ba ni na Allah.

     Amshi: Karigizo.

     Jagora: Inna ko hurar da ta kwan goma.

     Amshi: Karigizo.

     (Karigizo)

    A wannan ɗan ma a layi na biyu an nuna komai abu ya lalace mai bara shirye yake ya karɓe shi domin ba ya da zaɓi kuma ya shirya fuskantar wannan tasko.


    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.