5.13 Allazi Wahidun
Wannan ma wasa ne na yara maza. Misalin yara biyu ne zuwa sama da haka suke gudanar da wannan wasa.
5.13.1 Wuri Da LokacinWasa
i. Wasan na dandali ne.
ii. An fi gudanar da shi da dare, musamman yayin da akwai farin wata.
5.13.2 Kayan Aiki
i. Takalma
ii. Ƙwallon goruba
iii. Bishiya ko katanga ko wani abin da aka sanya a matsayin sha.
5.13.3 Yadda Ake Wasa
Yara sukan tsaya ba bisa ƙa’ida ba. Sannan wannan wasa ba ya da shugaba ko limami. Kowanne daga cikin ‘yan wasa zai nemi takalmi ya riƙe a hannunsa. Daga nan za a sanya ƙwallon goruba a tsakiya, sannan a yi waƙa kamar haka:
Allazi wahidun,
Mai rabo sa’a,
Marar rabo sai haƙuri.
Daga nan za a fara hanƙoron buga wannan ƙwallon goruba da takalman da ke hannun yara. Kowa zai riƙa ƙoƙarin buga ƙwallon gorubar zuwa ƙafar wani. Wanda aka bugo zuwa gare shi kuma zai yi tsalle don kada ta taɓa ƙafarsa, ko kuma ya sanya takalmi ya buge ta zuwa wurin ƙafafun wani daban. Haka za a ci gaba da yi, kowanne yaro yana ƙoƙarin ƙwallon gorubar ta taɓa ƙafar wani.
Duk wanda ƙwallon gurubar ta taɓa ƙafarsa, to shi ne allazi, kuma za a bi shi da duka da takalman da ke hannun ‘yan wasa. Wanda ake duka zai yi ta gudu domin ya je wurin sha. Da zarar ya sha to ya tsira.
5.13.4 Sakamakon Wasa
Sakamakon wanda ƙodagon goruba ya taɓa ƙafarsa shi ne duka da takalma. Zai yi ta gudu domin ya sha. Ba za a bar shi ba har sai ya sha.
5.13.5 Tsokaci
Wannan wasa yana koyar da jarumta da juriya ga yara. Sannan hanya ce ta motsa jiki gare su. Sannan masu wasa sukan samu nishaɗi.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.