Ticker

6/recent/ticker-posts

Cincin Sakatum

5.14 Cincin Sakatum

Wannan wasan dandali ne na maza. Yawanci yawan yaran da ke gudanar da shi na kaiwa takwas zuwa sama da haka. Yana tafiya da waƙa, amma ba a buƙatar wani kayan aiki yayin gudanar da shi. Kasancewarsa wasan dandali, an fi gudanar da shi da dare, musamman lokacin farin wata.

5.14. Yadda Ake Wasa

Yara sukan yi da’ira. Daga nan kuma wani zai shiga tsakiya. Wanda ke tsakiya zai fara waƙa yayin da yake dafa ƙirjin mutane ɗaya bayan ɗaya. Waƙar ita ce:

Cincin,

Sakatum,

Cincin,

Awut!

 

Duk wanda wannan waƙa ta ƙare a kansa, to ya fita. Haka za a ci gaba da yi har sai kowa ya fita saura mutum ɗaya. Daga nan mai waƙar zai yi musu tsakanin su biyu. Wanda ya gagara fita shi ne kura. Daga nan wanda ya tsaya tsakiya zai riƙe kura, saura kuma za su gudu. Wanda ke riƙe da kura zai tambaya:

“A sake kura?”

Masu wasa za su ce:

“Eh.”

Daga nan mai riƙe da kura zai sake ta, shi ma ya gudu. Kura kuwa za ta bi su da gudu. Duk wadda ta samu za ta yanka. Duk wadda kura ta yanka kuwa, to ya zama kura. Saboda haka zai taya kura kamu. Haka za a ci gaba da yi sai an yanka kowa.

 

5.14.2 Tsokaci

Wannan wasa yana taimaka wa yara wurin motsa jiki. Sannan yana samar da raha da nishaɗi a tsakaninsu.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments