Balbela-Balbela

5.15 Balbela-Balbela

Wannan ma wasa ne na dandali da yara maza ke aiwatarwa yayin da akwai farin wata. Kimanin yara takwas zuwa sama ne suke gudanar da wannan wasa. Wasan na tafiya da waƙa, sannan yana buƙatar kayan aiki yayin gudanar da shi.

5.15.1 Wuri Da Lokacin Wasa

i. Wannan wasa ne na dandali.

ii. An fi aiwatar da wannan wasa da dare, musamman lokacin farin wata.

5.15.2 Kayan Aiki

i. Riga da aka nannaɗe domin dukan wanda ya faɗi

ii. Wurin sha

5.15.3 Yadda Ake Wasa

Yara sukan tsaya ba bisa wani tsari ba, wato kara-zube. Daga nan kuma jagora zai shiga gaba. Jagora zai riƙa waƙa yayin da saura ke amsawa:

Jagora: Balbela-balbela,

Yan Wasa: Jalingo.

 

Jagora: Ina za ki je ki?

Yan Wasa: Jalingo.

 

Jagora: Gidan Audu rimi.

‘Yan Wasa: Jalingo.

Jagora: Da ceɗiya da rimi,

‘Yan Wasa: Jalingo.

 

Jagora: Ala jiƙan maza sun faɗi ragwas! 

Da zarar an kai wannan gaci, kowa zai ƙame a yadda yake ba tare da motsi ba. Duk wanda ya motsa to ya faɗi, don haka za a hau shi da bugu har sai ya sha.

5.15.4 Sakamakon Wasa

Sakamakon wanda ya faɗi a wannan wasa shi ne duka da riga da aka nannaɗe. Ba za a bar dukan wanda ya faɗi ba har sai ya sha.

5.15.5 Tsokaci

Wannan wasa yana taimako wa yara wurin ware jini. Sannan yana sanya musu juriya da jarumta, musamman yadda yara za su tsaya cak cikin wani hali mawuyaci. Amma haka za su daure ba tare da sun yi motsi ba. Bayan haka, wasan na samar da raha da nishaɗi tsakanin yara.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments