Noti-Noti

5.16 Noti-Noti

Wannan wasa ne da yake da zubi da tsari da kuma sakamako irin na wasan jini da jini. Abin da ya bambanta su kawai shi ne waƙar da ke cikin wasannin biyu. Sai dai jini da jini ana ƙoƙarin bambance abubuwa masu jini a jiki da marasa jini a jiki ne. Wasan noti-noti kuwa ya karkata ne zuwa ga bambance abubuwan da suke da noti a jikinsu da kuma waɗanda ba su da noti.

Waƙar wasar noti-noti ita ce kamar haka:

Bayarwa: Noti-noti,

Amshi: Gulum noti!

Bayarwa: Mashin noti,

Amshi: Gulum noti!

 

Bayarwa: Mota noti,

Amshi: Gulum noti!

Bayarwa: Keke noti,

Amshi: Gulum noti!

 

Bayarwa: Inji noti,

Amshi: Gulum noti!

 

Bayarwa: Jirgi noti,

Amshi: Gulum noti!

 

Bayarwa: Akuya noti,

Amshi: Gulum babu!

 

Duk wanda ya ambaci noti a abin da ba ya ɗauke da noti to ya faɗi. Haka ma wanda ya nuna babu noti a jikin wani abu alhali yana da shi. Sakamakon wannan wasa da kuma amfaninsa daidai ne da na jini da jini kamar yadda aka kawo a sama.

WASANNI A ƘASAR HAUSA

Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.


Post a Comment

0 Comments