5.17 Damo Riya Damo
Wannan ma wasa ne da ke da zubi da tsarin jini da jini da kuma noti-noti. Abin da ya bambanta su kawai shi ne waƙoƙin da ke cikin kowace wasa. Waƙar damo riya damo ta kasance kamar haka:
Bayarwa: Damo riya damo,
Amshi: Damo!
Bayarwa: Damo ɗan hajiya,
Amshi: Damo!
Bayarwa: Mu je Katsina da kai,
Amshi: Damo!
Bayarwa: Mu lafto kanwa,
Amshi: Damo!
Bayarwa: Mu kai wa hajiya,
Amshi: Damo!
Bayarwa: Ta ɗanɗana ta ji,
Amshi: Damo!
Bayarwa: Sauran wani ya faɗa.
Yayin da aka kawo wannan gaɓa, duk wanda ya ambaci damo to ya ɓata, saboda haka hukuncin wasa ya hau kansa tamkar yadda aka tattauna a sama, cikin bayanin wasan jini da jini.
Citation: Sani, A-U. & Gobir, Y.A. (2021). Wasanni a Ƙasar Hausa. Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-59094-1-8.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.